Sashe 13
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta sha jinin jikinta ta fara muzurai da idanu daga mata gera ya yi ya na fadin " uhm , sai kin yi mi ? ida maganarki " wasu yawu ta hadiye ta na girgiza mishi kai alamun ba komai " Ah Haba ? ki fadi maganarki , ko sai mun je gaban Daddyn naki na fada mishi abun da yarinyarsa ke yi a wajen Daular ? haka ki ke so ? " da sauri ta girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka ta ce " a'a , don Allah ka yi hakuri , don Allah " ta fada ta na marairaice fuska " miko min littafina " da sauri ta duka ta dauki littafin ta sa Alkyabarta ta goge shi sannan ta mika mishi ta na fadin " don Allah kar ka fada mishi , ka ji ? " ta fada ta na marairaice fuska hannu ya kai karbi littafinsa , ya na shirin magana ya ga dayar ta iso wajen ta na tambayar lafiya dai'dai lokacin da idanunta su ka sauka saman Prince da ke tsaye ya tsare su da ido nan take ita ma ta sha jinin jikinta ta na muzurai da idanu a hankali ya nade hannayansa a kirji , ya matse gera ya ce " wacece cikin ku ta shigo min bedroom a hotel ? " shiru su ka yi ba su ce mishi komai ba sai muzurai su ke da idanu " ba za ku ba ni amsa ba ? " ya fada ya na matse gera da sauri ta farkon ta nuna kanta ta na fadin " ni ce , don Allah kar ka fadawa Daddy " ta fada ta na marairaice murya wani dan karamin tsaki Aleesherh ta yi ta na fadin " ke don Allah yi wa mutane shiru , ba abun da zai yi , wuce mu tafi " ta fada ta na riko hannunta da sauri ta ce mishi " ka yi hakuri don Allah " " Aleenah , ki daina ba shi hakuri ba abun da zai yi , wuce mu tafi " Aleesherh ta fada ta na jan Aleenah su ka raba ta gefensa su ka bar wajen ita dai Aleenah sai marairaice fuska ta ke ta na tsoron ya fadawa Al-Sayid ta shiga mishi bedroom , har a hotel ma , ta san shikenan ta su ta kare ba zai kyale su ba ita kuwa Aleesherh ko a jikinta ko hakuri ba ta ba shi , ta san barazana ce kawai ya ke musu dan ya ba su tsoro ko sannu Prince bai ce musu ba ya ci gaba da tafiyarsa , har ya karaso parking space din masarautar , ya shiga motarsa ya fice masarautar, kai tsaye hotel din da ya sauka ya koma , ya na isowa bedroom din sa ya ga P.A din sa tsaye cikin bodyguards din sa ko sannu bai ce mishi ba ya shiga bedroom din sa bin bayansa P.A din ya yi , ya shigo ya na sallama kafin ya ce " Good morning sir " " me ya kawo ka ? " Prince ya fada a takaice ya na cire sneakers din kafafunsa cikin nitsuwa P.A din ya fara fadin " Sir maganar meeting din nan ne " cikin nitsuwa ya katse shi da cewa " ku soke ta kawai har na samu dama , next week zan koma Saudiya , in na je cen zan san abun yi " " amma sir tun last week mu ka shirya zaman nan ya za a soke shi lokaci guda haka ? " dago kai Prince ya yi a hankali ya zuba mishi wadanan hazel eyes din nashi irin na Malik ya dan dauki lokaci kafin ya ce " ku soke ta kawai na ce , ba shawara na ke ba ka ba , now get out please ina son na huta " " okay sir , ku na bukatar wani abu na sa a kawo muku ? " " fruits " ya fada a takaice kafin ya mike ya nufi toilet ya shiga ya na shiga P.A din nashi ya fito bedroom din ten minutes bayan fitar sa wani server ya shiga rike da tray din fruits, kai tsaye ya nufi table din gaban gadon ya ajiye kafin ya juya ya fice after SOME minutes Prince ya fito da ga cikin toilet din sanye da bathrobe kai tsaye ya wuce wardrobe jim kadan ya fito sanye da wani trouser three cuter da t-shirt , ya saki wannan smooth hair din nasa ya haye gadon kai tsaye ya yi rub da ciki , ba jimawa barci ya yi gaba da shi dan a gajiye ya ke sosai DAULAR YEMEN ALEESHERH konce ta ke rub da ciki saman royal bed din ta , cikin wani makeken bedroom hade da parlourn baki daya ma dan cen gaban gadon na hango wasu tsadadun sofas irin na gidan sarauta har da Tv ta na konce rike da wani book ta na zane , wayar ta na gefe music na tashi , ta na