← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 61

Sashe 3

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ta ce " me za ki yi ? , ko ki na tunanin za ki iya yin wani abu a kansa ne ? " wani dan karamin murmushi ta saki , kafin ta daura hannunta saman cikinta , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ni ba zan yi komai ba , amma dan da zan haifa ya yi wani abu a kai , in har jinina ne kuma jinin Aymane , na tabbata ba zai taba barin wanda ya raba shi da mahaifinsa ya yi rayuwa cikin farinciki ba , sai ya daukar min fansar da ni na kassa dauka , sai na ruguza wannan masarautar ta Saudiya , in har ban yi haka ba to ban cika diyar Mohammed ba " a razane Manisha ta ce " ke Hafsat ki na da hankali kuwa ? kin san ab...... " ba ta karasa maganarta ba kawai ta ga Hafsat ta bace bat , babu ita babu mai kama da ita tsananin tsoro Manisha ba ta yi wani motsi ba ta sulale sumamiya a wajen ( to fa , a na dara ga dare ya yi , sihirin Aymane ne ya dawo jikin Hafsat , ko ta babyn da ke cikinta ne ta ke sihirin , TO NI NA YI GABA , MAY BE KAFIN NA DAWO , TA DAWO ITA MA ________________________________________________________ Tsaye mama da Diya su ke bakin kofar Cemetery din masarautar , babu kowa da ga su sai Allah tsakiyar rana , sai bin wajen da kallo su ke , yi , yadda ka san sahara haka ya ke " mama , ai wannan samo shi kamar neman alura cikin ciyawa ne , ba za mu iya neman sa ba " fadin Diya cikin raunin murya " kai ba za ka iya ba , amma macijinka za iya samo wajen da su ka bizine shi , in har Aswad na jikinsa to zai iya samo Nayab " ta fada ba tare da ta kalle shi ba wata irin muguwar faduwa gabansa ya yi , har sai da ya ga wasu dan taurari , a dubu dari ya juyo ya na kallon mama ya na zaro idanu a hankali ta juyo ta kalle shi , ta saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ta ce " ko ka yi tunanin za ka iya boye min ? ina sane da duk abun da ke faruwa a zagaye da ni , ko da abun a boye ya ke ina iya gani , tun ba yau ba na san da wannan maganar , kawai na yi shiru ne , yanzu ka fitar da macijinka ba mu da isashen lokaci " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya lumshe idanunshi , ya fara motsa lips din sa a hankali farat daya kawai ya koma macijinsa , a hankali ya konta kassa , ya fara tafiya , ya na zagaye kabaririkan da je wajen , sai da ya iso tsakiyar cemetery din sannan ya tsaya , ya mike ya juya ya kalli mama , alamun ya samo wajen gyada mishi kai mama ta yi kafin idanunta su sauya su koma farare kal , bat ta bace , sai ga ta tsaye geffen macijin nan , ta na fitowa idanunta su ka dawo dai'dai ta na kallon wajen ta ce " tono ramin mu gani " ba musu ya sa wutsiyarsa , ya fara ginar wajen , a haka har su ka fara hango wani warin veil wata yar karamar ajiyar zuciya mama ta sauke kafin ta Zube saman guyiwowinta a wajen , ta fara gina da hannayanta janye wutsiyar sa ya yi , ya birkice ya koma mutum , sannan ya shi ma ya tsuguna ya fara gina da hannayansa sai da su ka fito da babyn su ka kontar da shi a kassa da sauri mama ta sa hannu ta warware tissu din ba shiri ta mike tsaye ta na karanto kalmar shahada a rude ta ke kallo Diya ta ce " Diya , ina Nayab ya yi ? " ta fada dan ba doll ce a nade cikin tissu din " mama ni ma jan sani ba , amma duk yadda a ka yi an nade Nayab cikin tissu din nan , sai in dai da ga baya su ka fitar da shi " " Hakan na nufin Nayab bai mutu ba , Diya bai mutu ba " mama ta fada a dan razane ta na zaro idanu shiru Diya ya yi bai ce mata komai ba , ya kassa cewa komai yanzu me Malik zai yi in ya ji labarin Nayab bai mutu ba , zai sa a neme shi ko zai bar maganar ? to wa ya sace Nayab ? dan wannan sace shi a ka yi in a na da Niyyar medo shi da ba za a saka doll cikin tissu din ba WATA SABUWAR KUMA , NAYAB BAI MUTU BA , KUMA DA ASWAD A JIKINSA KAR FA A JE HAFSAT TA ZAGAYO TA DAUKE SHI
Chapter 3 · 0% Book details