Sashe 57
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo ta na sallama kassa kassa nan ta isko shi kwance saman gado da ga shi sai short , ya daura hannu guda saman forehead , da gudan kuma ya na rike da wayarsa ya na latsawa wani cool murmushi ta saki kafin ta tako a hankali , kai tsaye ta Haye saman shi ta kwanta , ta lumshe idanunta a tare duk su ka sauke ajiyar zuciya , sannan ya sauko da hannunsa da ga saman forehead ya daura saman bayanta ya fara shafawa a hankali a sanyaye ta ce mishi " tashi mu je mu yi breakfast " kashe wayarsa ya yi ya daura saman bedside drawer ya ce mata " okay , bari na je na saka kaya " mikewa ta yi a hankali da ga jikinsa ta koma bakin gadon ta zauna a hankali shi ma ya mike zaune ya sauko da ga saman gadon ya nufi dressing room ya shiga ita dai ta yi zaune ta zuba mishi ido , da ga gani akwai abun da ke damun shi ta na zaune a haka har ya fito sanye da wasu kananan kaya wandon Jeans da T-shirt ya karaso bakin gadon ya mika mata hannu da sauri ta sauko da ga saman gadon ta riko hannunshi su ka fito a tare a nan parlourn su ka zauna su ka yi breakfast din , shi coffeen da ta hada mishi kawai ya sha dan shi kadai ya ke da bukata a yanzu sai da su ka kammala ba wanda ya ce ko ufan , ta tattare kayan ta meda kitchen bayan ta dawo ta isko ya na konce a kassa saman carpet , ya lumshe idanunshi , Tabbas ko bai fada mata ba ta san wani na damun sa dan ba ta taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba , ko dai bomb din da ya tashi da jet insa ne abun ya ba shi tsoro , ko kuma wani abun a hankali ta karaso in da ya ke kwance ta haye saman shi ta zauna saman cikinsa slowly ya ware idanunsa , sannan ya ce ta sauka ya zauna ba musu ta mike tsaye , ya zauna ya ja da baya ya jingina bayansa da sofa , sannan ta koma ta zauna saman Thigh insa zagayo da hannayanta ta yi a wuyansa ta ce mishi " Honey , me ya faru don Allah ? na ga duk ka sauya lokaci guda , ko ba ka jin jikinka ? " sai da ya ja wani dan karamin tsaki kafin ya ce " Ba haka ba ne Beautie , just akwai abun da ya tsaya min a rai na rasa ya zan yi " " ka fada min minene , may be ka ji sauki idan ka fada min , please " ta fada ta na marairaice mishi fuska sai da ya share five minutes bai ce mata komai ba ya zuba mata ido , haka ita ma ta zuba mishi ido ta na jiran ta ji abun da zai ce mata a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya bude baki ya ce mata " ni ma ban sani ba , may be idanuna ne su ka samu matsala , ko dai kama ce kawai " cikin rudu ta ce mishi " ban gane ba Honey , me ya faru ? " " i think , i saw Nayab " " What ? " ta fada da dan karfi dan lumshe idanunsa ya yi a hankali kafin ya sake bude su ya ce mata " Beautie , ban san ya zan fada miki hakan ba , Lokacin da mu ke airport za mu shiga Jet , na tsaya ina kokarin kiran ki na fada miki zan dawo , juyawar da zan yi kawai na ga kaina ina kokarin shiga wani jirgin , you know it is impossible a ce na ga kaina a waje biyu , yadda ki ka gan ni haka , haka ni ma na gan sa , ba abun da ya banbanta mu , na fada miki har wannan smooth hair din nawa , da yanayin jikina , tsayina , idanuna , lips ina , All , Beautie kamar ina kallon kaina ne cikin mirror haka na gan sa , na yi tunanin ko kawai ba na gani ne kyau na tsaya na zuba mishi ido har ya shiga jet din , ya tashi , ya na barin wajen ne Jet din mu ya tashi da Bomb " Wata sabuwa kuma , Nayab dai wannan Nayab da kowa ke shaidar ya mutu , a ka je da gaske Prince Nayab ne ya gani ? gaskiya akwai sauran labari ) a hankali ta matso kussan kirjinsa , ta kai hannu saman face insa , cike da kula ta ce mishi " Honey , please ba abun da ka ke tunani ba ne , kai fa da kanka ka ce min Nayab ya mutu tun lokacin da ya shigo duniya , ta ya za a ce ka gan shi lokaci guda haka ? " " Beautie , ni ma na kassa yarda , hankalina ya kassa dauka " ya kai karshen ya na lumshe idanunsa " dan haka kar ka ba shi damar dauka " ta kai karshen ta na janye hannunta da ga saman fuskarsa slowly ya ware idanunsa ya fara ganin wani dishi dishi kafin ya fara gani dai-dai a hankali ya ga ta yi sama yar t-shirt din ta , ta fidda ta ta ajiye gefe zagayo da hannayansa ya yi a kugunta ya matse ta a jikinsa , a hankali ya kai lips din sa saman wuyanta ya manna mata kiss a dai-dai lokacin ko Aleenah ta shigo musu parlourn ta na sallama da fara'a a face din ta a tare duk su ka zaro idanu musaman Aleenah ba ta yi tunanin za ta tardo su cikin wannan yanayin ba da sauri ta juya za ta bar wajen , ba ta yi taku daya ba Aleesherh ta tsayar da ita da cewa " kar ki tafi madam , dawo ai kin riga da kin ga komai " a hankali Prince ya dago kansa , cikin rada ya ce mata " tashi na tafi , ina son na kwanta " " please honey , ka zauna mu yi hira da ita " ta fada ta na marairaice mishi fuska gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce mata komai murmushi ta saki kafin ta sauka da ga saman shi , ta auki rigarta ta saka ta na sauka ya tashi da sauri ya nufi corridor ya shiga , gwara ya yi mata wayo ya san in ya biye mata za su yi ta jayayya ne , yanzu ga shi cikin ruwan sanyi ya kubce mata cike da shagwaba ta shiga kiran sunansa ta na fadin " Honey , please ka dawo " amma ya share ta ya ci gaba da tafiyarta sai da ya shiga sannan ta kalli Aleenah da ke tsaye ta juyawa parlourn baya ta ce mata " to ke malama sai ki shigo , kin kore shi kin ji dadi " wata yar karamar dariya Aleenah ta yi kafin ta juyo ta fara takowa a hankali ta karaso cikin parlourn ta na fadin " to ke madam , bedrooms din naku wani aljani ne a ciki da ba ku iya tsayawa a cen ? " ta fada cikin zolaya hararrar ta Aleesherh ta yi kafin ta ce " wai me ma ya kawo ki waje na a wannan lokacin ? " zama gefenta Aleenah ta yi kafin ta ce " nothing , just ina kewar ki ne , shi ne na zo ganin ki " ta kai karshen ta na rungumo ta " to yanzu ga shi kin sa Honey ya tafi , ai da sai ki min text za ki zo , da yanzu naked ki ka tardo mu fa ? " bushewa da dariya Aleenah ta yi har da tapi , sai da ta tsagaita dariyarta sannan ta ce " sannu Honey , shikenan bari na tashi na tafi in da na fito " da sauri Aleenah ta riko hannunta ta na fadin " no , kar ki tafi , na ji dadin ganin ki , mun jima ba mu zauna ba haka , na yi kewar ki sosai " wata yar karamar dariya Aleenah ta yi kafin ta ce " na zata kin manta da ni , ki na nan rungume da Honey " " hmmm , ke ma kin sani duk abun da zai faru ba zan iya mantawa da ke ba , ke ce dai ganin ki ya zama kallon rana , kullum ki na ciki sai ka ce amaryar , ki dinga fitowa may be ki hadu da naki Prince din " ta fada cikin zolaya ta na wata yar karamar dariya murmushi mai dan sauti Aleenah ta yi kafin ta ce " in sha Allah , watarana zan hadu da shi , amma ba yanzu ba , yanzu dai tashi ki je ki kula da Honey , ni na tafi " " no , gaskiya babu in da za ki je , yau tare za mu zauna mu yi hira " Aleesherh ta fada dan gaskiya ta jima ba ta zauna da yar uwarta haka ba , su ka yi hira ba dan ta so ba ta zauna su na zuba hira da dariya Prince kuwa ya na cen Bedroom din sa tunanin duniya ya yi mishi yawa , ya na tunanin abun da ya gani a airport ya kassa yarda da hakan , ta wani bangaran kuma ba ya tunanin gaskiya ne tun da har ya na da tabbacin Nayab ya rasu , amma minene tabbacin nasa ? Malik da Inaya su ka ce mishi ya rasu , a ka je su ma ba su da tabbacin ya rasu ? , gaskiya dole ya yi investigation in har da gaske Nayab ne ya gani to dole ya shiga neman dan uwansa ko da ya na bangon duniya a takaice dai haka su ka share inin ranar a haka , Aleesherh da Aleenah su na a parlour su na hira , sai da lokacin sallat ya yi sannan Aleesherh