← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 71

Sashe 67

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shiru baka sake cewa komai ba dangane da full address da nace ka samo na gidansu yarinyar da kake nema" Baba Alƙali ya faɗa, ya sunkuyar da kansa yace
"Amm daman an samu matsala ne Baba so kuma na manta ban dawo na gaya maka ba"
"Matsala wace iri kenan?"
"Ita yarinyarce da akwai wanda suke tare kafin ni kuma bata gayamun ba se daga baya nayi finding out so i felt thar she betrayed me kuma bata da gaskiya if she could hide such important things to me may be bada gaske take so na ba nima".

Baba Alƙali ya ringa kallonsa kafin yace
"Kodai uwarka ta shiga tsakani ba?"
"Wlh babu ruwanta Baba bata san komai ba har yanzu kawai wannan dalilin yasa nayi blackout saboda ni bana son Ƙarya a rayuwata" Jay yayi saurin defending Hajiya. Alƙali yayi murmushi yace

"Amma ko zaka daɗe kana bincike kafin ka samu budurwa da take kula saurayi guda ɗaya, daman ai se anyi takara wanda yafi ƙarfi ya kayar da yan uwansa" cewar Baba Alƙali. Jay yayi murmushi, kamar ya sanarwa da Baban abinda ya faru amma baze so ya zama silar raba Ahmad da abinda yake so ba dan Baban baze bari ya aureta ba ya sani, gara ace ita da kanta taji kunya tace ta fasa tayi biyu babu so that bazeyi blaming kowa da cewar shi ya hanashi auranta ba.

"Ai ita Baba har iyaye sun san maganar fa for almost 3 years suke tare yana wahalta mata amma bata gaya mun ba seda naje gurin Babanta and from the way yayi maganar se naji kamar yafi son wancan ma akaina"

"Allah ya baka haƙuri ya musanya maka da wadda ta fita Alkhairi, shikenan zamu jira daga gurin mahaifin yarinyar da Ɗan uwanka yake nema shi saura sati Ɗaya wa'adin daya bamu ya cika, idan kuma duk an kasa ku ne se ku ɗauki haƙuri mu tafi Bechi a nema muku mata" ya ƙarasa maganar cikin raha Jay yayi dariya.

GIDAN MALAM HAFIZU
Kamar yanda na sanar miki sati biyu na bawa wanda kika kawo a matsayin zaɓin ranki, yau kwanaki goma sha biyu kenan tun zuwan da yayi be sake dawowa ba, ina sake tuna sar dake kwana biyu rak ya rage miki idan suka cika ba tareda ya gabatar da kansa ba karkiyi kuka da duk hukuncin da zan yanke domin na baki dama a matsayinki na Ya dan haka nima zan gwada iko na na uba akanki" Baffah dake tsaye akan Fatima ya faɗi.
"Kinji me nace ko?" Ya sake jaddada mata seta gyaɗa kai alamar taji ya juya ya fice daga ɗakin. Kwanciya tayi kan katifa ta fashe da kuka amma mara sauti, bata sake samun Jafar a waya ba tun ranar da wani ya amsa yace ze haɗasu. Ta tabbata kuma yayi blocking nata a WhatsApp da sauran social media handles ɗinsa dan duk inda ta masa magana bata tafiya sedai ta gaji da jira ta haƙura.

A ɗan lokaci ta fita a hayyacinta, zuciyarta zafi take mata ga ciwon kan da tayi ƙaryarsa ya aureta da gaske me azaba irin wanda ko idanu idan ya tasar mata bata iya buɗewa. Yanda Umma tayi banza da ita tamkar ta manta da wanzuwarta a gidan ne yake sake ta'azzara mata ciwo da damuwa, bata da wanda zata tattauna dashi, Anty Sauda ma ta juya mata baya, Badar Babansu bashida lafiya har an fita dashi India suna can dukansu tunda ta mata sallama basu sake magana ba kusan kwana goma bata san layin da zata sameta acan ba shi kansa Ahmad da take ganin ya zame mata ƙuda ta rasa yanda zata yaki ceshi a yanzu da take buƙatar ɓangaren da zataji sanyi shima ya kaucez tun randa yaje be sake komawa ba haka waya befi sau huɗu sukayi ba saboda ayyuka da yace mata sun masa yawa baya samun lokaci sosai wannan shi ake cewa rana zafi inuwa ƙuna babu inda zata tsoma ranta taji daɗi ga wani sabon batu da Baffah yazo mata dashi ita ya zatayi????

