← Book details Nayel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 61

Sashe 55

Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amsa mishi sannan su ka yi mishi sallama kowane ya tafi part din sa sai da Malik ya kwantar wa Diya hankali ya tabbatar mishi ba abun da ya faru da su , sannan ya raka shi har part din sa su na tattaunawa a kan abun da ya shafi masarautar , akwai wata shawara ta musaman da su ka yanke amma ba za su fadawa kowa ita ba sai an yi arba-in na rasuwar MALIKAT INAS ( ko ma minene mu na jira mu ji bayan ya raka shi kai tsaye part din su ya koma , ya wuce bedroom din sa ya na shiga ko ya tardo Inaya zaune bakin gadon ta zubawa kofar shigowar ido da alamun tunanin wani abu ya ke a hankali ya juya ya rufe kofar ya saka mata security , sannan ya tako a hankali ya zauna gefenta sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ina tunanin mutum guda ne ya yi wannan aikin , wanda ya ke son ganin bayan Prince shi ne ya yi sanadiyar Ammie " wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " ni ban ma san abun da zan ce a kai ba , duk yadda a ka yi wanda ke mana wannan aikin ya na a tare da mu , in ba haka ba ta ya ya san Prince ya tafi UK , har ma ya na shirin dawowa " " haka ne , yanzu me ki ke so mu yi ? " a hankali ta juyo ta kalle shi , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " me fa za mu yi ? mu zuba ido mu ga abun da su ke shirin yi mana " wata yar karamar dariya ya yi kafin ya janyo ta jikinsa , sannan ya kwanta ya yi mata runfa da kirjinsa ya na kallon cikin idanunta ya ce " so ki ke na zauna su cutar min da ku ? " " ba abun da za su iya yi , ka manta su wa ke tare da familynka " ta na gama fadar haka na ga idanunta sun sauya kamar juyawar page su ka koma White , sannan su ka dawo dai'dai lokaci guda murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " tun da haka ne abun , yanzu ya za a yi da ni ? yunwa na ke ji My Cutie " hararrar wassa ta yi mishi ta na fadin " tsakani da Allah baby ba yanzu mu ka yi diner ba ? kuma ka ce yunwa ka ke ji ? " " Noooo ! ni fa ba irin wannan yunwar na ke ji ba , tun jiya fa ba ki kula da ni ba , ba dole na ji yunwa ba , yanzu dai ki san yadda za ki yi a kai " bushewa da dariya ta yi kafin ta zagayo da hannayanta a wuyansa kafin ma ta ce wani abu ya toshe mata baki da nasa bakin ya fara yi mata kiss Ni kuma na dauki takarduna na fice , wannan game din ba irin namu ba ne ALEESHERH bayan sun shiga bedroom din Princess , ta zaunar da ita bakin gadonta ta na fadin " zauna, bari na je na hada miki ruwa ki yi wanka " da to kawai Aleesherh ta amsa mata , da ga haka ta juya ta shiga toilet ta na shiga Aleesherh ta dago wayarta , ta shiga kiran layin da Prince ya kira ta da shi dan yanzu Muryarsa kawai ta ke da bukatar ji ko ringing biyu kiran bai yi ba ko ya daga ya na sallama kassa kassa kamar an yi mishi dole wani dan karamin murmushi ta saki ta na sauke ajiyar zuciya a tare kafin ta amsa mishi sallamarsa cikin nitsuwa ya ce mata " har kin kammala diner ? " " Eh baby " ta fada a sanyaye " shikenan , yanzu tashi ki yi wanka sai ki kwanta ki huta " " ba zan iya ba , ni so na ke kawai ka dawo , da yanzu wani abu ya same ka na san ba zan iya jurewa ba " " na sani , that's why ma na kassa shiga jirgin ina na kokarin kiran ki na fada miki za ni dawo , da ba dan ke ba da na san yanzu wata maganar a ke daban , na gode da ki ke cece ni " wata yar karamar dariya ta yi , kafin ta shagwabe fuska kamar ta na gabansa ta ce " na ji shikenan , amma da ga gobe in ka dawo ba zan sake barin ka ka tafi kai kadai ba , kullum tare za mu tafi ko ina ne ma " " okay , I love you my Beautie " " I love you too my Baby " " okay now tafi ki yi barci , sai da safe " , ya na gama fadar haka bai jira amsarta ba ya katse kiran sauko wayar ta