Sashe 6
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kitchen din nan ba " ba dan ya so ba ya janye hannunsa , ya zauna bakin gadon cikin sigar rarrashi ya ke ce mata " please Cutie , ke ma kin san halin Princess in ba ta samu abun da ta ke so ba , kuma fruit salad din nan ta shiga ranta , please ki bari na kai mata " mikewa zaune ta yi ta zuba mishi ido , cikin tsare gida ta ke fadin " shikenan ? wai me ya ka ke biye mata ne ? ba fa yarinya ba ce shekarunta 30 , a yanzu ya kamata a ce ta na da aure har da babys , amma don Allah dubi ta na nan zaune da mu bayan shagwaba ba abun da ta ke , duk ka bi ka bata ta " " to ya ki ke so na yi in ban shagwaba ta ba ? shagwababen nawa ya gudu ya bar ni , duba tsakani da Allah tsawan three months ba mu da labarinsa , sai dai ya turo mana letter ya ce kar mu damu ya na nan lafiya , wannan shi ya koma Exiled Prince ba ni ba " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta daura hannunta saman face din sa ta na fadin " kar ka damu , in sha Allah zai dawo mana cikin koshin lafiya , kawai ya na son ganin ya duniya ta ke , ya na son bude ido , kar ka ga laifinsa , yanzu dai ya kamata ka yi min maganin wannan shagwababiyar dan gaskiya ba zan ci gaba da zama da ita a gida guda ba a to " ta qarashe maganar ta na janye hannunta , ta koma ta konta wata yar karamar dariya ya yi kafin ya mike ya dauki bowl din ya juya ya fice da shi ya na fitowa ko ya ga Princess tsaye gefen kofar dakin ta nade hanayanta a kirji , ta na faman turo baki mika mata bowl din ya yi ya na fadin " Take it , in kuma ki bari ta kama ki ba ruwana " da sauri ta kai hannu ta karbi bowl din ta na washe baki kafin ta dan dago ta manna mishi kiss saman kumatu ta juya da sauri ta bar wajen da kallo ya rakata har sai da ta gama saukar stair din Sannan ya juya ________________