Sashe 2
Nayel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
THE BIGINING ( IN DAI KIN SAN BA KI KARANTA EXILED PRINCE BA , BOOKS 1 , 2 , 3 & 4 , TO KAR MA YI KI YI KOKARIN KARANTAWA DAN BA ZA NI GANE KOMAI BA WANNAN KARAN NA ZO MUKU DA SABON SALON SOYAYYA KAMAR KULLUM BA ZAN CIKA KU DA SURUTU BA , SAI MUN SHIGA CIKIN LABARIN ZA KU GANE , WANNAN KARAN ZAI TASHI KWAKWOLWAR KU KAMAR BOMB TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANEL https://whatsapp.com/channel/0029Vaudu1uGpLHRdHh76P0s _______________________________________________ PAGE___1 FOUR YEARS BEFORE DAULAR SAUDIYA har ya kai bakin kofar mama ta ce mishi " tsaya don Allah ina son na yi magana da kai , auta yanzu na dawo " ta kai karshen ta na sakin Inaya ta mike ta bi bayan Malik su ka fita ita kuma Inaya ta koma ta konta sai da su ka yi dan nisa da dakin sannan su ka tsaya mama ta ce mishi " na sani Triplets ne ta haifa , ban ga laifin ka ba dan ka boye mata dan kar ta cutu , amma ina jin wani abu wanda ba zan iya fada maka ba " cikin rudu ya ce mata " ta ya a ka yi ku ka san uku ne bayan ni da doctor da nurse biyu ne kawai mu ka san triplets ta haifa , ko ita na yi mamakin yadda a ka yi ta san Triplets ne " " Muryar shi ta jiyo , haka ni ma na jiyo Muryar shi ta haka ne na gane su uku ne ta haifa , but zan so ka koma wajen doctor ka tambaye ta ina babyn ka ya ke in ba ta gan shi ba za ta iya samun sukuni ba , haka za ta yi ta jin Muryar shi " wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " ki yi hakuri mama , ba zan iya ba , na san in ta ji labarin shi ba za ta iya jurewa ba , shi ya sa na boye wannan maganar , ke ma ina rokon ki don Allah kar ki fada mata " " amma ya ka ke so ta yi Muryar shi da ta ke ji ? " " zan san yadda zan yi " ya na gama fadar haka bai jira amsar ta ba ya raba ta geffen ta ya wuce a hankali ta juya ta bi shi da kallo na dan lokaci kafin ta juya ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya sannan ta koma dakin Inaya ko da ta koma ce mata ta yi " auta jira ni yanzu na dawo " ita dai Inaya da to kawai ta ke amsa mata haka mama ta sa kafa ta fito bedroom din , kai tsaye office din doctor din da ta karbi haihuwar Inaya ta nufa kamar ko ta san hanya da sallama a bakinta ta shigo , ta na gaishe da doctor da fara'a doctor ta amsa mata cikin girmamawa dan ba wanda bai San mama ba cikin masarautar nan " Doctor , babyn da Malik ya ce ku bizine shi na ke son adawowa yarinyata da kayanta " nan take murmushin da ke saman face din doctor ya bace ta ce " ki yi hakuri ranki shi dade , amma mun riga mun bizine shi , akwai nurse din da su ka fita da shi ta hanyar sirri , na san yanzu haka su na kan hanyar dawowa " " innallillahi wa'ina illaihi raji'un , a ina su ka bizine shi ? " mama ta fada dan karfi " a makabartar da ke fitar masarautar , Malik ya ce kar wanda ya san da maganar nan shi ya sa mu ka kai shi cen " wani dan karamin tsaki mama ta ja kafin ta fice da sauri , ba dakin Inaya ta koma ba , kai tsaye word room din ta fito kamar za ta tashi sama sai sauri sauri ta ke yi kai tsaye part Diya ta nufa , dan ta san shi kadai ne yanzu zai iya yarda da maganarta , kuma ya taimaka mata da sallama a bakinta ta shigo part din , nan ta tardo Nesrine zaune ta na rike da Junior ta na ba shi nono , Diya na konce saman dayar sofa ya zuba musu ido sai murmushi ya ke saki , kamar ya meda su cikin cikinsa ya ke ji a tare duk su ka dago kai su ka amsawa mama sallamarta da sauri Diya ya mike zaune ya na fadin " sannu da zuwa mama " wani dan murmushi ta saki kafin ta ce " yawwa sannu , Nesi ina fatan ki na kula da shi yadda ya dace , ko sai na taimaka miki ? " girgiza mata kai Nesi ta yi ta na fadin " no mama , duba ki gani ma " " mama , ku zauna mana ku na tsaye " Diya ya fada ya na mikewa tsaye zai ba su