← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 61

Sashe 50

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abun da za ki yi " ta na gama fadar haka ta bace da ga cikin mirror din , lamps din dakin duk su ka kunnu............ *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , 500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP IN* *HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE 200* THE BIGINING https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i _______________________________________________ [ FREE PAGE ___ 24 wani dan karamin tsaki Izzat ta ja kafin ta mike tsaye ta na fadin " gaskiya na gaji da wannan aikin , ga shi sun bar ni cikin duhu , sun ki fada min abun da su ke son aikatawa " ta kai karshen ta na Hayewa saman bed din ta ta yi rub da ciki ba ke kadai ba har da ni , har yanzu na kassa tantance me su ke hari , micece manufarsu dan tabbas akwai abun da su ke hari cikin masarautar , ko daukar fansa ko kuma ganin bayan ahalin Malik AFTER SOME HOURS ALEESHERH Duk yinin ranar a part din MALIKAT INAS ta share shi , sai wajen karfe 8 sannan ta tashi ta koma part din su da sallama a bakinta ta shigo parlourn part din su , ya na gyare sai qamshi ke tashi wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ci gaba da takawa ta nufi corridor ta shiga bedroom din ta sam ba ta kawo a ranta ta duba bedroom din shi in ya na ciki ko ba ya ciki ko da ta wuce bedroom din ta toilet ta shiga ta yi lafiyayen wanka sannan ta fito ta shafa shafa lotion din ta dan perfume ta wuce dressing room jim kadan ta fito sanye da wata Abaya white color ko veil babu a kanta , ta saki kyakyawan gashinta a baya sai tashin qamshi ta ke yi fitowa ta yi da ga cikin bedroom din ta na taku a sanyaye har ta juya za ta baro corridor din ta ga kofar bedroom din sa a bude kadan haske na fitowa da alamun akwai mutum ciki wani dan murmushi ta yi kafin ta nufi bedroom din sa , ta tura kofar a hankali ta shigo ta na sallama nan ta gan shi zaune tsakiyar gadonsa , da ga shi sai short da singlet , da laptop saman kafafunsa ya na aiki a hankali ta tako ta tsaya bakin gadon ta na fadin " Baby ? " " Yes , me ya faru ? " ya fada ba tare da ya kalle ta ba zama ta yi bakin gadon sannan ta kai hannu a hankali ta rufe laptop din sa bai ce mata komai ba ya dago kai a hankali ya kalle ta ya na daga mata gera a sanyaye ta ce mishi " i'm sorry , Aleenah ta fada min abun da ya faru " gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juya ya bude laptop din sa ya ci gaba da aikinsa sake rufe laptop din sa ta yi ta na fadin " Baby , ba ka bukatar wani abu na kawo maka ? " sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya kalle ta ya ce " No , just ina son na kammala aikin da na ke yanzu " " and me ? " ta fada ta na marairaice mishi face " you , what ? me ki ke so ? , ki bari na kammala aikina ko ? " ba musu ta janye hannunta da ga saman laptop din sa ta juya mishi baya ta fara latsa wayar hannunta har ya bude laptop din sa zai ci gaba da aikinsa kawai ya ji zuciyarsa ta yi wata muguwar bugawa wadda bai taba jin irin ta ba da sauri ya saki laptop din sa ya diro da ga saman gadon ya nufi dressing mirror har ya tuntunbe ba karamar razana ta yi ba ganin yanayin da ya sauko da saman gadon ta mike ta bi bayansa ta na fadin " Baby , me ya faru ? " ko sauraron ta bai yi ba ya nufi dressing mirror ya tsaya ya sa hannayansa ya fidda singlet din sa , ya na kallon kirjinsa sai ya ga sunan da ta rubuta mishi a kirji ya na rufewa da kansa , kirjinsa ya dawo kamar ba ta yi mishi rubutu ba , hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya ga gashin kansa ya koma white duk hankalinsa ya bi ya tashi sai wani nunfashi ya ke ja sama sama ya na zaro idanu ita dai Aleesherh ta na tsaye gefensa ta na kallon shi ba ta ma san abun da za ta ce ba , tun da ta ke ba ta taba ganin irin wannan abun ba , ba laifi in a ka ce mata sunan da ta rubuta mishi ya goge amma wannan abun it's not normal , a ce lokaci guda haka ya