← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 71

Sashe 71

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Haba dai ni nasan Ahmad mutum ne me kyakykyawar zuciya baze taɓa kwatanta rama sharri da sharri ba, kawai dai nasan ya fahimci keɗin zuma ce seda wuta saboda idan ya ɗauke miki ai kina shiga taitayinki ki nemoshi kuma gara ya fara shata miki layi karki zata idan kukayi aure haka zakije ki cigaba da masa shirmen da kika saba gara ki sani da da yanzu akwai banbanci Mijinki yake shirin zama na random saurayi da kika sani a baya ba, amma wlh da ace ma da gaske tama ki yakeyi da naji daɗi domin kin azabtar da bawan Allahn nan koda yake Allahnsa ya rama masa kiyi addu'a Allah yasa abin ya tsaya iyakar haka" amsar da Badar ta bata kenan.

Biki ya rage sauran sati huɗu aka kai lefe kowanne gefe, na Jafar aka fara kaiwa Akwati iyakar ganinka gasu nan shaƙe da kaya saitin gwal biyar aka zuba wanda tsofaffin na Binta wanda Turai ta yi yaƙi ta bayar dasu aka narka akayo mata sababbin designs ta sake jaɓe su ta ajiye a ciki aka ɗiba aka bata kuɗin rabi kyauta dai haka akayi mata fahin kayanta. Tsabar zirgilli cewa tayi da ita za'aje dukda ba can Abuja aka kai kayan ba Adamawa aka kai can ne Asalin garin mahaifin Fatiyyan dan auran ma acan za'a ɗauro shi daga ƙarshe dai wayo aka mata aka gudu aka barta ai kuwa har kuka tayi, a waya Lawan ya ringa nuna mata videos dake trending dan su Fatiyyah fa bada wasa suke ba ita da Ƙawayenta sun gama gigita Social media da zancen Auran tun ana saura wata biyu aka fara save the date dan ma Angon yaƙi bada haɗin kai yanda ya kamata shiya ragewa abin Armashi dan cewa yayi ma se biki ya rage sati ze dawo da ƙyar ya maida shi sati uku.

Kwana biyu da aka kai lefen Jay aka kai na Ahmad, Lefe na mutunchi shima dukda babu tarkacen akwatuna kamar na Jay amma babu wanda ya isa ya raina lefensa ita kanta Hajiyar duk hassadarta da aka buÉ—e musu suka gani seda tace
"Ai daman Amadu badai zuciya ba ita dai yar Bakanike shar da ita toh Allah sa karsu kai kwari su karyar a samu na siyan kayan ɗaki, daman idan tazo kafi diddigi kai ka ɗauki hoton komai yanda ko tsinke ya ɓace zaka gane" kowa ya mata shiru dai ba'a tanka taba. Shima dai da aka tashi kaiwa guduwa akayi aka bar Hajiya, Hajiya Ummu Yayarta da suka zo kai Lefen Jay basu koma ba dasu aka tafi kuma ita tace acewa Binta seda Yamma za'aje tunda kusan duk wanda za'aje dasu a hanya za'a haɗu su da suka tashi fita sukace mata zasu shiga Kasuwa ne shikenan aka barta a gida tana saƙa irin abinda zatayi idan sunje, ta ƙudiri a ranta seta kunyata Aisha, ko za'ayi auran nan ba zata bari tayi shi cikin farin ciki da daɗin rai ba se gashi tana can tana saƙa mugun ƙulli taga ana shigowa da Ruwa da Lemo da Farantan kayan snacks ana kaiwa Ɗakin Momy.

Haka taje ta dirawa Alhaji Kuka wai Aisha ta wulaƙantata an kai lefen Ahmad banda ita bayan ita a na Jafar sune kan gaba cewa akayi ita zata wakilceta shi kuma, besan ya akayi ba be kuma bi ba'asi ba ya kira Aishar ya mata tatas akan me zatayi haka ta karya masa doka bayan ya kafa cewar duk sabgar Ɗa ko Yar wanda ta tashi sauran Kishiyoyinta ne zasu wakilceta a gurin ita dai bata tanka ba domin tayi rantsuwar ba zata bati Binta taci galaba akanta ta hanata jin daɗin auran sanyin Idaniyarta ba.

Rabon da Afeeyah ta shiga Social Media harda WhatsApp kuwa ta manta, fin watanni uku, kai tun bayan data yarda da gaske Jay ya barta ta cirewa kan lasisin duba Social Media ta sauke komai daga kan wayarta ta zama sedai tayi kira a kirata kawai saboda bata so taci karo da wani abu daya dangance shi, ko me suna Jafar aka kira a kusa da ita a ranar se tayi kuka balle kuma tun mugun ganin da tayi shida wannan yarinyar daya haÉ—a sunansa da nata har ya iya posting nata a private account É—insa ta tabbatar dagaske ne ya barta.