waje da sauri ta ce " a'a Diya , wajen ka na zo , ina son mu yi magana " bai kawo komai a ransa ba ya ce " bismillah " " no , taho muje dai " ta fada ta na juyawa ta fice nan ma bai kawo komai a ransa ba ya bi bayanta su ka fito ya na xe ma Nesrine yanzu ya dawo da to kawai ta amsa mishi ta ci gaba da shayar da babynta a harabar part din su ka ci karo da Abdoul ya fito da ga cikin part din sa , ya na ganin mama ya saki wani dan karamin murmushi ya karaso wajen ko ta kansa mama ba ta bi ba ta ce ma Diya " Diya ina bukatar taimakon ka , cemetery din da fitar masarautar nan za ka kai ni " da sauri Abdoul ya ce " cemetery kuma mama ? me za ki yi a cen ? " kafin mama ta ba shi amsa Diya ya rigata cewa " saboda a cen su ka bizine dayan babyn Auta , ni ma jiyo lokacin da Malik ke cewa nurse su boye maganar nan , shi ya sa na yi shiru ban ce mishi komai ba , amma ni ma na san baby triplets ne ta SAMU " " please Diya , mu je ina ji a jikina kamar yaron nan bai mutu ba , in ma ya mutum ina son auta ta gan shi in ba haka ba Aswad ba za ta kyale Malik ba , babynta ne ajikin na biyun " " shikenan mu je " Diya ya fada ya na yin gaba da sauri mama ta bi bayan shi su ka bar wajen , Abdoul dai ya zama dan kallo dan sam bai gane maganar me su ke yi ba ko da su mama su ka fito kai tsaye cikin motar Diya su ka shiga , su ka bar masarautar da mugun gudu a kan idon Malik dan ya na ganin duk abun da ke faruwa tun shigar mama part din Diya __________________________________________________ HAFSAT zaune ta ke tsakiyar parlourn irin zaman nan na cin tuwo , ta na sanye da wasu bakaken kaya na takaba , idanunta sun yi jazir , ta yi kuka har hawaye sun kassa fitowa ta na zaune a haka Manisha ta shigo parlourn ta na sallama ta na rike da tray cike da fruits , ta karaso gaban Hafsat ta ajiye ta na fadin " ki ci wani abu mana , ko dan babies din da ke cikinki " ta fada cike da so cikin bacin rai Hafsat ta sa hannu ta buge tray din nan take fruits din su ka watse cikin parlourn wani dan karamin tsaki Manisha ta ja ta koma saman sofa ta zauna , sannan ta ce " ki godewa Allah ma da Malik ya ce a sake ki , bai sa an cire miki kai ba , bisa abun da ku ka yi wa yar uwarsa " da sauri Hafsat ta juyo ta wurga mata wani mugun kallo da jajayen idanun nan nata " Ni kuma abun da su ka yi min fa ? ya kashe min mahaifina , yanzu ya dawo ya kashe min mijina " " Hafsat, ba ki yi dacen miji ma mahaifi ba ne , na san kawai dan ki dauki fansar kashe mahaifinki da Malik ke ya yi ki ka auri Aymane , abun da su ka shuka ne kawai su ka girba , mahaifinki ba mutumin kirki ba ne , ina sane da hakan na yarda na aure shi , ko kashe Marigayi Malik Hicham da ya yi kokarin yi ina sane , saboda na san mugun kishinsa da mahaifinki ya ke , in ba ki manta ba kafin Malik ya tafi Makkah , na samu rauni a hannuna wajen yankar fruits , aikin mahaifinki ne , babu ko tausayi ya sa wuka ya yanke min hannu saboda na yi kokarin dakatar da shi , shi da so ya yi ya samo jijiyata na mutu amma Allah bai yi ba , da bai samu nassara ba ne na ja baki na na hi shiru , haka Aymane ki na sane da abun da ya ke aikatawa , amma ki ka rufe ido ki ka goya mishi baya , yanzu wa gari ya waya ? " " no , karya ki ke min , kawai ki na son kare shi saboda yaron yar uwarki ne " " ke Hafsat , rashin mutuncin naki har ni za ki yi wa ? ni za ki cewa karya na ke " Manisha ta fada ta na dan zaro idanu da karfi Hafsat ta ce " na fada , na fada , duk karya ku ke min , mijina ba abun da ya aikata , ni ce shaida tare da shi na ke kwana na ke tashi , ban taba ganin shi ya sha jini ba , kawai ku na son yi mishi kasafi ne saboda azabar da na yi wa RIANNA , wlh ba zan taba bari ba Nawfel ya ji dadin rayuwarsa tun da ya hana ni jin dadin tawa rayuwar " wata yar karamar dariya Manisha ta yi ta na tapi , sannan