rufe kamar bai taba samun rauni a wajen ba slowly ya juyo ya kalle ta ya ce " me ya faru ? " " ni ma ban sani ba " ta fada a dan razane wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya daura hannu saman kansa ya fara shafa gashinsa , shi bai ma san irin tunanin da zai yi ba , ga shi ko bai da wanda zai ba shi amsa ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji ta rungume shi ta kontar da kanta a bayansa ta na fadin " ka kontar da hankalinka baby " " ta ya za ki ce na kontar da hankalina , ki na ganin abun da ya faru , my hair is White , ko ba ki gani na ? " " na gani " " ina son magana da Cutie " ya fada ya na shirin rabawa ta gefenta ya wuce da sauri ta rungume shi ta na sakin kuka ta ce " please kar ka tafi , ka tsaya , so ka ke hankalina ya gama tashi ? " wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya rungume ta shi ma ya na dan bubuga bayanta cikin sigar rarrashi sannan ya ce " please stop crying , babu in da zan je " wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara rage sautin kukanta , ta fara shigewa jikinsa ta na shafa bayansa a hankali , ta na goge face din ta a kirjinsa wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sa hannayansa ya dauke ta cancak ya nufi gadonsa kai tsaye ya kwantar da ita sama , sannan ya bi ta ya yi mata runfa da kirjinsa wani dan karamin murmushi ta saki ta na daga mishi gera guda bai ce mata komai ba ya kai hannu ya riko zib din Abayarta ya zuge shi har kassa , sannan ya dago hannu ya kashe lamps din dakin baki daya Okay , kora ta a ka yi ko ? No problem na tafi ni ma , amma ka ji wa yarinyar mutane ciwo kar ka neme ni ) PRINCESS zaune ta ke cikin garden , duk da cikin dare ne ba ta jin tsoron zama nan ita kadai , ta yi kuka har ta gaji ta na zaune ta zubawa waje guda ido , Allah kadai ya san abun da ta ke tunani ta na zaune a haka Junior ya iso wajen ya na yi mata sallama , ya na sanye da kayan barcinsa , Wajen Prince ne ya so tafiya amma ya na ganin ta ya ji zuciyarsa na bukatar kasance wa da ita sai da ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan ta dago kai ta kalle shi ta na murmushi ta ce " Hi Junior , ba ka yi barci ba ? " " ta ya zan yi barci rabin raina bai yi barci ba " ya fada ya na karasowa gefenta ya zauna wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " na ji shikenan " " me ya sa ba ki yi barci ba ? ki na tunanin Ammie ko ? " gyada mishi kai ta yi a hankali ta ce " har yanzu ba kassa yarda ta tafi kenan , you know how much i love her , yanzu wa zan dinga tsokana ? " " ba ga ni ba " ya fada ya na riko hannunta wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kontar da kanta saman shoulder din sa ta ce " a yanzu , na san duk lokacin da ka yi aure za mu daina ganin juna , za mu daina tafiya shan ice cream da shopping , sai dai ka tafi da matarka " " wa ya fada miki ? ko auren na yi tare za mu dinga tafiya shan ice cream , mu na tafiya Shopping da sauran wajaje " " hmmm , kai ka na ganin matarka za ta yarda , duk da ni kanwarka ce , amma in dai ta na son ka ba za ta ji dadin ganin ka da wata ba " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya zuba mata ido , har yanzu ya kassa tantance me ya sa ya ke son ta haka ba , duk da sun tasso a matsayin brother and sister , amma duk lokacin da ya ke tare da ita ya na jin wani feeling da bai taba ji tare da wata macen ba , that's why ya yarda da cewa tabbas son ta ne ya ke , amma ya ga alamun ita sam ba ta lura da hakan sai da ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya sannan ya kira sunanta a Sanyaye " uhm " ta amsa mishi ba tare da ta dago kanta ba da ga saman shoulder din sa ya dan dauki lokaci kafin ya bude baki cike da shakku ya ce mata " Princess , za ki aure ni ? " Dam ta ji zuciyarta ta buga ta dago kai ta na kallon shi ta ce " What ? ka san me ka ce ? " gyada mata kai ya yi kafin ya ce " na sani , please ki fada min za ki aure ? " " aure fa ka ce Junior ? anya kanka guda kuwa ? , ko dai wassa
Chapter 50 · 0% Book details