yi a hankali ta ajiye saman bedside drawer ta na ajiye ta ko Princess ta ce mata " shikenan ? har kun ida hirar ? ba irin wannan jan ajin ? ki dan ja shi da hira , ki na zuba mishi shagwaba , ki na kiransa da wadanan kananan sunayan like my Angel , My Chocolate , Sweet , Candy , Honey ya ji ba ya son kashe kiran ma ba ki daya kamar ya janyo ki ta cikin wayar ya rungume " wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta ce " yanzu wannan da na yi bai isa ba ? " " hmmmm , shiga ki yi wanka ki zo na gwada miki yadda a ke yi Mrs Prince " ta fada ta na karasowa bakin gadon ta zauna ba musu ta tashi ta shiga toilet ta yi wanka ta yi wajen 45 minutes kafin ta fito sanye da bathrobe , a lokacin har Princess ta fiddo mata kayan barcinta ta saka karbar kayan Aleesherh ta yi ta shiga dressing room din ta , ta saka kayan sannan ta fito , nan ta isko Princess zaune tsakiyar gadon ta na rike da wayarta ta na latsawa karasowa ta yi bakin gadon ta zauna ta na fadin " me ki ke yi da wayata ? " murmushi mai dan sauti Princess ta yi kafin ta ce " zuba ido ki ga yadda a ke yi " ba ta ce komai ba ta yi shiru ta zuba mata ido ta na murmushi ta na a haka ta jiyo wayarta ta fara ringing da alamun kira ne ta ke sai dai kiran ya katse ta sake yin wani , wannan karan bai yi ringing biyu ba Prince ya daga ya na sallama amsa mishi sallamar Princess ta yi kafin ta ce " Prince , ka na lafiya ? ba abun da ya same ka ? tun dazu na ke kiran ka sai yanzu za ka dauka ? hankalina har ya fara tashi " cikin nitsuwa ya ce mata " don't worry , na shiga wanka ne , ba abun da ya faru da ni " " and Junior ? please ba shi wayar ina son na yi mishi magana " ta fada ta na marairaice murya da okay kawai ya amsa mata , kafin na ji wajen shiru kamar ya na taku a haka na jiyo Muryar Junior ya na fadin " Hello ! My Princess " wani cool murmushi ta saki ta na fadin " Junior , ba abun da ya same ka ? " " Hmmmm , ki daina kirana da Junior yanzu " " na ji shikenan My Heartbeat , yanzu fada min , ya jikinka ? ba ka ji ciwo ba ? please ka yi sauri ka dawo " ta fada cikin yar shagwaba " uhm , har kin fara kewa ta kenan ? " " ba dole na yi kewa ba , rabin raina ya tafi ya bar ni , tun safe ba abun da na yi kawai ina kwance ina tunanin ka , kuma ka ce ba zan yi kewa ba , yanzu ni dai ka yi saurin dawowa gobe " wata yar dariya ya yi sannan ya ce mata " ni fa ba gobe zan dawo ba , Prince ne kadai zai dawo gobe , ni sai Thursday " " what ? sai jibi ? no gaskiya ban yarda ba , so ka ke a kwantar da ni jinya ? ko yanzu zazzabi na ke sai da Daddy ya ban magani na sha " ta fada cike da shagwaba har da turo dan karamin bakinta dama gwana ce " shikenan , yanzu idan na dawo me za ki shirya min ? " " ka fara dawowa , ba zan rasa abun da zan shirya maka ba , ko da kuwa kaina ne " " Really ? " ya fada cike da zumudi wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sai da safe ni barci na ke ji " da sauri ya ce mata " no , kar ki kashe , please ki fada min mana , kin san yadda ki ka tayar min da hankali ? , yanzu kin sa dole gobe sai na dawo " " idan ka na son ganin ko minene zan shirya maka , to gobe ka dawo , ina tabbatar maka sai ka mutu ba ka ji irin wannan dadin ba " ta na gama fadar haka ta katse kiran , ta mikawa Aleesherh wayarta kafin ma ta kai hannu ta karba ta ji wani kiran ya shigo cikin nitsuwa Princess ta ce mata " kar ki dauka , duk kiran da za a yi " " why ? " Aleesherh ta tambaye ta ta na meda wayarta saman bedside drawer ja da baya Princess ta yi ta jingina bayanta da forehead din gadon ta ce mata " just dan na yi excited din shi " ta fada ta na daga kafadunta alamun ba ta damu ba sannu da kokari , ai kam aikinki ya cika , kin samu abun da ki ke so ) *WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN
Chapter 55 · 0% Book details