Sashe 54
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cutie , za ta rage miki kewar Babynki ' ta kai karshen cikin zolaya ba musu Aleesherh da Aleenah su ka mike su ka bi bayanta su ka nufi part din Malik *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , 500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP IN* *HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE 300* https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 26 SAUDIYA CENTRAL PRISON IZZAT zaune ta ke a waiting room saman chair ta zubawa kofar shigowa ido ta yi wajen five minutes zaune a haka kafin Izayn ya shigo dakin babu ko sallama ta na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " haba don Allah , tun dazu na ke jiran ka " bai ce mata komai ba ya fiddo wata yar karamar bottle da ga cikin aljihunsa da wasu ruwa farare a ciki ya mika mata ya na fadin " sai kin yi hankali wajen aiki da shi " hannu ta kai ta karba ta na fadin " Ba ku fada min abun da zan yi ba " a hankali ya tako dab da ita ya kai bakinsa saitin kunnenta ya fara yi mata rada ko me ya ke fada mata , da ga ji ba alkhairi ba ne ) da sauri ta ja da baya ta na girgiza mishi kai ta na fadin " gaskiya ba zan iya ba , a ka je a ka kama ni fa ? " ta fada a dan razane " ba za a kama ki ba , kawai ki san yadda za a yi laifin ya koma kan wani cikin fadar , wanda za a iya kama shi cikin sauki " shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba da alamun tunanin wani abu ta ke yi " ni zan tafi , ki san yadda za ki yi , da ga yanzu kar ki sake dawowa wajena " ya fada ya na juyawa zai fita da sauri ta ce mishi " why ? ba ka son na dinga zuwa ? " a hankali ya tsaya , ba tare da ya juyo ba ya ce " no , Ina son Mai girma Malik ya san da zamana cikin kassar Saudiya , da ga nan kuma ki jira ni a Daular , ba zan jima ba zan fito " ya na gama fadar haka ya fice sai da ta dauki lokaci zaune cikin prison din ta na tunaninta kafin ta baro , ta bi hanyar da ta ke bi kullum ta koma Daular DAULAR SAUDIYA MISALIN KARFE 8 NA DARE Yau dai duk ahalin Malik sun hadu a part din sa , a floor na uku , yau tare duk za su yi diner , da Diya , Nesrine , Tesnim , Abdoul , Rianna , Princess , Azmat , Aleesherh , Aleenah , har da Faaz , sannan uwa uba Malik da Inaya sai abinci su ke ci su na hirar su gwanin burgewa , musaman Malik ya jima bai tara ahalinsa haka ba su ka yi diner Ita dai Aleesherh ta yi shiru kanta na sunkuye ta na wassa da spoon din ta cikin plate din ta ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Alee , lafiya tun dazu ba abun da ki ka ci sai wassa ki ke da spoon din ? ko ba ki jin jikinki ne ? " girgiza mata kai ta yi a hankali , ta na shirin magana Princess da ke zaune gefen Inaya ta riga ta cewa " Cutie , ba wani ciwo da ta ke , kawai ta na kewar Babynta ne " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya wani dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya ce " to sannu ke kuma , ina laifi dan ta na kewar mijinta , na ga ke ma naki tun da ya tafi bai kira ki ba " da sauri Abdoul ya ce " Malik , Yaushe Princess ta yi miji ba na da labari ? " ya tambaye shi dan shi yanzu duk yawancin abun da ke Faruwa cikin masarautar ba shi da labari saboda yanzu shi office din President ya koma da aiki , Diya kuma ya na a Fada murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya ce " ka tambaye ta ga ta nan zaune gefenka " da sauri ta ce " Alee , ba ki fadi abun da ke damun ki ba ? ko ciwo ki ke mu ke na duba ki ? " ta fada dan ta na san kawar da zancen sai da Inaya ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " Alee , rabu da wannan , fada min me ke damun ki ? " murya a sanyaye ta ce " ni ma ban sani ba momy , tun da yamma nana ke jin gabana na faduwa , kamar wani mugun abu na shirin faruwa " a hankali Malik ya dafa shoulder din ta dan dama a gefen hangunsa ta ke