Sashe 44
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da tsoro da alamun wani abu aljanunsu su ka jiyo , in ba ku manta ba Prince shi ma ya gado aljanunta , may be shi ya sa Malik bai ji abun da su ke ji ba kafin ma Malik ya iso bakin ruwan wasu ruwa su ka sauko da ga saman dutsen da muguwar karfi , lokaci guda su ka tafi da shi wata razananiyar kara Inaya ta saki , Prince kuma ya na fadin " Daddy ! " da mugun karfi duk yadda Malik ya so fita da ga cikin ruwan ya kassa sai tafiya da shi ruwan su ke yi ga shi ko wajen duk duwatsu ne sai buguwa ya ke ciki da sauri Prince ya fara gudu bakin ruwan ya bi Malik , ya na a haka kawai ya ga Malik ya bugu da wani dutsen , nan take kansa ya fara zubar da jini , jikinsa ya yi sanyi ya sume " Daddy ! " Prince ya fada da mugun karfi ganin abun da ya faru da Daddynsa hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya hango wata waterfall , yadda ya san kassar saudiya , ya San akwai wani teku bayan masarautar kuma tabbas ruwan nan cikin tekun za su Zube , in har Malik ya fada cikin tekun nan to tabbas mutuwa zai yi kamar kiftawar ido na ga idanunsa sun koma farare kal , gashin kansa shi ma ya koma fari kal , pin din da ya daure shi ta fadi nan take ya fara tashi cikin iska Inaya na ganin gashin kansa ya koma Fari ta tsaya da ga gudun da ta ke ta na sauke ajiyar zuciya lokaci guda na ga Prince ya tsunduma cikin ruwan nan , amma sam ba na iya ganinsa cikin ruwan kamar ya bace haka dai na tsaye ina bin ruwan da kallo ina jiran fitowarsa ina a haka kawai na ga ya fito da ga cikin ruwan dauke da Malik , ya yi sama da shi cikin iska ya na kallon Dutsen da ruwan su ka zubo , nan ya ga wani bakin abu kamar inuwar mutum tsaye su na kallon juna kafin ta bace bat sai da ya bace sannan ya sauko kassa bakin ruwan , ya kontar da Malik , dai'dai lokacin da Inaya ta karaso wajen su ta na bin Prince da kallo a hankali na ga kwayar idonsa ta fara fitowa , har idanunsa su ka dawo dai'dai gashin kansa amma har yanzu white ne da sauri ta daura hannayanta biyu saman cikin Malik ta fara dannawa da karfi , duk lokacin da ta danna sai ruwa sun fito da ga cikin bakinsa , a haka har su ka daina fitowa amma Malik ko motsi ba ya yi da sauri Prince ya mike ya dauki Malik ya saba saman shoulder ya nufi hanyar komawa cikin building din , Inaya na biye da bayansa bayan sun koma bedroom din , kai tsaye saman gado ya kontar da Malik ya bude bedside drawer ya fiddo A box , cikin nitsuwa ya yi wa Malik dress a wajen da ya ji ciwo sai da ya yi mishi dress sannan ya kontar da kansa saman kirjinsa ya na sauraron bugun zuciyarsa ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dago ya kalli Inaya da ke tsaye bayansa ta ce " momy kar ki damu , suma ce kawai ya yi " wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna bakin gadon , ta riko hannun Malik ta manna mishi kiss a hankali Prince ya mike ya nufi kofar fita da sauri Inaya ta ce mishi " Prince , ta ya za ka fita a haka , ka tsaya na kawo maka ko jallabiya ce ka saka " gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juyo , ita kuma ta mike ta shiga dressing room jim kadan ta fito rike da Jallabiyar Malik brown color ta na mika mishi a hankali ya fara takowa ya karbi jallabiyar ya saka , ya na sakawa Idanunsa su ka sauka saman dressing mirror , nan ya ga gashin kansa har yanzu white color ne zaro idanu ya yi da karfi ya na kallon kansa , a rude ya kai hannu ya fara shafa gashin kansa ya na janyo sa gaban face din sa kamar wani zarrare ya ke fadin " momy , my hair , what happened ? ya a ka yi ya koma white haka ? " cikin sanyin murya ta ce " Prince , calm down ba abun da ya faru " " kamar ya na kontar da hankalina ? momy gashina ya koma white ki na ce min na kontar da hankalina , i'm sick ? ko dai ruwan nan ne ? tsaya ya ma a ka yi Daddy ya fito da ga cikin ruwan ? ni ban ga lokacin da ya fito ba ? " wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta a hankali , ta ware su , sun koma farare kal dama kayan jikinta white color ne , ta bude baki a hankali ta ce " Abyad , fito ina son magana da ke " ta na rufe bakinta ko Idanun Prince su ma su ka koma white color , nashi na komawa white nata kuma su ka sauya su ka dawo dai'dai cikin nitsuwa ta ce " Abyad , me ya sa har yanzu gashinsa ya tsaya fari ? " wannan karan ba Muryar Prince na jiyo ba , muryar Abyad na jiyo ta na fadin " momy , ni ma ban sani ba , momy sai kun yi hankali , na ga wani abu da ya tayar min da hankali " " ni ma ina ji a jikina kamar a na bibiyar mu " ta fada ta na takowa a hankali ta zauna bakin gadon a hankali shi ma ya tako ya zauna , sannan ya ce " momy ba bibiyar ku a ke yi ba , abun da ke son cutar da ku ya na tare da ku , ina ga saboda tsoron da na ji ne gashinsa bai dawo dai'dai ba , momy wlh ba karamin abu ba ne na gani " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta riko hannunsa ta ce " kar ki damu ba abun da zai faru in sha Allah " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya a hankali , kafin ya ware su a hankali , idanunsa sun dawo dai'dai amma har yanzu gashinsa har yanzu white ne tun kafin ya ce wani abu Inaya ta ce mishi " kar ka damu , gashinka zai dawo dai'dai " " when momy ? ta ya ya zama white haka lokaci guda , ni dai na san ba na shafa color " " may be da ga ruwan ne " " ruwa kuma ? " ya fada a dan rude gyada mishi kai ta yi kawai sannan ta ce " tashi ka tafi ka yi wanka , may be in ka zuba mishi hot water zai dawo dai'dai " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya mike ya fice bedroom din , ya rasa abun da ke faruwa , ya San dai shi ba yadda za a yi ruwa su sauya color din gashin mutum lokaci guda haka , sai dai in wani abu ne a cikin su , ya kuma a ka yi Malik ya fito da ga cikin ruwan , shi dai ya san ba shi ya fiddo shi ba , ba kuma Inaya ce ba , ya a ka yi to ya fito ? da wadanan tambayoyin a kansa har ya baro part din bangaran Inaya kuma , ya na fita ko ta ida Hayewa saman gadon ta zauna gefen Malik , ta daura hannun saman kansa cikin sanyin murya ta ce " ban san abun ke shirin faruwa da mu ba , amma na san Allah ba zai bari wani abu ya samu ahalina ba , da a ce yanzu Abyad ba ta fito a jikin Prince ba ta ceco ta ka da ban san ya zan yi da rayuwata ba , na san in har ka fada tekun nan ba za mu taba samo ka a raye ba , ya Allah , ko ma minene ke shirin faruwa ka yi mana tsari da shi , ko wasu makiyan gare mu bayan idon mu ya Allah kar ka ba su damar cutar da mu " ta kai karshen ta na sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , a lokacin ko jiyo Muryar Malik ya na kiran sunanta a hankali wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " ga ni nan Baby , ba abun da ya faru da kai " slowly ya ware idanunsa , ya na kai hannu ya dafe kansa dan ba karamin zafi ya ke mishi ba , a sanyaye ya ce " my Cutie , me ya faru ? kaina mugun zafi ya ke min " " ba komai Baby , kawai ka bugu ne cikin dutse , amma ba abun da ya faru " ajiyar zuciya ta sauke kafin ya yi kokarin mikewa zaune a hankali ya jingina bayansa a forehead din gadon ya na kallon ta sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Cutie , fada min gaskiya , na ga sarai lokacin da ruwa su ka tafi da ni , na ga kuma lokacin da gashin Prince ya fara komawa White kafin na suma " shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba dan gaskiya ba ta da amsar da za ta ba shi , ita kanta ba ta san abun da ke faruwa ba ta na a haka ta ji ya rungume ta a jikinsa , nan take kuka ya kubce mata ta juya da sauri ta boye face din ta a kirjinsa ta na fadin " da yanzu wani abu ya same ka ban san ya zan yi da rayuwata , ba zan iya rayuwa babu kai ba " wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " ki kontar da hankalinki , ba abun da ya faru da ni , kuma in sha Allah ba abun da zai raba mu