Dalilin shirin bikinta Badar ta uzzura mata seta bude WhatsApp da IG, tuntuni ta buɗe musu group acan anan suke ta shiri da sauran ƙawayensu amma babu Amarya a ciki, data rasa uzurin da zata bayar se tace bata da waya. Ita ta fitar da Ankon Yini da Kamu wanda zasuyi na gidansu Ahmad yace zasuyi dinner wannan mutum goma suka ware masu Anko dan karsuyi yawa musamman da bikin biyu ne, bisa uzzurawar Badar da take cewa
"You are getting married in to Bechi Family Afeeyah bafa wani karabitin Family bane ya kama muma mu motsa asan da anayi" Tilas ta koma kan Network ta saita komai da dare ranar bayan sun gama waya tana gaya mata mitar da mutane suke tayi ya za'ayi ace ana ta shiri ba'ajin ta bakin Amarya kuma shine ta gaji ya koma. Bayan sun gama maganganunsu a WhatsApp harta kwanta zuciyarta ta ringa Azazzalarta akan ta shiga IG, ta tashi ta kunna Data ta shiga, A jejjere duka bloggers da take bi taga sukayi posting hotonsu, ta ringayin ƙasa idanuwanta kamar zasu cire su diro Ƙasa, jikinta tamkar mazari haka yake rawa gaf gaf wayar ma Ƙoƙarin suɓuce mata takeyi, garin babi zafi sam domin yanayin sanyi ya fara shigowa ita da yake kumamace ma har safa ta saka saboda sanyin data ji bayan tayi Alwalar Isha'i se gashi lokaci gida Zufa ta wanke har kayan jikinta na naso.

Ta dinga duba hotunan kamar zararra ta shiga wannan page ta fito ta shoga na Ƙasansa domin kamar da gayya ake posting abun saboda ta gani. Su biyun babu wanda kamanninsa ze ɓace mata duk wuya duk daɗi haka kuma ba zatace gizo bane ko kuma Ƙwaƙwalwarta ce bata fassara mata daidai ba. Dadai taga kallon pictures ɗim baze kaita ba ta shiga duna caption ɗin da yake akan duka pages ɗin,
*_"Latest grooms in town, the Bechi brothers"_*.

Comment section ta shiga domin har sannan bata gama tantance abinda ta karanta ba, ta ringa scrolling yau idanunta sun zama kamar wasu scanner a seconds take karance abinda aka rubuta, ashe ba ita kaÉ—ai ce cike da mamaki ba, kusan tambayar da kowa yakeyi 'Daman Jay ÆŠan Bechi ne?'
Su nasu iyakar mamaki ne sedai ita ta shiga gigita, tashin hankali, É—imuwa kai babu abinda ma bata shiga ba, Jay shine Jafar É—in Ahmad kuma shine Jay É—inta?

Dishi dishi take ganin screen ɗin ma a zaune take amma juwa ke neman kwantar da ita. Ta shiga call log, she needs to call someone that will wake her and tell her that it was all a dream abinda ya faru a baya ba gaskiya bane ko kuma abinda take gani a yanzu shine mafarki ba gaskiya ba. Rikicewar da tayi ta saka ta kasa fahimtar kira ya shigo wayarta wanda Badar ce take kira, a kusan lokaci ɗaya suka ga hoton, Badar tasan Jay zeyi aure domin dai duk me shiga Social media tuni ya haddace ƙirgen Kwanakin auran Jay da suka rage wanda ze kama rana ɗaya dana Afeeyah, yana daga dalilin daya saka bata damu sosai da barinta hawa social media ba domin tasan sanin abinda yake faruwa ze iya rusa shirin da sukeyi na ganin sunyi bikin farin ciki. Ko yau WhatsApp tace tayi downloading ita kanta bata san sanda ta shiga kiran Afeeyar ba bayan data ga wannan twist ɗin domin a rikice take, Jay Ƙanin Ahmad ne kenan Afeeyah tayi soyayya da Yaya da Ƙani tana sane ko kuwa Arashi aka samu abinda take so ta tambayeta kenan.

"Afeeyah Ahmad and Jafar are brithers yanzu na gani a IG"
"Badar Ahmad and Jay are brothers tell me this is not true Badar ki cemun hallucination nakeyi" Afeeyah da Badar suka haÉ—a baki gurin faÉ—i kana iya tantance tashin hankalin dake cikin muryoyinsu karma ta Afeeyah taji labari.

END OF BOOK 2
Chapter 71 · 0% Book details