Sashe 39
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na fitowa ta ga wata maid ta baro dining table ta na shirin komawa kitchen da sauri Aleesherh ta taro ta ba musu ta tsaya ta dawo ta zube saman guyiwowinta a gaban Aleesherh ta na gaishe ta cikin girmamawa wani dan karamin murmushi Aleesherh ta saki kafin ta ce " mike tsaye don Allah , kar ki sake min irin wannan abun , ba kin girme ni ba " ba musu ta mike tsaye kanta a sunkuye ta ce " haka ne ranki ya dade , na girme ki amma matsayin mu ba daya ba " " shikenan , ya sunanki ? " " Asmeet , ranki shi dade " " Asmeet , don Allah akwai kitchen a wajen nan ? " " Eh ranki ya dade " " mu je ki gwada min please " gyada mata kai kawai Asmeet ta yi kafin ta fara takowa ta yi gaba kai tsaye su ka nufi hanyar fita wajen su ka fito harabar part din , su na fitowa su ka yi dama nan ta ga wata door ta zallar glass , su na isa door din ta bude nan ta ga kitchen din cike da maids har wajen goma , kitchen din a share a goge kamar ka ci abinci a kassa , sai aiki su ke yi duk su na ganin Aleesherh kowace ta tsaya cak su ka sunkuyar da kai su na gaishe ta kai ka ce ita ce MALIKAT INAYA da murmushi a face din ta ta amsa musu , sannan ta fada musu abun da ta ke bukata ta shirya wa Prince breakfast , sannan ta ce musu da ga yau duk abincinsa ita za ta shirya shi da to kawai su ka amsa mata sannan su ka fiddo mata abubuwa da ta fada cikin nitsuwa ta fara hada mishi breakfast da coffee cike da so , bayan ta kammala ta shirya komai saman tray sannan ta dauki kayanta ta fice ta bar su su ka ci gaba da aikinsu da sallama a bakinta ta shigo parlourn duk da ba ta san in ya na nan ko ba ya nan ta na shigowa ta gan shi zaune saman sofa sanye da kananan kaya , wandon jeans da rigarsa duk Blue color , ya na rike da wayarsa da hannu guda ya na latsawa Princess ta na konce gefensa ta tada kai da laps din sa , hannunta da hannunsa na sakale cikin na juna , ta lumshe idanunta da wani dan karamin murmushi a face din ta Dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ganin su a haka , har wasu ruwa su ka ciko mata a ido , kishi ta rufe mata ido ta kassa ganin kamar da ke tsakanin prince da princess , dan kamar an tsaga kara su ke , yadda ta ke da Aleenah haka ya ke da Princess , Sai dai ita kawai mace ce nan take jikinta ya yi sanyi , ta sunkuyar da kai , ta karaso wajen ta nufi dining table ta ajiye tray din sannan ta juya ta shiga corridor da gudu duk wani takunta ya na sane , kawai ba ya son magana ne sai da ta shiga bedroom din ta sannan ya ce wa Princess " kin gani ko yanzu kin saka ta kuka ? to sai ki je ki ba ta hakuri dan ni ba in da zan je " wata yar karamar dariya Princess ta yi kafin ta saki hannunsa ta mike zaune ta na fadin " Prince , babynka ta cika kishi , yanzu ba ta ga kamar da ke tsakanin mu ba ? " " duk dai laifinki ne , yanzu tashi ki je " ba musu ta tashi ta na dariya ta nufi corridor ta shiga ta na isowa bakin kofar dakin Aleesherh ta jiyo Muryarta ta na kuka a hankali ta shiga cikin dakin ta nade hannayanta a kirji ta zuba mata ido sai kuka ta ke baiwar Allah ta boye fuskarta cikin pillow sai da ta kare mata kallo sannan ta tako a hankali ta na fadin " to shi kuma kukan na minene ? ko ni ma ba na da izinin zama kusa da dan uwana ? " ko sauraron ta Aleesherh ba ta yi ta ci gaba da kukanta a hankali ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta dafa shoulder din Aleesherh ta na fadin " za ki daina kukan nan ko sai raina ya baci ? " sai a lokacin Aleesherh ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta goge face din ta cikin pillow din , ta dago kai a hankali ta kalli Princess ta na zama Princess ta saki wani dan karamin murmushi ta ce mata " kukan kuma na minene ? ni fa sister din ki ce , ta ya za ki yi kishi da ni ? " " sister ? " ta fada cikin rudu " yeah , i'm Nailah or Princess , Twins