← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 61

Sashe 41

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zauna mana haka kamar gidanku ? " wani kyawatacen murmushi Aleesherh ta saki kafin ta ce " I don't know too , in ki ka samo amsar sai ki zo ki fada min , ni ma zan so na sani " ta kai karshen ta na kallon Prince hararrar ta sama da kassa Azmat ta yi kafin ta ja wani dan karamin tsaki , su na zamansu ta wani zo ta katse musu nitsuwarsu Aleesherh kuwa ko a jikinta , a hankali ta dafa laps din Aleenah , a sanyaye ta ce mata " shikenan , komawarki , ni ma part di na zan koma yanzu " cikin rudu Aleenah ta ke kallon ta , alamun ba ta gane abun da ta ke nufi ba da wutsiyar ido ta mata alamun ta bar wajen wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " shikenan , but next time in kin san ba zama za mu yi ba kar ki kara janyo ni " ta kai karshen ta na kai hannu ta dunguri kanta sannan ta mike ta bar wajen wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi ta na dan sosa wajen da Aleenah ta zungure ta shi dai Prince kamar babu shi a wajen , gwara ya yi shiru dan in ya ce ya biye musu duk sai sun kwana a word room Aleesherh kuwa sai da ta bari Aleenah ta yi nisa sosai da wajen , kadan ya yi saura ta isa Part din MALIKAT INAS , Ta mike tsaye a hankali ta juya za ta bar wajen taku biyu ta yi carpet din wajen ya tade ta , dip ta fadi a kassa baki daya ta na saki kara , har sai da kanta ya bugu a kassa nan take Azmat ta bushe da dariya har da tapi Prince kuwa ya na jin kararta ya saki wayarsa da sauri ya mike ya nufe ta , ya sa hannayansa dukka biyu ya tado ta ya na fadin " ba ki ji ciwo ba ? " kukan shagwaba ta sakin mishi ido a rufe ta dafe forehead da hannu guda ta na fadin " Honey , kaina ya bugu " hannu ya kai ya riko hannunta ya janye shi da ga saman forehead din ta , nan ya ga wajen har ya yi jazir kun san yanayin farar fata ba wata juriya ne da ita ba cikin sanyin murya ya ce mata " sorry , let's go zan shafa miki pommade kar wajen ya ja jini " gyada mishi kai ta yi a hankali , mikewa tsaye ya yi ya na rike da hannayanta biyu ya taimaka mata ta mike tsaye wata siririyar kara ta saki ta na neman komawa ta fadi da sauri ya riko kugunta ya janyo ta jikinsa ya na tambayar ta mi ya faru " Honey , ina ga kafata ta bugu , zafi na ke ji " ta fada cike da shagwaba " i have thought you was strong " ya fada ya na daga mata gera hararrar shi ta yi kafin ta raba jikinta da nashi , ta juya a hankali ta taka da kafar ta bar wajen ta na ingishi sai da ya bari ta yi wajen taku uku sannan ya juya ya dauki wayarsa ya saka cikin aljihunsa ya juya ya bi bayanta ya na rike da hannayansa a baya , sai da su ka kusa fita garden din sannan ya sa hannayansa biyu ya dauke ta cak kamar baby a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kontar da kanta a kirjinsa , cikin nitsuwa ya ci gaba da takawa har su ka shiga part din su ita dai Azmat ta zama yar kallo , ta na ganin abun kamar a film , kenan wannan ita ce matar da ya auro ? kuma da ga gani ya na son ta tun da har ya damu da ita , haka dai ta yi zaune ta zuba musu ido ta ma rasa abun da ke yi mata dadi PRINCE sai da ya kai ta har cikin bedroom din ta sannan ya zaunar da ita saman gadon , ya jingina bayanta da forehead din gadon sai a lokacin ya lura da hawayen da ke saman face din ta , har hancinta ya yi ja , sai jan majina ta ke a hankali ya zauna bakin gadon ya na kallon ta ya ce " ashe kin iya kuka " ko sannu ba ta ce mishi ba ta kauda kai gefe ta kai hannu ta fara goge hawayenta ta na a haka ta ji hannunsa saman kumatun , wata boyayyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ji saukar lalawsan hannunsa saman face din ta , kamar fatar baby goge mata hawayenta ya fara yi a hankali ya na fadin " ba zan hana ki kuka ba in har ki na jin zafi , amma ba zan so ki bari wani ya ga rauninki ba , ba zan so wani ya samu damar tozarta ki cikin masarautar nan " ko sannu ba ta ce mishi ba ta kauda