← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 61

Sashe 30

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

so na tafi " slowly ya motsa lips din sa kamar an yi mishi dole ya ce " ni na saka ki ? " " No , amma rashin tausayina bai kai haka ba , kai ka ce min na kawo maka coffee kawai taimakon ka ne na yi " ta na gama fadar haka ta janye hannayanta da ga saman kansa ta nufi hanyar fita bin bayanta da kallo ya yi har sai da ta kai bakin kofar sannan ya ce " Na gode " wani dan karamin murmushi ta saki amma ba ta tsaya ba ta sa kafa ta fice sai da ta fita sannan ya meda idanunsa ya lumshe , ya san Sarai ba ita ya yi wa magana da farko ba saboda yanayin Muryarsu ba daya ba ce , shi kansa ya rasa ta ya ya ke gane su cikin sauki haka bayan su na kama tak kamar an tsaga kara , amma kallo daya ya ke musu ya gane su ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji a na yi mishi knocking sai da ya ja tsaki sannan ya ware idanunshi ya kalli saitin kofar wani dogari ne a tsaye ya na ganin ya juyo ya ce " ranka shi dade mai girma Al-Sayid ya na jiran ku a parlournsa ku yi breakfast " gyada mishi kai kawai Prince ya yi kafin ya mike tsaye ya nufi toilet ya shiga Jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya nufi dressing room dan jiya ya yi musu online shopping na kayan da za su saka kafin su koma Saudiya jim kadan ya fito sanye da kananan kaya wandon Jeans da T-shirt duk white color, da fararen sneakers a kafafunsa bedside drawer ya nufa ya dauki wayarsa ya saka cikin aljihunsa sannan ya nufi kofar fita ko neman Junior bai yi ba , ya na dunkule cikin bargo sai barci ya ke bayan ya baro part din su kai tsaye parlourn Al-Sayid ya nufa dan jiya wajen zagaye zagayen shi har ya iso parlourn ba shi da labari da sallama a bakinsa ya shigo parlourn , nan ya tardo duk Familyn Al-Sayid har da su Twins din sa , su na zaune tsakiyar parlourn a kassa saman carpet , ga abinci tsakiyar su da alamun yanzu za su breakfast Al-Sayid na ganin shi ya saki wani cool murmushi ya na fadin " sannu da zuwa Prince , bismillah zauna , yau tare za mu yi breakfast " cikin girmamawa Prince ya ce " ina godiya sosai da irin wannan karramawar , na san ba kowa ke samun Alfarmar cin abincin da familyn shugaban kassar nan mai Albarka , na gode amma ina sauri ne zan fita , idan har mai girma Al-Sayid ba shi da matsala da hakan " gyada mishi kai Al-Sayid ya yi a hankali ya na murmushi gaskiya ba karamin tafiya da zuciyarsa Prince ya yi ba , tun ba yau ba , tun lokacin da ya zo masarautar neman littafi yanayin da ya ke magana ya yi mugun burge shi godiya Prince ya mishi kafin ya juya ya yi tafiyarsa da sauri Sayida Ahlame ta tabo Aleesherh da ke zaune gefenta ta ce " ba za ki raka shi ba ? " tsuke fuska Aleesherh ta yi kafin ta ce " ni na kawo shi ne ? " " Aleesherh ba na son wannan yanayin maganar taki " Al-Sayid ya fada cikin tsare gida kauda kai gefe ta yi ta na turo dan bakinta ba tare da ta ce komai ba " Aleenah , ina son ki taimakawa yar uwarki ta shirya mishi diner yau " fadin Al-Sayid da to kawai ta amsa mishi kanta na sunkuye ta na shan fruits Aleesherh kuwa sai shan tsami ta ke , kai ka ce ba saboda shi ne ta yi kuka kawai dan ya ki yi mata magana ta na a haka ta jiyo Muryar Sayida Ahlame ta na fadin " ranka shi dade , gaskiya yaron nan ya na da nitsuwa dubi yadda ya ke magana cike da girmamawa , na so ya na da dan uwana da na ba shi Aleenah " ta fada ta na kallon Aleenah har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana Sayida Fadwah ta riga shi cewa " me ya sa ba za a ba shi Aleenah ba ma a kan Aleesherh " a tare Aleesherh da Aleenah su ka dago kai su ka kalle ta " na ga Aleesherh ita ce babba , ta ya za a ba shi auren Aleenah al'halin ita ba ta da auren , amma tun da shi kansa bai san wadda na ba shi ba kuma Aleesherh ta ce ba ta son auren , in har Aleenah ta amince sai a yi auren da ita " fadin Al-Sayid ya na kallon Aleenah alamun tambaya dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ta na kallon Aleenah har zaro