Sashe 19
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a yi wa Malik ? wani abu su ke boye wa shi da Malikat Inas ko kuwa ? bari dai mu ci gaba da mu jiyo amsoshin da ga baya ) INAYA da Sallama a bakinta ta shigo parlourn part din su da ke floor na uku amma sai ta ga babu kowa a cikin part din , yawancin lamps ma su na kashe kawai sai ta juya ta koma cikin lift ta Haye a floor na hudu nan kuma ta na shigowa ta ga Jallabiyar Malik ajiye saman sofa wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ci gaba da takawa a hankali har za ta shiga corridor din ta hango shi ta cikin glass din bayan dining room a hankali ta juya ta nufi glass din ta na kallon shi ya na cikin ruwan nan da su ke zuba ta dutsen da ke bayan masarautar , ya juyawa glass din baya wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta nufi corridor din ta shiga kai tsaye bedroom din su ko da ta shigo ta ga kayan barcinta shinfide saman gadonsu da alamun shi ya fiddo mata su ba ta bi ta kan kayan ba kai tsaye ta nufi dressing room MALIK yadda Inaya ta bar shi ko motsi bai yi ba , ya kurawa moon ido ga shi ko yau ta cika gwanin burgewa , ko tunanin me ya ke yi, Allah kadai ya sani ya na a haka na ga Inaya ta karaso wajen , ta na bi ta cikin manyan duwatsun nan har ta karaso bakin ruwan hannu ta kai ta warware veil din ta , ta ajiye bakin ruwan , sannan ta fidda Abayarta ta sama ta bar wata doguwa fara mara nauyi ta cikin Abayar a hankali ta shiga cikin ruwan da ya ke wajen ba wani zurfi ne da shi ba ta fara takawa a hankali har ta karaso inda ya ke tsaye , ta zagayo da hannayanta a gabansa ta rungume shi ta kontar da kanta a bayansa wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daura hannunsa saman nata da ke saman chest din sa ya na fadin " ba cewa na yi ba ki tafi ki yi barci ba, ko ba ki ga takardar da na ajiye miki ? " cikin shagwaba ta ce mishi " ni ban ga komai ba , kuma kai ma ka sani ba zan iya yin barci ba in ba ka tare da ni " murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya juyo a hankali su na fuskantar juna bai ce mata komai ba kawai ya sa hannu ya yi sama da rigarta sannan ya tilla cen bakin ruwan in da ta ajiye abayarta sai da ya tilla rigar sannan ya ce mata " Cutie , please ki ba ni wani babyn , wlh ina son mu samu wani babyn " nan take yanayin face din ta ya sauya , ta marairaice mishi ita ta na fadin " Baby , ko ina so ba zan iya ba " " why ? na ga har yanzu ba ki daina period ba , please my Cutie " " don Allah ka bar maganar nan , Twins din mu ba su ishe ka ba ne ? , ko har ka gaji da su ? " " no , ban gaji da su ba , kuma kin sani ina son su fiye da rayuwata , Just ina son na sake jin wannan farincikin da su ka saka ni lokacin da su ke baby , lokacin da na ke riko hannunsu ina koya musu tafiya , ina ba su abinci a baki , lokacin da na koya musu addini , ba ki sani ba amma wadanan lokutan su na daya da ga cikin abubuwan da su ka fi mahimanci a rayuwata , da zan iya komawa baya dan na sake yin hakan da na yi , amma yanzu komai ya sauya , dubi Prince ba ya ma zama tare da ni , sai na yi wajen three months ba na da labarinsa , please my Cutie ki ba ni wani babyn in ya so da ga shi ba kari " nan take ta ji jikinta ya yi sanyi jin abun da ya ce , ita ta sani duk abun da zai ce ba za ta iya samun wani babyn ba , ba dan ta na tsoron abun da ya faru da farko ba , kuma har yanzu ba ta daina period ba , akwai wani sirrin da ta boye mishi tsawan shekaru a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta juya mishi baya , murya a sanyaye ta ce mishi " i'm sorry Yaya Zayd , ko ina so ba zan iya samun wani babyn ba , lokacin da na samu cikin Twins da mu ka fara zuwa test Hospital , likita ya ce min blood type di na da na su ba daya ba ne ta bangaran Rhesus factor , ya kuma ce min akwai allurar da ya kamata a yi min da zarar na haihu dan kashe Rhesus