← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 71

Sashe 42

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afeeyah ta zumɓura baki, kafin tayi magana wayarta ta shiga ƙara, ringing tune data sakawa Jay ne dan haka ta miƙe da sauri da wayar a hannunta ta shige ɗaki Anty Sauda ta rakata da ido tana cewa
"Idan kina da rabo Allah ya ganar dake amma wlh nasan wannan Jay yake kowa yaudararki yakeyi ba auranki zeyi ba gara tun kina da sauran dama kiyi amfani da ita amma ba takanki zanbi ba, Baffa zan samu tun wuri asan abinyi baze yuwu shekara biyu ki gama yaudare bawan Allah kizo kice ba zaki aure shi ba" taja wayarta ta shiga kiran Baffansu sedai wayarsa a kashe. Tayi ƙwafa a fili ta sake cewa
"Har gidan zanje, gara ko auran dole ne miki tunda baki da hankali" ita dai Afeeyah na kan gado tana malele kuwa Jay na kasheta da kalaman Love, tunda suka shirya ta manta komai. Hatta maganar dake ta azalzalar zuciyarta ta mahaifiyarsa bata tayar ba tama manta da batun ta sake zama daram akan Alƙawarurrukan madarar ƙaunar da yace ze shayar da ita idan sukayi aure. Ya mata Alƙawari nan da watanni shida zezo Nigeria musamman saboda ita, ya kuma ce mata zuwan da zeyi zeje ya gaida Mahaifinta daga nan iyayensa suzo dan ya rigada ma harya gayawa Yayansa maganarta shima shirin Aure yakeyi tare za'a haɗa da nashi dan haka ta fara duk wani shirinta da idan yazo tana iya yuwuwa daga tambaya taji an ɗaura musu aure kawai sedai taji ana fito kibi Mijinki.

Ranar tayi dariyar maganarsa yace tasaka wasa zata gani da gaske yakeyi, Alhajinsu bashida wasa ko yau yace masa zeyi aure muddin ya yarda da inda ya nemo auran magana ta ƙare tambaya kawai za'aje ayo. Wannan tasa ta yanke shawarar sanar da maganarsa a gida tunda wuri ba wai se rana tsaka ba, ta fara takan Anty Sauda domin itace tsanin da ze kaita gasu Baffa. Muddin tayi na'am da abin tasan komai ze zo da sauƙi sedai daga yanda ta karɓi maganar tasan ko zata yarda se an yi ƙwaibai da ita dan tamkar Badar itama Ahmad ya lashe mata zuciya sonsa suke nasa son abinda ze taɓa shi. Daga ce mata sunyi faɗa tace seta kirashi ta bashi haƙuri idan ba haka ba ta gayawa Baffa ta samu wani saurayi yana hure mata kunne harta kori Ahmad ta masa wulaƙanci shiyasa ta kirashi.

****************
Hajiya Binta zaune kan carpet tana zubawa Alhaji Audu faten Accar da tayi masa saboda tana da buƙatu yau da kanta ta tsaya ta masa girki me kyau ta kashe gayu da wata kamfalarta shadda ta saka daham, lallen bikin da aka mata tun yau litinin yayi raɗau a hannayenta da Ƙafa dukda na Salatif ne me yankan Siga amma da yake fatar da sauran Armashinta ya mata kyau. Humrar da akayiwa Amarya Hafsatu ta bulbula abinta ƙamshin har hawa kai yakeyi dan seda Alhajinya kunna fanka bayan Ac dake falon saboda Atishawar da turaren nata ya saka ya fara jerawa.

