← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 61

Sashe 5

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta tsufa ne ? ko kuma son da na ke miki ki na tunanin shi ya tsufa ? ki shirya kawai mu tafi honey moon , wannan karan zan ba ki mamaki " ya qarashe maganar ya zagayo da hannunsa a kugunta ya matse ta turo dan karamin bakin nan nata ta yi kamar ya ce zai yi mata Kiss , cike shagwaba ta ce " wai kai ba ka gajiya ne Baby ? ni gaskiya ba wata Honey Moon da zan tafi " " ta ya ki ke so na gaji My Cutie ? kullum da inki sabo ya ke zame min , kamar ma shi ne karo na farko da na ke dandana zumarki , please ki yarda mu tafi , na shirya miki surprise " " wacce irin surprise ? " ta fada ta na sakin wani kyawatacen murmushi bai ce mata komai ba ya mike tsaye da ita a jikinsa bai dire ta ko ina ba sai saman bed din su , ya haye saman ta ya yi mata runfa da fafadar kirjinsa , ya fara manna mata kiss ko ina a saman face din ta ita dai sai dariya ta ke yi tsawan shekaru yanzu amma kullum Malik da sabon salo ya ke zo mata , har yanzu ta kassa sabawa da romance din sa , wata rana ya yi mata da dadi wata ranar kuma sai ta dinga yi mishi kuka ta na rokonsa ta kyale ta ta na haka kawai sai jin hannunsa ta yi saman breast din ta da sauri ta ce mishi " ya isa haka baby , ka fara yin breakfast ka ga har karfe tara ta yi " a hankali ya dago kai ya zuba mata wadanan shanyayun idanunsa kamar na dan maye ya ce " ki fara ba ni breakfast din kafin na je na yi " marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " please baby , so ka ke sai ka gama da ni na koma tsohuwa sannan za ka hakura ka bari " ta fada ta na turo dan bakin nan nata ai kuwa bai yi wani tunani ba ya kai nasa a sama ya manna mata kiss ya na fadin " ba za ki taba tsufa ba a idona My Cutie " murmushi mai dan sauti ta yi , har ta bude baki za ta yi magana wayarsa da ke saman bedside drawer ta fara ringing a tare shi da ita su ka kai kallon su wajen bedside drawer a hankali ya sauka da ga saman ta , ya zauna bakin gadon , ya kai hannu ya dauki wayar wani dan karamin murmushin gefen fuska ya saki kafin ya dauki kiran , ya kai wayar a kunne ya na sallama kassa kassa kafin ya daura da cewa " Ammiena , ina fatan ki na lafiya ? " Inaya na jin ya ce Ammie ta gane da MALIKAT INAS ce ya ke waya , da sauri ta mike zaune , ya haye saman bayansa ta na fadin " Ammie , na yi kewar ki sosai " a hankali ya sauko wayar ya daura saman Hand free dai-dai lokacin da MALIKAT INAS ke fadin " ni ma na yi kewar ki sosai MALIKAT , ya ki ke da Twins di na ? " " su na nan lafiya Ammie " ta fada ta na zagayo da hannayanta a wuyansa cikin nitsuwa ya ce " Hope ki na lafiya Ammie , da Rianna ? " " mu na lafiya , ya jikin naka ? " " da sauki sosai Ammie , kamar ma ban taba ciwon ba " ya fada ya na juyawa ya mannawa Inaya kiss saman kumatu , dama ta kontar da kanta saman shoulder din sa " Alhamdoulilah , yanzu fada min yaushe za ku zo ? tun shekaran jiya na ke jiran ku amma shiru " Fadin MALIKAT INAS cikin sanyin murya cikin rudu ya ce mata " zuwa kuma Ammie ? ke ma kin san dai cikin watan azumi mu ke zuwa , ga shi yanzu azumi saura wata biyu ma , ba wani tsayi ai " " ban gane ba , kenan ba za ka zo ka duba jikin Diya ba ? " a rudu ya ce mata " Diya kuma ? wani abu ya same shi ne ? " " Nawfel , kar dai ka ce min ba ka da labarin abun da ya same shi , tsawan sati guda yanzu " a rude ya ke fadin " Ammie please fada min , wlh ban san abun da ke faruwa ba , duk kin sa hankalina ya tashi , ba dai wani abu ya same shi ba ko ? " sai da MALIKAT INAS ta dauki lokaci kafin ta ce mishi " satin da ya wuce ne , na san stress ya yi mishi yawa ne har jininsa ya hau , bayan mun kai shi likita ne doctor ke cewa wai bangaran hagunsa ya yi paralyze , amma Alhamdoulilah yanzu ya samu sauki har