Sashe 28
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MALIK a zaune su ke cikin parlourn MALIKAT INAS shi da Cutiensa , da RIANNA da MALIKAT INAS da Faaz kamar kullum Diya kuma yau ya koma Fada dan tun lokacin da ya konta ciwo Abdoul ne ke kula da komai yau to ya koma dan ya na son a gyara masarautar kafin dawowar su Prince su na zaune a haka wata mata ta shigo parlourn ta na sallama ta na sanye da wasu suit black color , ta medical glass a idanunta , ta na rike da wata bag a shekaru ba za ta wuce 30 years ba ko 35 haka RIANNA na ganin ta ta mike tsaye ta nufe ta ta na fadin " Prof barka da zuwa , bismillah shigo " ta kai karshen ta na mika mata hannu ba musu ita ma ta dago hannu su ka gaisa sannan RIANNA ta karaso da ita cikin parlourn cikin rudu ko wane ke kallon ta dan su ba su san ta ba kamar ko RIANNA ta san kallon me su ke sai ta ce musu " wannan ita ce prof din da na dauka za ta dinga yi wa Faaz class a nan gida kafin ya saba na kai shi school cikin sauran yara " sai a lokacin ko wane ya gane abun da ke faruwa Faaz kuma ya na jin abun da ta ce ya mike tsaye ya na fa din " no , ni ba na so , ba in da zan tafi " cikin sigar rarrashi Rianna ta ce mishi " kar ka damu ba in da za ka tafi , a nan cikin bedroom din ka za ta koya maka , okay ? " da sauri ya girgiza mata kai ya na shirin magana Rianna ta riga shi cewa " no , keep quiet ! in ba so ka ke ka bata min rai ba ka yi shiru ku tafi ta koya maka " kunbure fuska ya yi ya na turo dan karamin bakinsa ya fara takawa ya nufi corridor kallon prof din Rianna ta yi ta na fadin " bismillah mu je na kai ki bedroom din sa " gyada mata kai kawai prof din ta yi kafin ta fara takawa su ka shiga corridor sai da su ka shiga sannan Malik ya ce wa MALIKAT INAS " Ammie, wai yaron nan ba zai koma gidan marayu ba ? na ga RIANNA duk ta sangarta shi " a sanyaye MALIKAT INAS ta ce " to me ka ke so na ce ? ka san halin yar uwarka , ko na ce ta meda shi ba za ta yarda ba saboda ta na son shi " ta na gama rufe bakinta ko Rianna ta fito da ga cikin corridor ta na murmushi ta koma in da ta tasso ta zauna a hankali Malik ya juyo ya kalli Cutien sa ya ce " Junior ya kira ni ya ce wai Al-Sayid ya ce su zauna har lokacin da za a yi bikin auren prince " wata yar karamar dariya ta yi ta na kallon shi ita ta san halin yaronta duk lokacin da ya yi karya ta na iya gano shi sai da ta gama dariyarta sannan ta ce " wane Al-Sayid kuma ? kawai bai shirya dawowa ba ne , kawai ya yi anfani da damarsa ce ya koma in da ya fito " wani dan karamin tsaki Malik ya yi dan al'amarin Prince ya fi karfinsa " zai dawo ya same ni " ya fada a dakile ita dai Inaya dariya kawai ta ke yi bari na leko su Faaz kafin nan zaune ya ke bakin gadonsa ya nade hannayansa a kirji sai hura kumatu ya ke prof din na zaune geffensa rike da wani book ta na murmushi ta ce mishi " yawwa yanzu zan so na sani in ka taba zuwa school ko so guda ? " " No " ya fada a takaice " kenan ba ka san alphabet ba ? " ta tambaye shi murya cike da sanyi a hankali ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo ya na fadin " ke na yi miki kama da wanda bai san alphabet ba ? in har ki ka bude baki ki ka sake min magana sai na kashe ki a wajen nan sakara kawai " tsit prof ta yi ta na kallon ikon Allah ta na tambayar kanta ko dai aljanu ne su ka shige jikinsa sai da ta saita nitsuwar ta sannan ta ce " okay , yanzu fada min sunanka " tass ta ji saukar mari a face din ta , baki sake ta ke kallon shi ta dafe kunci, wai da gaske shi ne ya mare ta ko dai aljanu ne su ka mare ta ? dan ita ba ta ga lokacin da ya daga hannu ba a hankali ya mike tsaye ya nufi kofar fita dakin ya sa hannu ya tura ta ya saka mata security sannan ya juyo ya na kallon ta , wata yar karamar dariya ya yi kafin ya