← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 61

Sashe 49

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

, amma bai yi tunanin Ammie ce ba , tun ya na karami ba karamin so ta ke nuna mishi ba , duk ita ta sangarta shi lokacin da ya ke karami har ya ke yi wa Malik jaraba , duk yawancin shawarwarin da ya yanke cikin rayuwarsa da sa hannunta , ko auren nan nashi da Aleesherh , ita ta kwantar mishi da hankali ta ce ya yarda cikin kankanin lokaci zai sha u da ita , ga shi ko maganarta ta tabbata , yanzu kuma a ce ta tafi lokaci guda ya yi nisa duniyar tunaninsa ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Prince , ya kamata ka tafi wajen Daddynka , na san zai ji sanyi idan ya gan ka , ya na Floor na hudu " gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juya ya fice ya na taku kamar an zare mishi lakar jiki ya na fita Inaya da Princess su ka koma su ka zauna bangaran Aleesherh kuma kai tsaye bedroom din Aleenah ta wuce ta na yi mata sallama ta na zaune tsakiyar gadon idanunta sun yi jazir da alamun kuka ta sha cikin rudu Aleesherh ta karaso wajenta ta na fadin " Aleen , lafiya na ga idanunki sun yi ja haka ? " ta kai karshen ta na zama bakin gadon wani dan karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta ce " Amarya , sai yau ki ka yi niyar dawowa " " please Aleenah , ki ba ni amsar tambayata , me ya faru ne ? na ga kowa yanayinsa kamar sun yi kuka " " Kakar mijinki ce ta rasu Jiya " " innallillahi wa'ina illaihi raji'un " Aleesherh ta fa a a dan razane ta na zaro idanu shi ya sa ta ga duk mutanan wajen sun yi sanyi , kamar an aiko musu sakon mutuwa ashe mutuwar ce a ka yi , ta san yanzu Prince inta ya na cen cikin wani hali dan ya fa a mata yadda ya ke son Ammiensa , ta so ta na kusa da shi ta kwantar mishi da hankali a hankali ta kwanta ta aura kanta saman cinyar Aleenah ta lumshe idanunta wani an karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta kai hannu saman kanta ta fara shafawa a hankali MALIK zaune ya ke tsakiyar gadonsu , ya daura Pillow saman cinyoyinsa , hannayansa na saman pillown , ya zubawa waje guda ido , idanunsa sun yi jazir har sun kunbura da alamun ya sha kuka ko ya sha hawaye a hankali Prince ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama cen assan ma oshi ko motsi Malik bai yi ba , ko sallamarsa cikin zuciyarsa ya amsa mishi ita , ba ya jin ya na da karfin yin wani motsi a yanzu a hankali ya karaso bakin gadon ya tsaya ya na kallon Malik ya ce " Daddy ? " wata doguwar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya kauda kai gefe , ya kai hannu ya goge ruwan da su ka tarun mishi a ido sannan ya juyo ya kalli Prince ya saki wani cool murmushi ya ce " ya ? har kun gama honey moon in ? na zata sai na tafi cigiya da kaina " zama ya yi bakin gadon sannan ya ce " ba kai ne ka ba mu One week ka ai ba , da ma two weeks ka ce , ni gaskiya wannan Honey Moon in ba ta ishe ni ba " " hum, amma ai da farko ce wa ka yi ba ka so " hannu ya kai ya fara sosa bayan keyarsa ya na kauda kai murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya lumshe idanunsa ya na a haka ya ji Prince ya kwantar da kansa saman shoulder din shi a sanyaye ya ce " Daddy , I'm sorry , na san ka yi kewa ta sosai tsawan shekarun nan da ba na zama tare da kai " " na yi kewar ka sosai , amma hakan ya sa na ji irin kewar da Daddyna ya ji lokacin da na nan , da sauki ni na san halin da ka ke ciki , shi ko bai da ma tabbacin in ina raye , na sani ba laifinka ba ne , kuma ni ba na fushi da kai tun da ga shi yanzu ka dawo " " I love you my Daddy " ya fa a ya na zagayo da hannayansa a kugun Malik ya rungume shi ta gefe , ya lumshe idanunsa sai da ya saki wani dan karamin murmushi sannan ya juyo ya manna mishi kiss a forehead ya na fadin " I love you too , my baby " shiru Prince ya yi bai ce mishi komai ba , ajiyar zuciya kawai ya saukewa assa assa ya na a haka ya ji Malik ya zagayo da hannunshi a bayansa ya na