ya na iya takawa da shi " kalmar shahada Malik ya shiga karantawa , ya na marairaice fuska ya ce " haba Ammie , ta ya za ku yi shiru ba ku fada min ba , ai da tun ranar da ya fara ciwon ya kamata ku kira ku fada min , sai da ku ka bari har ya samu sauki sannan za ku fada min , Diya fa dan uwana ne , in wani abu ya same shi ba zan iya jurewa ba , yanzu wane hali ya ke ciki ? " cikin sanyin murya MALIKAT INAS ta ce " na yi tunanin ka na sane da abun da ke faruwa a nan , shi ya sa kawai ban kira ka ba na fada maka ina jiran zuwanku , amma yanzu alhamdoulilah har ma ya koma part din sa " wani dan karamin tsaki Malik ya ja kafin ya ce " shikenan , in sha Allah gobe mu na nan zuwa " " shikenan , Allah ya kawo ku lafiya , ka gaishe min da babies di na " ta fada cikin sanyin murya da ga nan su ka yi sallama ya sauko wayar ya ajiye saman bedside drawer a hankali ya juya ya kalli Inaya da duk ta yi sanyi a jikinsa a sanyaye ya ce mata " tashi na je na saka kaya yanzu " noke mishi kafada ta yi ta na turo dan karamin bakin nan nata murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " to me ki ke so yar babyna ? " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " ni kai na ke so , I love you " " i love you too , but now let me make my cloths you know how is our princess , yanzu za ta fado mana kamar da ga sama " ai kam bai gama rufe bakinsa ba ya jiyo Muryarta ta na fadin " me kuma na yi ? " " kashhh ! " ya fada ya na dafe forehead din sa da hannu ya lumshe idanu ita dai Inaya dariya ta fara yi ta shiga goga face din ta a shoulder din sa da sauri ya mike tsaye ya na fadin " ba za ku kashe ni ba ku biyun nan " ya fada ya na fara takawa ya shiga dressing room da kallo su ka raka shi har sai da ya shiga sannan su ka yi dariya , amma lokaci guda Inaya ta tsuke fuska ta ce mata " me ki ke yi a nan ? ba ki iya knocking ba ? " " ba ke ce ki ka gudo da bowl din nan ba , ni kuma ina son na ga me ke ciki " ta fada ta na turo dan bakin ta , dai ita dole sai ta ga abun da ke cikin bowl din , ( ni a nawa sanin Princess sam ba ta da hayaniya , yanzu kuma ita ce mai rigimar , tukunna ma ina Prince ni har yanzu ban gan sa ba ) hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " Nailah , fice min da ga daki tun ban bata miki rai ba " ta fada cikin tsare gida wai su Inaya an san minene tsare gida a na ba da umarni daga kai sama Princess ta yi ta na fadin " Daddyyyyyy ! ! ! ! ! " ta fada da mugun karfi ba shiri Malik ya fito da ga cikin dressing room ko button din shirt din sa bai gama sakawa ba , a tunaninsa wani abu ne ya faru da yar babyna tasa " Princess , what happened ki na min irin wannan kiran ? " ya fada ya na karasowa wajen ta ya na kokarin saka button din rigarsa nuna mishi bowl din da ke saman bedside drawer ta yi , ta na turo dan bakin nan nata ta ce " Daddy , ce wa Cutie na yi ta bari na ga abun da ke cikin bowl din nan , amma ta ce min na fice mata da ga nan ko ta bata min rai " ta fada cike da shagwaba ta na hura kumatu wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya kalli Inaya , ya na juyowa ko ta wurga mishi wani mugun kallo ta na tsuke fuska ba dan ya so ba ya shanye abun da ya zo fada , ya juya ya riko hannun Princess su ka fice bedroom din , gwara ya je ya rarrashe ta da ya ja fushin Cutien sa , ya san in ta yi fushi yau tasa ta kade Inaya kuma su na fita ta ida Hayewa gadon ta konta ta lumshe idanunta jim kadan Malik ya dawo cikin dakin ya na sallama ba tare da ta bude idanunta ba ta amsa mishi sallamarsa a hankali ya karaso bakin gadon ya kai hannu saman bedside drawer zai dauki bowl din da ga ajiye ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " ka san Allah ? ka dauki bowl din nan ka kai mata , ku da abinci sai dai na restaurant dan ba zan sake shiga
Chapter 5 · 0% Book details