Hira take masa wadda duk labarin irin tsaruwar gidan Hajiya ƙaramar take zayyana masa. Jiya su Turai suka dawo daga jere, dakyar da roƙon Allah ma ta yarda ta zauna dan cewa tayi da da ita za'aje.
"Wannan wane irin abune babu kunya kawai Binta ki bimu se a ganki tsalam ace ga uwar Amarya a ina kima taɓa ganin anyi haka? Ita Aisha data aurar da Yaya biyu gata uku wanne kika gani a ciki tajewa jere baku ne kuke zuwa ba se kece zakice se kinje salon ki zubarwa da yarinya ƙima tun bata kai ga shiga cikinsu ba? Abujar ce baki taɓa zuwa ba ko kuwa ance za'a rufe shigarta ne idan bakije yanzu ba?" Turai ta ringa zazzaga mata bala'i dan lamarin Ƙawar tata ya fara kaita bango.

Fafur tace Anty Rabi da Momy ba zasuje mata jere ba, Baba Bilki ma da tace ba za'a da ita ba dake har yau na sanyi tayi ba tace ai uban Binta ma yayi kaɗan balle ita ta hanata zuwa gano gidan Yar Audu. Saboda neman suna tace wai Hajiya Balaraba tazo aje da ita tace Aa saje kai Amarya daga ƙarshe dai bisa tursasawar Turai suka tafi da ita da Momy wadda bata so zuwa ba se Hajiya Zainab da Munirah ƙanwar Binta wadda har yau sama da shekaru hamsin kenan tana zaune bata samu Mijin aure ba bayan rasuwar Mamansu ne ta dawo nan Kano da ta fara zama gidan Binta zama yaƙi daɗi se kawai ta siyi gida take zaune abunta tana kasuwancinta tana cigaba da roƙon Allah daya yanke mata dukda ta san cewar ba komai ya janyo mata shiga halin da take ciki ba se haƙƙin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba suka laƙa mata sharrin da harta mutu wasu na kallonta dashi. Suka hanata zaman lafiya a gidan auranta harta koma ga Allah.

A can Kaduna suka haɗe da sauran yan uwan Binta akaje akayi jeren wanda babu wani abin arziƙi data siya. Kayan Gado dai a BECHI FURNITURES yace aje a ɗaukar mata duk abinda uba yakeyi saɓanin su Khadija dayake ƙayyade Adadin kuɗi yace a ɗauki kaya na kaza. Su Turai ne sukaje suka zaɓa suka darje kaya na ƙarshen mutunchi a shagon, da Alhaji yaga Invoice ya ringa surfa masifar da bata da Amfani domin dai shiya nada dama kuma sun rigada sun ɗauka har an jera dan a Branch ɗinsa na Abuja suka kwasa ƙarshe abin ya ƙare akan Aslamiyyah yace Gado biyu kujera biyu za'a ɗaukar mata saɓanin Hajiya ƙarama da aka sakawa huɗu, ɗaki biyar ne a gidan da faluka biyu manya se ƙarami ɗaya wanda yake haɗe da Master Bedroom a sama shine na Megidan iyayensa sun gyara masa dan haka hatta ɗakin da me aiki zata zauna Royal aka saka saboda samun guri da nuna akwai.

Kayan Kitchen dai daman yace musu a Al'adar Hausawa uwa ce takeyi to yana kan wannan magana har akan Hajiya be saketa ba dan haka ita tayi kayan kitchen tarkacen banza da wofi wasu matsiyatan kuloli da fulasai ta bakin Turai. Yanda ta ringa zuzuta ta gama siyan komai dan ƙin yarda suje siyayyar tare tayi, haka ta nuna mata kayan taƙi se randa zasu tafi Jere da za'a ɗiba aka tattara kaya ko cika buhu biyu basuyi ba amma faɗi take
"Kinga kaya ko Turai? Dama na gaya miki sena baki mamaki ai bikin Nazira shammatata akayi amma wannan na shirya"

"Billahillazi Binta idan baki fitar da kuɗinki kinci kin morawa kanki ba se kin mutu kina kwance a ƙasa zakiga yayanki na wadaƙa dasu, yanzu wannan kayan kike zuzutu akai? Abinda ko Talaka me zuciya se yayi ninkin abinda kikayi wannan abin kike so akai ace daga gidan Bechi suka fito? Turai ta ringa masifa kamar zata ari baki tana kafa mata hujja da kanta yanda takeyi idan zata aurar da Yayanta da sauran ƙawayensu, ta kawo mata Misalin Momy, auran Khadija da Annah ita da kanta tace har seda suka maido da wasu abubuwan gida dan seda aka kai sukaga an siya an ƙara siya tasan kuma yanzu ma na Aslamiyyah haka zata fitar da kanta kunay.