kai gefe janye hannunsa ya yi sannan ya bude box na biyu na bedside drawer ya fiddo A box , ya ajiye ta saman bedside drawer sannan ya bude ya fiddo wata pommade ya bude ya zuba kadan a yatsarsa sannan ya dago yatsar kai tsaye saman forehead din ta ya kai ya shafa mata a hankali dan rumtse idanunta ta yi da karfi dan ba karamin zafi ta ke ji ba " sorry " ya fada murya cen kassan makoshi dan ya ga yadda ta lumshe idanunta sai da ya gama shafa mata sannan ya janye hannunsa ya ce " miko kafarki na shafa miki " slowly ta ware idanunta ta juyo da kanta ta kalle shi , har wani sanyi ta ji cikin zuciyarta ganin yadda ta tsare shi da ido kamar ba ta da Niyyar miko mis hi kafar a hankali ya dan ja da baya , ya kai hannu saman kafarta a hankali ya yi sama da gown din ta har zuwa guyiwa sannan ya zuba pommade kadan a yatsarsa , ya shafa mata saman kafar cike da kula har wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta na kallon shi ta saki wani cool murmushi sai da ya gama shafa mata sannan ya tashi ya rufe pommade din ya meda cikin A box , ita ma ya meda ta cikin bedside drawer sannan ya nufi toilet din ta ya shiga ya wanke hannunsa, ya fito kai tsaye ya nufi kofar fita da sauri ta ce mishi " Honey " tsaya wa ya yi ya juyo a hankali ya ce mata " ki daina kira na da wannan sunan , ba na so " " to da me ka ke so na kira ka ? " " Prince " ya fada a takaice kafin ya juya zai fita da sauri ta sake taro shi ta na fadin " wannan sunan da shi kowa ya ke kiran ka , ba zan iya kiran ka da shi ba , ba gwara na dinga ce maka Big bro ba ko Boss " slowly ya juyo ya zuba mata wadanan hazel eyes din nashi , to shi ba gwara ta ce mishi Prince da Big bro sai ka ce wanda su ka fito ciki guda daga mishi gera guda ta yi ta na " lafiya ka na yi min irin wannan kallon Habibi ? " girgiza mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya fice da sauri dan ya san in ya tsaya sai ya shake ta ba shi da labari , a ce yarinya bakinki ba shi da linzami ina ga sai ta fasawa Prince zuciya , da alamun shi ma ya fara kamuwa da son ta, amma ya ki yarda , Team Aleesherh sai a taimaka ni na tafi wajen big boss ) MALIK Slowly ya ware idanunsa ya shanyayun idanunsa da su ka yi jazir , da alamun barcin bai ishe shi ba , ko kuma dai har yanzu sha'awar jiya ce ba ta gama fita ba a hankali ya juya ya kalli gefensa ya ga shi kadai ne saman gadon wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike zaune ya kai hannu ya dafa forehead din sa , da karfi ya ce " Cutie ! ! ! ! Where are you ? " ya na gama rufe bakinsa ya jiyo Muryarta cikin toilet ta na amsa mishi kiransa , sannan ta fito daure da towel a kirjinta , gashin kanta duk a jike a hankali ta karaso wajensa ta na fadin " baby , lafiya ka na min irin wannan kiran ? sai da ka ba ni tsoro wlh " a sanyaye ya ce mata " Cutie , marata ciwo ta ke min wlh " zama ta yi bakin gadon ta kai hannu a hankali saman mararsa ta shafa ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya koma ya konta ya daura hannu saman forehead wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " sai da na ce maka ka yi a hankali amma ka ki , yanzu wa gari ya waya ? " " Cutie , ni fa ba na son moral din nan da ki ke min kullum " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta sunkuyar da kanta a hankali ta manna mishi kiss saman mararsa sannan ta mike tsaye ta na fadin " Allah ba ka hakuri , tashi ka yi wanka , zan shirya maka breakfast " har ta juya ya riko hannunta ya janyo ta jikinsa da karfi ta fado saman kirjinsa zagayo da hannayansa ya yi a bayanta ya matse ta a jikinsa tsam ko motsin kirki ba ta iya yi marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " baby , me kuma ya faru ? ina son na je na shirya " " ta ya za ki tafi ki bar ni a haka ? kuma kin sani ba na jin dadin ki tashi ki kyale ni ina barci , amma ke kullum haka ki ke min " " shikenan na ji , yanzu tashi ka shiga ka yi wanka, ba za ka je fada ba ? " "
Chapter 41 · 0% Book details