zaune , cikin sanyin murya ya ce mata " ki kontar da hankalinki , ba abun da zai faru " ya na gama rufe bakinsa su ka jiyo wayar Diya ta na ringing a hankali ya mike tsaye ya na fadin " ku ci gaba bari na amsa " da to kawai su ka amsa mishi sh ka ci gaba da cin abincinsu ba wanda ya ce ufan dan Aleesherh ta kashe musu jiki Diya kuma Parlourn ya koma ya zauna , sannan ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cikin nitsuwa a daya bangaran Muryar wani Matashi na jiyo ya amsa mishi sallamarsa kafin ya ci gaba da fadin " Please ina son magana da mai Girma Malik " " Da shi ka ke magana " Diya ya fada sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Ranka shi dade , na kira ne da ga kassar London a UK , dan sanar da kai Jet din Yarima ya tashi da Bomb , a cikin airport din kassar " " What ? " Diya ya fada da mugun karfi ya na mikewa tsaye har ya saki wayarsa ta fadi kassa nan take hankalin kowa ya dawo kansa , sai innallillahi wa'ina illaihi raji'un ya ke furtawa kassa kassa da sauri Malik ya mike ya nufe shi ya na fadin " Diya ? what happened ? " a rude Diya ya shiga ce mishi " Malik , Jet din su ne Prince ne , ya tashi da Bomb a cikin airport " wata razananiyar kara Aleesherh ta saki ba tare da ta sani ba ta na toshe bakinta da dukka hannayanta biyu da sauri Aleenah ta rungume ta kamar za ta yi kuka ta ce " sai da na ce muku ina ji a jikina wani abu zai faru " " please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya faru da Prince , ba su cikin Jet din " fadin Malik a tare duk su ka ce mishi " ba ya cikin Jet din ? ta a ka yi ka sani ? " " sun ce a cikin airport ne , may be ba su kai ga shiga bomb ya tashi da Jet din " ya fada ya na son kontar musu da hankali su na a haka su ka jiyo wayar Aleesherh ta na ringing hannu Aleesherh ta kai saman table ta dauki wayar ta na kallon screen din lambar ta kassar UK ce , kawai sai ta kashe kiran dan a tunaninta dan su ce mata Jet din Prince ya tashi da Bomb ne su ka kira ta ko kuma su ce su na Hospital ta na kashe shi ko wani kiran ya sake shigowa wannan karan ba ta kashe ba , ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na jiran ta ji abun da za a ce mata kawai sai ta jiyo Muryarsa ya na fadin " Yaushe ki ka fara jin tsoro haka ? ba sace ki za a yi ba " da sauri ta mike tsaye ta na fadin " Baby ? ba abun da ya same ka ? " " please kontar da hankalinki , ba abun da ya same ni , please ki kai wa Daddy wayar ina son na yi mishi magana " a hankali ta fara kuka ta na fadin " don Allah ka dawo , kar wani abu ya same ka " " ki fara ba ni Daddy please " ya fada a sanyaye ba musu ta sauko wayar ta nufi Malik ta mika mishi ita , ta na zubar da hawaye hannu ya kai ya karbi wayar sannan ya kai ta a kunne ya na fadin " Prince , ba abun da ya same ka ? ina Junior ? " " ba abun da ya same ni Daddy , just Junior ya samu dan rauni a kansa , bayan haka ba abun da ya same mu " " shikenan Allah ya kara kiyaye gaba , yanzu yaushe za ku dawo " " kun san dai Jet ina ya tashi da Bomb ko ? sai kun turo mana wani jirgin za mu iya baro kassar " wata yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " shikenan , gobe ina sa Helicopter ya je ya dauko ku " " okay Daddy , sannan please ku kula min da ita ba na son ta saka damuwa a ranta , sai na zo " ya na gama fadar haka ya katse kiran sauko wayarsa Malik ya yi a hankali sannan ya mikawa Aleesherh kayanta ya na fadin " kar ki damu , ba abun da ya same shi , gobe za su dawo , Princess ! please zo ki kai ta bedroom inki ta kwana a nan gobe sai ta koma part inta " da to kawai Princess ta amsa mata kafin ta karaso ta riko hannun Aleesherh su ka shiga corridor ta wuce bedroom din ta da ita sai da su ka bar wajen sannan Malik ya kalli sauran mutanan wajen ya da ce " please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya same su " da to kawai su ka