din Prince , ko ba ki ga mu na kama ba ? " ta kai karshen ta na daga mata gera ita sai yanzu ta samu damar kallon ta da kyau kuma gaskiya su na kama har hazel eyes din su , a sanyaye ta ce mata " amma ni bai fada min ba ya na da twins ba " " shi fa Prince bai cika magana a kan rayuwarsa ba , da kin tambaye shi ya na da sister ko brother zai fada miki , amma in ba ki tambaye shi ba ba zai fada miki ba , now tell me what's your name ? " " Aleesherh " " Aleesherh , sunan ya yi dadi , yanzu tashi mu je ki yi breakfast ko ba ki jin yunwa ? " mikewa tsaye ta yi ta nufi toilet ta shiga wanke face din ta ta yi sannan ta fito , Princess na tsaye bakin kofar dakin ta na jiran ta a hankali ta karaso wajen , riko hannunta Princess ta yi sannan su ka fito bedroom din a tare su ka fito su ka fito parlour , nan su ka tardo shi zaune a dining table ya na shan coffeen da ta hada mishi ba karamin dadi ba ta ji ganin ya na shan coffeen har ta saki wani dan karamin murmushin gefen fuska dining table din su ka karaso Princess ta zauna gefen Prince , Aleesherh kuma ta zauna saman chair din da ke fuskantar tashi ta na kallon shi su na zama ko Junior ya shigo parlourn ya na sallama ya na sanye da suit blue da murmushi a face din sa ya karaso wajen ya na fadin " yau kuma a nan a ke breakfast ? " " Good morning Junior " Princess ta fada ta na murmushi chair din da ke gefenta ya janyo ya zauna ya na fadin " me ki ke yi a nan tun da safe haka ? a ka je ki ka tardo su cikin wani yanayi fa ? " ya kai karshen ya na daga mata gera wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " to ni ina ruwana , kuma Cutie ta ce min Prince na nan shi ya sa na taho wajensa " " shikenan tashi mu tafi " ya fada ya na mikewa tsaye cikin rudu ta ce " mu tafi ina kuma ? ba wajen Prince ka zo ba ? ni tafiya zan yi " girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , ni dama ke na zo nema , akwai wani sabon restaurant da ya bude cikin gari zan so ki raka ni " " da gaske ? su na saida ice cream ? " ta fada cikin yar shagwaba " to ai shagon ice cream ne baki daya , shi ya sa na ce mu je ki raka ni " ya fada dan ya san halinta da mugun son ice cream da sauri ta mike ta sunkuyo a hankali ta manna wa Prince kiss a kumatu ta riko hannun Junior su ka bar wajen , sai murmushi ya ke ya samu abun da ya ke so Prince kuwa ko a jikinsa sai shan coffeensa ya ke , Aleesherh kuma ta tsare su da ido ta na murmushi sai da su ka fita sannan ta ce wa Prince " Baby , amma wannan mijinta ne ko ? " slowly ya dago sexy eyes din sa ya kalle ta , murya cen kassan makoshi ya ce " kin ga na yi miki kama da baby ? " " to ai ni ba wancen babyn na ke nufi ba , ina nufin masoyi haka , ko ka fi son na kira ka da Honey ? " shiru ya yi bai ce mata komai ya dauki wayarsa ya fara latsawa ci gaba da magana ta yi ta na fadin " Honey , ba ka ba ni amsa ba , kuma yaushe za mu tafi honey moon ? " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wai me na ce miki jiya ? " marairaice mishi fuska ta yi kafin ta ce " sorry , ni just ina son mu yi hira ne " shiru ya yi bai ce mata komai ya ci gaba da aikinsa , ya ga alamun wannan bakinta bai iya shiru ba , da ma Aleenah ya fadawa Al-Sayid ya aura mishi dan ya ga ta fi wannan sanyi ya yi nisa duniyar tunaninsa kawai ya ji ta zauna a kujerar da Princess ta tashi , a hankali ta kai lips din ta saman kumatunsa ta manna mishi kiss nan take ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarsa lokacin da Princess ta yi mishi kiss ba abun da ya ji , yanzu kuma ita da ta yi mishi har wani shock ya ji cikin jikinsa ita kuwa ba ta ma san ya na yi ba , ta janyo tray din breakfast din da ta shirya mishi ta fara cin kayanta dan ta lura coffeen ne kadai ya ke bukata slowly ya dago kai ya kalle ta , ta na cin abincin cike da nitsuwa nan take ya tsargu da kallon ta , har ya manta aikin da ya ke da