factor din su da ga cikin jinina in ba a yi allurar nan ba ba zan sake haihuwa ba , i'm sorry ni ma ban san ya a ka yi wannan maganar ta fita da ga kaina ba har na manta ban fada maka ba , ni kaina ina son mu samu wani babyn amma ba zan iya ba , ka yi hakuri , amma ba komai ni na ba ka dama ka auro wata matar wadda za ta iya ba ka abun da ni na kassa ba ka " ta kai karshen kamar za ta yi kuka har wasu ruwa idanunta su ka kawo dan ba karamin zafi wannan maganar ta yi mata ba specially ma ta karshen , ba ta jin za ta iya jure ganin Yaya Zayd din ta da wata matar amma ta na son farincikinsa fiye da nata shi kansa jikinsa ya yi mugun sanyin jin abun da ta ce , kenan ba zai sake samun wani babyn ba da ita ? duk laifinsa ne , ya san ya cutar da ita dayawa lokacin da ta ke da cikin Twins din sa , har yanzu in ya tuno wannan abun sai ya ji kamar ya yi kuka ajiyar zuciya ya sauke kafin ya matso a hankali ya zagayo da hannayansa saman cikinta da ke shafe kamar ba ita ta haifi Prince ba sannan ya kontar da kansa saman shoulder din ta , kamar ya na yi mata rada ya ce " Cutie , babu wata macen a duniyar nan da za ta bani abun da ke ki ka bani ko da rabinsa ne , haka kuma babu wata matar da zan kwanta a kan gado guda da ita bayan ke , Cutie ke fa ce kinshigin rayuwata , In har babu Inaya to babu Nawfel , saboda Inaya ne kadai Allah ya hallici Nawfel ba dan Inaya da wata ba , ina son mu samu baby amma son da na ke miki ya fi komai , a cen baya na nuna son zuciya na saka ki cikin bakinciki da damuwa ba kadan ba , wannan karan farincikinki ya fiye min komai fiye da nawa , Alhamdoulilah ba dai mu na da magada ba ? sun ishe ni wlh a bar maganar wani babyn , in dai hakan na nufin na sake saka ki cikin wata damuwar , I love you more than my own life my Cutie , you know i can do anything for you " wani cool murmushi ta saki kafin ta lumshe idanunta ta ce " na sani Babyna , amma......... " bai bari ta karasa maganarta ba ya katse ta da cewa " tun da kin sani shikenan ba sai kin kara wani abu ba a kai , Cutie yanzu har za ki iya tunanin na hada ki da wata cikin zuciyata ? ke ma kin sani hakan ba za ta iya yiyu wa ba , kuma babu macen da za ta iya bani rabin abun da ki ka bani , kin ba ni farincikin da ban taba tunanin zan same shi a duniyar nan , ki ba ni soyayyarki da zuciyarki baki daya , kin ba ni family a lokacin da na rasa tawa , kin so ni a lokacin da kowa ke gudu na , ga shi yanzu kin sake ba ni wata familyn da sai na mutu ina alfahari da ita , haba My Cutie ki bar ma wannan zancen , kuma tsakani da Allah ni yanzu na tsufa na wuce maganar aure sai dai na Twins " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juyo ta rungume shi tsam dariya shi ma ya yi a hankali kafin ya fara shafa bayanta ya na fadin " bare ma mun kusa samun jikoki , kin ga zan samu wasu babys din " a hankali ta dago kanta da ga saman chest din sa ta ce " Baby , dama Ammie ce ta kawo shawarar aurar da Prince , ta ce wai in ya na familyn kansa zai hakura da wannan yawon da ya ke " " hmmm , ke ki na ganin Prince zai daina wannan yawon nasa ? ai cikin sauki zai dauki familyn tashi su tafi tare , kawai auren ya kamata mu yi mishi , dazu bayan na shiga part din Diya a ka kawo min letter da ga masarautar Yemen , Al-Sayid Abdoul-Mueed ya bawa Prince da Junior auren yaransa mata biyu , na kuma amince dan jira na ke Prince ya dawo da ga Yemen din na sa ya koma dan a daura auren a cen " " ban gane ba Prince ya na Yemen ? " gyada mata kai kawai ya yi ya na sakin murmushi murmushi ita ma ta sakin mishi kafin ta ce " Alhamdoulilah , dama ina tunanin wace yarinya za mu zaba mishi da za ta dace da shi " a hankali ya zagayo da hannunsa a kugunta ya matse ta a jikinsa ya na fadin " tun da mun kammala case din Prince , sai a kula da ni yanzu " wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " mu koma ciki to