← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 61

Sashe 22

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta gan ta da Uniform din Hotel din kamar ta yi kuka ta nufi kofar fita Hotel din ta fice da gudu idanunta cike da ruwa ALEENAH zaune ta ke tsakiyar bed din su sanye da wata yar karamar rigar barci kamar baby doll alamun yanzu ta farka da ga barcin ta na rike da wayarta ta na faman latsawa cikin konciyar hankali ta na a haka kawai ta ga Aleesherh ta fito da ga hanyar sirrinsu , idanunta cike da ruwa da sauri Aleenah ta sauko da ga saman gadon ta na fadin " Alee ? me ya faru na ga ki na kuka ? " " ba ya nan , ya tafi , ban san in da zan samo shi ba yanzu " ta fada ta na karasowa wajen gadon ta haye ta yi rub da ciki ta na sakin kuka wani dan karamin tsaki Aleenah ta ja kafin ta karaso bakin gadon ta zauna ta na fadin " don Allah ki kontar da hankalinki , kukan kuma na minene ? " " Aleen , ba za ki gane ba , wlh ina son saurayin nan , har cikin zuciyata na ke jin san , i don't know how ya sace zuciyata haka , da na sani da tun farko ban sake wa abun da zuciyata ke fada min ba , ga shi yanzu na rasa shi har abada " " Allah bai kaddara za ku kasance tare ba , ki yi hakuri , in sha Allah za ki samu wanda ya fi shi " Aleenah ta fada ta na son kontar mata da hankali , ta san yar uwarta ba karamin abu ba zai sa ta ce ta na son mutum , asali ma ko irin wannan friends ba ta da su , ko a school ba ta sakewa kowa fuska bare har a yi mata maganar abota , duk wanda ta bude baki ta na so har ta zubar da hawaye saboda shi ba karamar sa'a ya yi ba , ta so ta samu abun da ta ke so ko da wannan karan ne kawai amma Allah kadai ya san abun da ya shirya musu nan gaba , may be su sake haduwa may be ta hadu da wanda ya fi shi a hankali Aleesherh ta mike tsaye ta nufi toilet ta shiga ta bar Aleenah zaune a nan sai da ta shiga kawai na ga Aleenah ta fara zubar da hawaye , da sauri ta kai hannu ta goge hawayen kafin ta dauki wayarta ta ci gaba da latsawa a haka har Aleesherh ta fito da ga cikin toilet din sanye da bathrobe ta nufi wardrobe ta shiga mikewa ita ma Aleenah ta mike ta shiga toilet din ta yi wanka , ta fito sanye da bathrobe ita ma nan ta isko Aleesherh zaune bakin gadonsu rike da wayarta ta na latsawa ta daure fuskar tamau to fa na izzar sun motsa , Aleenah ke fada cikin zuciyarta wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta nufi wardrobe ta shiga MASARAUTAR SAUDIYA INAYA zaune su ke cikin parlourn MALIKAT INAS , tare da RIANNA da MALIKAT INAS da Nesrine Faaz ya na makale da RIANNA ko sakin ta ba ya yi kamar ita ce mahaifiyarsa , ita kuwa sam ba ta damu ba sai jan sa a jiki ta ke kamar yaronta na gaske, sai hira su ke cike da annashuwa sun saka Inaya tsakiya sai tsokanar ta su ke su na a haka su ka jiyo Muryar Prince cen kassan makoshi ya na sallama a tare duk su ka juya su ka kalli saitin kofar a hankali ya shigo ya na sanye da wasu suit white color ma su mugun kyau ya daure gashin kansa a baya , amma ya sako wasu a gefen dama kadan rufe mishi ido MALIKAT INAS na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " wayyo shalelena , zo na rungume ka " ta fada ta na bude mishi hannayanta noke mata kafada ya yi ya na fadin " ni ba baby ba ne ku kyale ni , kuma duk fushi na ke da ku " " fushi kuma shalelena ? me na yi ? " MALIKAT INAS ta fada cikin sanyin murya " ba ku ku ka sa na