Duk wanda yaga kayan gadonta da kujeru yasan ubanta ne yayi mata ke za'a zaga ace uwarta bata da zuciya dan wlh ko yar riƙo a gidan nanta wuci akaita da wannan tarkacen. Ƙarshe se Alhaji Zakariyya da Alhaji Naziru harda Yakubu Turan ta kira tace kowa yazo ya bada abinda ya samu, ta tattara ta bazama kasuwa tayo mata siyayyar kayan kichen na fita kunya suka kai ta barwa Binta tsiyarta da tace ta ajiyewa Auta Saratu ta huta ita tasan ba zata raina wannan ɗin ba toh fa tunda suka dawo aka kawo mata Video shikenan ta kasa nutsuwa labari data kai aya zata maimaito tun Alhajin yana ji harya gaji yace mata

"Binta yanda kike nanata mun labarin gidan nan ko zuwa nayi yanzu bazan ɓata ba danna gama gane kowanne lungu da saƙo na gidan, ki bani abincin naci kafin ya huce dan Allah do nakeyi na fita zamu haɗu da Alƙali mu tattauna yanda taro ze kasance kinga lokaci yana ƙaratowa yau Litinin saura kwana huɗu ɗaurin aure".

"Ai toh yi haƙuri wlh santin gidan ne yaƙi ya barni, ai Hajiya dai tayi gida Allah ya tsole idon maƙiya yasa mutu ka raba" ta faɗa tana bashi. Shida ya shiga cin abincin yana jinta dan batayi shiru ba. Ta gyara zama tace

"Dama Alhaji zancen gurin Kamu ne an gama magana da mutanen nan yanzu sun dawo sunce wai kuɗi yayi kaɗan se an ƙara kuma ni nayi ƙarƙaf dubu Ashirin yanzu se nayi da gaske zan fito da ita ai bikin nan dai ya talautani da gaske".

Ya kalleta ta gefen ido a ransa yana mamakinta, wai ta kashe kuɗi kome ta yi se Allah bayan duk abinda ake ciki yana da labari. Zakariyya ya gaya masa su suka bada kuɗin kayan kitchen bayan ta ɗiora musu Alhakin abinda za'aci a gurin Mother's eve data shirya shi kuma nan be san Buhu nawa da galan na mai nawa da sauran kayan abinci data kwashe masa a Store tace za'ayi abincin biki ba. Kaji ɗari biyu ya saka aka bata ita kaɗai banda Sa da za'a yanka na abincin yini. Tunda aka fara zancen bikin nan Aisha bata ce ma ya bata sisin kobo ba, Bilki ce ta nusashsheshi har ya batan dukda be kai ko kwatan abinda Binta ta Ƙwamusa a hannunsa ba. Kayan gado kansu ya banbanta Hajiya Ƙarama cewa yayi su ɗauki wanda ya musu Aslamiyya kuwa dalilin ɓarnar da su Turai suka masa shiya faɗi kalar wanda za'a ɗaukar masa an gaya masa Ahmad da Sarki ne sukayi cikon Kuɗaɗe masu nauyi suka ɗaukar mata irin na Hafsatun kuma duk abinda ya kamata ace yayi wanda Aisha bata tambayeshi ba su sukayi yana kallo aka ringa sauke ruwa da lemo besan katan nawa bane inji Ahmad Jafar kuma shi ya siya Musu Cinema Tv su biyun nan cikin Yaya bila'adadin daya haifa ne suke da zuciyar bashi gudummawar auran ƙannensu dukda sun san yana dashi ba babu ba amma yaji abinhar cikin zuciyarsa.
Chapter 42 · 0% Book details