idanu ta ke haka ita ma kallon Aleesherh ta ke zuciyarta na duka uku uku kar a je Al-Sayid ya dawo da auren kan ta , ta san Aleesherh ba za ta taba yahe mata hakan ba saboda son da ta ke wa Prince a fusace Aleesherh ta mike ta nufi kofar fita da sauri ta fice sai kiran sunanta Al-Sayid da Sayida Ahlame su ke amma ina ba ta jin su sai da ta fita sannan Al-Sayid ya kalli Aleenah ya ce " Aleenah ba ki ba ni amsa ba ? tun da ita ba ta so sai na aura miki shi ? ko ya ki ka gani ? " da sauri Sayida Fadwah ta ce " ba sai ka tambaye ta ba ta amince , na ga kai ne da iko da su ba akasin haka ba " ta fada dan burinta guda a janye maganar auren Aleesherh da Prince , ko wani za ta aura ta fi son ta auri Abdoul-Jalil wanda ke matsayin nephew din ta da sauri Aleenah ta ce " no , Daddy wlh ba na so , ba na so " ta fada kamar za ta yi kuka wata yar karamar dariya Al-Sayid ya yi kafin ya ce " kontar da hankalinki , ni dama wassa na ke miki , na riga da na ba shi Aleesherh ba zan sauya ba ko da ba ta son shi sai an yi auren " wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da ta lumshe idanunta kafin ta mike tsaye ta na fadin " Daddy na koshi " " shikenan " Al-Sayid ya fada a takaice , da ga haka ta sa kafa ta bar wajen ta bi bayan Aleesherh sai da ta fita sannan Al-Sayid ya ce wa Sayida Ahlame " Za ki iya tafiya ke ma ! " ba musu ta tashi ta yi musu sallama sannan ta tafi ya rage da ga shi sai Sayida Fadwah cikin nitsuwa ya ce mata " Fadwah , ban san me ki ke nufi da maganarki ba , amma zan so ki sani Auren Aleesherh da prince ba abun da zai hana shi , na sani Abdoul-Jalil kamar d'a ya ke a gare ki kuma na ji dadi da har ki ka nema mishi auren Aleesherh , to Allah ya yi Aleesherh matar Prince ce , da kin yi min wannan maganar tun da farko da sai na ba shi ita , amma na riga da na bawa Prince , amma in har ya na son Aleenah ni ba ni da matsala zan ba shi auren ta " " zan iya tafiya ? " ta fada cikin sanyin murya gyada mata kai kawai ya yi dan ya san halinta in ba ta son abu to shikenan ba za ta so shi ba har abada a hankali ta tashi ta fice parlourn ta bar shi nan zaune ALEENAH bayan ta baro parlourn Al-Sayid kai tsaye part din su ta koma ta na shiga ta ga Aleesherh konce tsakiyar gadon ta yi rub da ciki karasowa ta yi ta zauna bakin gadon ta na fadin " Alee , in har da gaske ki na son shi ya kamata ki fito ki fada masa wannan shan tsami da ki ke mishi ba shi ne solution ba , yanzu ba dan Daddy wassa ya ke mana ba da yanzu ya fasa aura miki shi " shiru Aleesherh ta yi ba ta ce mata komai ba ganin ba ta amsa mata ba kawai sai ta daga kafadunta ta tashi ta koma saman sofa ta zauna ta na kallon ta MISALIN KARFE 8 NA DARE PRINCE zaune ya ke cikin part din su ya na sanye da wasu pajama white color , da laptop saman cinyoyinshi ya na aiki Junior na konce gefensa ya na rike da wayarsa ya na latsawa su na a haka wani dogari ya iso wajen ya na yi musu knocking a hankali Junior ya sauko da ga saman gadon ya nufi kofar ya na rike da wayarsa ya na isowa ya bude kofar cikin girmamawa dogarin ya ce mishi " ina mika sakon gaisuwata ga shugaban , Gimbiya Aleesherh ta aiko da sako zuwa ga Prince " ya fada ya na mika mishi wata paper da duka hannayansa biyu hannu Junior ya kai ya karba ya na yi mishi godiya kafin ya juya ya dawo dakin ya na bude paper din ya fara karanto abun da ke ciki sai da ya gama sannan ya saki wani dan karamin murmushi ya na fadin " Prince , babynka ta shirya maka diner a garden " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wane baby ? ni babu in da zan je kuma sanyi na ji " da sauri Junior ya nufi dressing room ya shiga jim kadan ya fito rike da wata jacket white color ya karaso wajen Prince ya mika mishi ya na fadin " ko wane problem ya na da solution , dan haka malam tashi ka tafi wajen madam ta shirya maka abinci " marairaice mishi fuska Prince ya yi ya na fadin " please kyale ni , wlh sanyi na ke ji , kuma ka san cikin sauki zazzabi ke kama ni in ina jin sanyi " " wlh ko ka tashi ka tafi ko
Chapter 30 · 0% Book details