dawo ba , ni gaskiya komawa ta zan yi ki cewa Daddy ya kyale ni na yi aikina " wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " shikenan zan yi mishi magana yanzu dai zo rungume Ammien ka " ba musu ya tako a hankali ya rungume ta ya na fadin " na yi kewar sosai Ammie " " ni ma na yi kewar ka shalelena , fatan ka na cikin koshin lafiya ? " " i'm fine Ammie " ya fada ya na raba jikinsa da nata a hankali ta dago kai ta manna mishi kiss a forehead ta na murmushi a hankali shi ma ya sunkuyo ya manna mata kiss saman kumatu sannan ya kalli RIANNA , sai da ya ji zuciyarsa ta buga lokacin da idanunsa su ka sauka saman Faaz , ga shi ko shi ma ya tsare shi da ido kamar zai cinye shi " momy , ba dai replaced di na ki ka yi ba da wannan abun ? " ya fada ya na nuna Faaz wata yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce mishi " kai ma ka sani ba zan iya ba " " shi ne ki ka ki taho wa ki rungume ni ki na rike da Babynki ? shikenan ni ma da ga yau kar ki sake ce min babynki " ya na gama fadar haka ya nufi Nesrine ya rungume ta da murmushi a face din ta ta ce " sannu da zuwa My Prince " bai amsa mata ba ya dago da ga jikinta " haba my Baby , yanzu fushi za ka min ? " RIANNA ta fada cikin sanyin murya " ba kin yi sabon baby ba , ni kyale ni mun bata " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kalli Faaz ta ce " Faaz sake ni one minute " ai ko kara matse ta tsam ya yi ya na fadin " no , ni sai dai mu tafi tare , ba zan sake ki ba " wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta kalli Prince ta na marairaice mishi fuska kauda kai ma ya yi kamar bai gan ta ba ya nufi Inaya da tun lokacin da ya shigo ta tsuke fuska A hankali ya tsugunna a gabanta ya riko hannayanta ya na kallon face din ta , ita ko ta kauda kai gefe murya a sanyaye ya ce " momy , ba za ki kalle ni ba ? " kwace hannayanta ta yi ta na fadin " tashi ka koma in da ka fito tun da ni ban da mahimanci a wajen ka " " haba momy , ta ya za ki ce haka ? kin san yadda na yi kewar ki kuwa ? yanzu na dawo kuma kin juya min fuska " " to ni na ce ka tafi ? da ka na so na da gaske kamar yadda ka ce da ba za ka yi wannan tsawan lokacin ko kira na ba ka yi , ni kyale ni na yi fushi da kai , kuma ko hakuri ka ba ni ba zan hakura ba " riko kunnuwansa ya yi , ya yi Kneel down , ya na fadin " I'm sorry my Cutie , please forgive me , ba zan sake ba , ba na jin dadin fushin da ki ke min " " Zan yi hakuri amma da sharadi " ta fada ta na dawo da kallon ta gare shi da sauri ya ce " Eh na yarda ko ma minene " wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta nuna mishi gefenta da hannu a hankali ya mike ya zauna geffenta hannu ta kai saman face din sa , ta dago kai ta manna mishi kiss a forehead ta na fadin " ka sani ba ka da kirki ko ? ka san yadda Daddynka ya yi kewar ka kuwa ? kullum sai ya kira lambarka ya na sa ran za ka dauka , amma shi ne za ka gudu ka bar mu " " I'm sorry Cutie , i promise ko zan sake tafiya ba zan wuce one week zan dawo " " you promise ? " ta tambaye shi ta na murmushi gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba kara fadada murmushinta ta yi kafin ta matso a hankali ta rungume shi ta na fadin " na yi kewar ka sosai my baby " " ni ma haka Cutie " ya fada ya na kontar da kansa saman shoulder din ta su dai MALIKAT INAS da sauran sun zuba musu ido gwanin burgewa ________________
Chapter 22 · 0% Book details