fadin " Ba ka fada min ya Honey moon inku ta kasance ? " " So Sweet " ya fada a takaice da alamun ya manta da wa ya ke zaune dan zaro idanu Malik ya yi jin abun da ya ce ko kunyar sa bai ji ba , shi kuma ya ci gaba da tambayar shi ya na fadin " kenan yarinyar mutane ka ta a ? " " na ga ai Mallaka min ita a ka yi , har gaban Allah tawa ce " da ga haka ya ware idanunsa ya na kallon Malik , ya ci gaba da fadin " amma ka san wani abu Daddy ? ban taba jin irin wannan dadin ba , Allah Daddy sai da na dinga ganin wasu stars " Bushewa da dariya Malik ya yi har sai da idanunsa su ka ciko da ruwa bai da labari , amma Allah Prince ya cika dan Duniya , ko kunyar Malik bai ji ya fadi wannan abun , ai da farko da a ka ba shi auren ce wa ya yi ba ya so shi ya sa Malik ya bushe da dariya , yanzu ya fara jin dadin d'iyar mutane har da ganin wasu taurari sai da ya gama dariyarsa sannan ya ce mishi " ka na ji , idan ka kai makura ba stars kadai za ka gani ba , sai ka ga universe din ma baki daya , Allah ya sa dai ba ka takura mata " " to ba ita ta ce za ta iya ? dole ta yi hakuri tun da ta lasa min zuma " " hakan na nufin you love her ? " " Yes Daddy , ina son ta , fiye da yadda na ke jin ina son kaina , but I love you more than her " ya fada ya na kara matse Malik wata yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya rungume shi tsam shi ma , a haka har barci ya yi gaba da su AFTER SOME HOURS INAYA a hankali ta turo kofar dakin ta shigo ta na sallama a sanyaye ta na shigowa idanunta su ka sauka kan Malik da Prince kwance , Prince na kankame da Malik kamar wani ya ce zai kwace mishi shi har sai da ta saki wani cool murmushi ba ta da labari dan ta manta last time da ta gan su manne da juna haka a hankali ta ci gaba da takowa bakin gadon , ta sa hannu a hankali ta janye hannun Malik da ke saman bayan Prince sannan ta dan bubuga kumatun Prince , kassa kassa ta ce mishi " Prince , ba za ka je ka yi wanka ba ? " cikin magagin barci ya ce mata " please Baby , barci na ke ji " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta murde kunnesa ta na fadin " wake up , ba ita ba ce , Maza tashi min da ga saman gado " cikin wata siririyar murya ya ce mata " ashhh , Cutie da zafi fa " " sauko to " ta fada ta na sakin kunnensa a hankali ya tashi da ga jikin Malik ya sauko da kafafunsa kassa ya zauna bakin gadon ya na kallon ta ya na yamutse fuska hararrar shi ta yi kafin ta nuna mishi kofar fita da hannu bai ce mata komai ba ya juya ya manna wa Malik kiss a kumatu , sannan ya mike tsaye ita ma ya yi mata kiss a kumatu kafin ya sa kafa ya fice, ya baro part din baki daya sai da ya fita sannan ta saki wani dan karamin murmushi , ta tako a hankali ta kwanta in da ya tashi , ta rungume Malik kawai sai jin saukar hannunsa ta yi a bayanta , ya juyo su na fuskantar juna ya bude idanunsa a hankali , dama ba barcin ya ke ba , tunanin MALIKAT INAS ya hana shi barci a sanyaye ya ce mata " me ya sa za ki korar min babyna ? ba ki ga barci ya ke ba ? " cikin shagwaba ta ce mishi " ni kuma fa ? ni ma barci na ke ji " wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya matse ta tsam a jikinsa ya lumshe idanunsa ita ma lumshe idanunta kawai ta yi ta na sauke ajiyar zuciya IZZAT zaune ta ke gaban mirror din bedroom din ta , ta buga wani uban tagumi , tun safe ta ke kiran Queen ta ce fada mata MALIKAT INAS ta mutu amma har yanzu shiru har ta gaji da jira ta na wannan zaman jiran ta ga duk lamps din dakin sun mutu lokaci guda wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta na fadin " tun dazu na ke jiran ki , sai yanzu ki ka yi niyar zuwa ? " ta na gama fadar haka Queen ta fito cikin mirror kamar kullum saman chair din ta , inuwarta kawai a ke gani cike da isa ta ce " kiran me ki ke min ? MALIKAT INAS ce na sani da ta mutu " " to sai ki fada min abun da zan yi na gaba , tun da har step na farko ya cika " " idan ki koma wajen Izayn , zai fada miki
Chapter 49 · 0% Book details