rera waka cikin konciyar hankali cen na Hango Aleenah tsaye bakin gadon sai kai kawo ta ke yi , duk a tsorace ta ke kar a je Prince ya fadawa Al-Sayid wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta zauna bakin gadon ta kai hannu ta dan bubuga kafar Aleesherh ta na fadin " ke Aleesh , please ki tashi, wlh hankalina ya kassa konciya , kar a je ya fada wa Daddy, " a takaice Aleesherh ta ce " ba abun da zai yi " " why ? ba ki sani ba dai " Aleenah ta fada ta na marairaice fuska " you know what ? i'm falling in love for him , he is so handsome , really i love him " Aleesherh ta fada cikin ko in kula zaro idanu Aleenah ta yi ta na kallon ta , a rude ta bude baki ta ce " kin san abun da ki ke fada kuwa ? love fa ki ka ce ? how ? " " Aleen i know what i say , wlh na kassa cire lokacin da na gan sa a kasuwa , kar ki so ki ga yadda ya taro ni , sai ki ce jarumin wani film " ta na gama fadar haka ta janyo pillow ta rungume ta na sakin murmushi a hankali Aleenah ta kai hannu saman wuyanta , ta janye ta daura saman forehead din ta cikin rudu Aleesherh ta ce mata " lafiya ? " " dubawa na ke na ga in ba zazzabi ne ya kama ki ba " wani dan karamin tsaki Aleesherh ta ja kafin ta sa hannu ta buge hannun Aleenah janye hannunta Aleenah ta yi ta na fadin " ba ki da hankali wlh , mutumin da ko sunansa ba ki sani ba ki ce kin kamu da son shi " " and so what ? i'm serious i love him , kuma ke za ki taimaka min na samu abun da na ke so " " ni kuma ? " Aleenah ta fada cikin rudu gyada mata kai Aleesherh ta yi ta na fadin " Eh , ke , yanzu fara fada min a wane hotel ya ke zaune ? " da sauri Aleenah ta girgiza mata kai ta na fadin " nooooo , ba ruwana a cikin wannan maganar " ta kai karshen ta na kokarin tashi da ga saman gadon da sauri Aleesherh ta mike ta bi bayanta ta na fadin " please my lovely sister , yanzu ba za ki iya taimakawa sister din ki ba ta samu abun da ta ke so ? kuma ai ba ke za ki tafiya ba , ni zan je please ki fada min " a haka su ka shiga zagayen bedroom din , Aleesherh na rokon ta ta fada mata sunan hotel din Aleenah kuma ta kafe ta ce ba za ta fada ba ta na tsoron ta janyo musu matsala , ita ko yanzu a tsorace ma ta ke su na a haka wata mata ta shigo dakin ta na sallama da gudu Aleenah ta gudu ta boye a bayanta ta na fadin " Anna , ki ce mata ta kyale ni tun dazu ta ke neman ta dake ni " dan zaro idanu Aleesherh ta yi ta na kallon ta ta ce " ke dai yarinyar nan ba ki tsoron Allah , yaushe na ce zan dake ki ? " wata yar karamar dariya Anna ta yi kafin ta ce " ya isa haka shikenan , yanzu ku je bangaran Mai dakin Gabas , mahaifinku na jiranku a cen " " Daddy kuma ? " su ka fada a tare a dan razane gyada musu kai ta yi ga na fadin " ku yi sauri ya na jiran ku " ta qarashe maganar ta na juyawa ta fice part din kallon juna su ka tsaya yi su na zaro idanu cen sai Aleenah ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka ta ce " kin gani ko ? sai da ya fadawa Daddy , yanzu Allah kadai ya san abun da zai mana " tsaki kawai Aleesherh ta yi kafin ta fara takawa ta raba ta gefenta ta wuce ta na fadin " tsaya nan , ni kin ga tafiyata " da sauri Aleenah ta bi bayanta su ka fito part din kai tsaye part din Mai dakin Gabas su ka nufa wato Sayida Ahlame wadda ita ce mahaifiyarsu kuma uwar gida ga Al-Sayid da Sallama su ka shigo parlourn , murya a sanyaye kamar mutanan arziki su na zaune ccikin parlourn , Al-Sayid ya cire Alkyabarsa , Sayida Ahlame kuma na zaune geffensa da Alkyabarsa saman cinyoyinta da alamar yanzu ya shigo wajen sai da su ka karaso wajen sofar sannan su ka zauna saman guyiwowinsu su na fadin " sannu da hutawa Daddy , sannu da hutawa momy " su ka fada a tare cike da girmamawa a takaice Al-Sayid ya ce musu " da ga ina ku ke ? " " Daddy mu na part din mu mana , shi ne Anna ta je ta ce wai ku na neman mu " Fadin Aleesherh " kafin nan ina ku