daga hannayansa dukka biyu sama kamar da wassa kawai na ga wasu kananan kwari sun fara fitowa da ga cikin tafin hannayansa wata razananiyar kara Prof ta saki ta ida Hayewa saman gadon ta na ja da baya , shi kuwa sai dariya ya ke kwarin nan na kara fitowa da ga cikin hannayansa duk su ka nufe ta su ka fara Hayewa saman gadon sai da ya ga kwarin sun kusa taba ta sannan ya damke hannayansa ya sauko su kassa , batt kwarin nan su ka bace kamar ba a taba yin su ba ita kuwa baiwar Allah sai kara ta ke saki kamar ta yi kuka a hankali ya tako bakin gadon ya na fadin " yi min shiru ko in kashe ki wajen nan ! " ai ko da sauri ta daura yatsa saman lips din ta ta na girgiza mishi kai kamar ta yi kuka , gaskiya ta razana wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Aunty , ki na ji ni ba na son wannan karatun , in kin fita ki cewa momy ke ba za iya koyar da ni ba , kin ji ko ? " ya fada cike da shagwaba gyada mishi kai kawai ta yi da sauri alamun Eh zama ya yi bakin gadon ya na fadin " shikenan tun da kin yarda za ki iya tafiya , in kuma ki fadawa wani abun da ya faru sai na kashe ki " da sauri ta sauko da ga saman gadon ta dauki bag din , ita littafin ma da ta fiddo ta manta da shi ta nufi kofar fita dakin da ya ke ta ga wajen da ya danna kofar ta rufe kawai ta sake dannawa kofar ta bude ta fice da sauri Kamar ta ga wani abun tsoro a nan parlourn kuma su na zaune su na hirar su cikin konciyar hankali su na a haka kawai su ka ga prof ta fito da sauri ta nufi kofar fita parlourn ko ta kan su ba ta bi ba , ga yanayin ta duk ya sauya cikin rudu RIANNA ta mike ta na fadin " Prof lafiya na ga kun fito ? har kun gama ? " ba tare da ta tsaya ba ta ce " ki yi hakuri ranki shi dade amma ba zan iya koyar da shi ba , ina da aikin yi , na gode " ta na gama fadar haka ta sa kafa ta fice cike da rudu RIANNA ta ke kallon Prof har sai da ta fita sannan ta nufi corridor ta shiga ta na kwallawa Faaz kira ko da ta shigo bedroom din sa ta gan shi zaune a kassa sai kuka ya ke ya dafe kumatunsa da hannu guda karasowa wajen sa RIANNA ta yi ta sa hannu ta mikar da shi tsaye ta na fadin " Faaz me ya faru ? wani abu ta yi maka ? " ya na kuka ya ke ce mata " momy ba ta da kirki, bugu na ta yi , ce wa ta yi na karanta mata alphabet na ce ban iya ba shi ne ta shiga bugu na , da na ce zan fadawa momyna ta sa a cire mata kai shi ne ta tashi ta tafi ta na ce min shege " ya kai karshen ya na kara sautin kukansa cikin sigar rarrashi RIANNA ta ce mishi " shikenan , i'm sorry , i'm sorry daina kukan nan please , bari zan sa a cire mata kai kamar yadda ka ce , ka na so ? " da sauri ya gyada mata kai ya na kai hannu ya fara goge hawayensa kiss ta yi mishi saman forehead kafin ta rungume shi ta na fadin " shikenan stop crying now " rungume ta shi ma ya yi ya na kukan karya da wani kyakyawan murmushi a face din sa TO FA , A NA DARA GA DARE YA YI , GA DUKKAN ALAMU FAAZ BA DA MANUFA MAI KYAU YA SHIGO DAULAR NAN BA , TUKUNNA MA WANENE SHI ? SU WA SU KA AIKO SHI ? ME YA KE SHIRIN AIKATAWA ? HMMMM NI DAI NA KOMA GEFE GASKIYA ) INAYA bayan RIANNA ta shiga corridor ta mike tsaye ta na fadin " Ammie bari na je na duba su " da sauri Malik ya riko hannunta ya na fadin " no , bar ta da babynta , mu tafi " ya kai karshen ya na mikewa tsaye da sauri ta ce mishi " amma baby ka bari na ga kar a je wani abu ta yi mishi " " to ina ruwanki Ah ? wuce mu tafi ko kuma na ja ki da karfi , kin kuma san in na ce na ja ki da karfi ba za ki ji dadi ba ko ? " hararrar shi ta yi ta na turo dan bakinta kafin su bar wajen ya na rike da hannunta ita dai MALIKAT INAS ta na zaune ta na kallon dramarsu sai da su ka fita sannan ta tashi ta shiga bedroom din ta bangaran su Malik kuwa ko da su ka fito a tunaninta building din su za su koma