Daga kwancen da take ta janyo wayarta ta buɗe Tiktok, a can ne take zaton be rufeta ba kai tsaye tayi searching account ɗinsa ta shiga profile ɗin. Ƙirjinta ya buga dum da ganin video da yayi pinning a farko, hannunta har yana rawa ta buɗe, videonsa ne da wata yarinya, Jaa ce dan kalar fatarta farace irin me sirkin jini. Ƙirarta irin jikin yayan madarar nan da zaka gansu fatarsu luf kamar an hura musu iska a cikinta, kyakykyawa ce bata cika tsayi ba, tana da cikar ƙirji sosai da mazaunai wanda fitinannen ɗinkin doguwar rigar data saka ya bayyanar dasu. Hannayensu sarƙe da juna tana masa magana yana doka murmushin nan nasa me tsada. Ta ringa maimaita karanta Caption ɗin daya rubuta
# FatiyyahJay#

PAGE 24
Comment section ta shiga, hawayen da suka lulluɓe mata ido suka saka bata iya ganin abinda aka rubuta. Tana kuka tana typing
"Unblock me and answer my calls Jay dan girman Allah I'm going to explain ba abinda kake tunani bane" Tana turawa ta fita ta shiga gurin message nan ma ta fara jera masa maganganganu amma harta haƙura cire tsammani be amsa ba, kuma official account ɗinsa ne babu batun ace be gani ba. Wacece wannan yarinyar? Menene haɗinsa da ita? Ta ringa tambayar kanta. Kuka tasha har seda taji tana neman shiɗewa sannan tayi shiru amma hawaye basu dena zubar mata ba.

JAY

Abuja yayi zango bayan ya bar Kano, sati huɗu yayi niyyaryi tareda Afeeyarsa kafin ya koma, abinda yake ji a ransa yasa baze iya cigaba da zama a Kano ba kuma baze koma France ba dan ya san kewa ce zatayi masa yawa, damuwar da yake ciki nunkuwa zatayi. Ahmad ne ya rakashi Abuja as usual a Ƙoƙarinsa na son nuna komai lafiya lau sedai Ahmad ɗin ya masa shiru ne kawai yana binsa a yanda yake so amma ya gano tabbas akwai abinda Jafar ya ke ɓoyewa, sanin menene kuma ya barwa Allah yana dai da yaƙinin ko meye idan lokacin daya kamata ya sani yayi base ya tambayeshi ba ze gaya masa. Ya masa magana dai akan Afeeyah saboda sun fita da Alhaji yace masa Baba Alƙali ya masa zancen an fasa zuwarwa Jay tambayar aure kamar yanda aka shirya a farko, daya tambayeshi dalili yace masa

"Mayaudariya ce Azzaluma, tana da wanda iyayenta suka fi so yake wahalta mata for ages so tayi ta yaidareni Allah yasa na ganota da wuri" ya bashi sa. Ahmad yace
"Kuma da gaske kakeyi ka haƙura da ita? Daman duk kurarin soyayyar nan a bakine ba gaskiya ba? Ai na zata se in har kaji an ɗaura mata aure da wani ne zaka sare ashe ma bada gaske kakeyi ba"

"Yah Ahmad kenan" abinda ya sake ce masa kenan daga nan suka bar maganar dan shima be jata ba. Daya kaishi Abuja a ranar ya juyo dan da sassafe suka tafi be kuma zauna ba ya masa sallama ya juyo dan akwai ayyuka a gabansa sosai da yake so yayi. Wannan tasa Jay ya kashe wayarsa dan baya so wani a gida ma yasan be tafi ba, seda ya shafe kwanaki biyu a Hotel room sedai yayi wanka yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana tunani. Duk ta yanda ya ke lissafa ze warwarewa Afeeyah se yaga daga ƙarshe abin akan Yah Ahmad ze ƙare. Ranar daya kwana uku ya gaji da kwanciya da dare ya shirya ya fita, mota ya ɗauka a Hotel ɗin ya fita ya ringa yawo a titin Abuja harya gaji, haka nan yaji yana kwaɗayin Shawarma dan haka ya tsaya wani guri dake kan titin daya biyo.

Yana tsaye gurin cashier kamar daga sama yaji an kira sunansa
"Jayyy" yanda taja sunan ya sanar masa da wacece, ita kaɗai take kiransa haka mamakinsa ya akayi ta ganeshi? Ya juya baya kuma kota gaba ta kalleshi fuskarsa lulluɓe take da facemasks saboda tsaro. Ya juya sosai yana kallonta, FATIYYAH MU'AZ ce, fuskarta ɗauke da murmushi me kyau take kallomsa itama, kafin yayi wani abu ta isa gareshi ta rungumeshi and he couldn't help it but to hug her back.

"When did you come back to Naija?" Ya tambayeta bayan daya raba jikinsu, hannunta sarƙe cikin nasa tana binsa da kallo kamar mayya tace
"Since last month, mun ma dawo duka nan ai"
"Wow, at long last" ya faɗa da wide smile. Ta kai hannu zata zare masa facemask ya riƙe yana girgiza mata kai ta ɓata fuska,
"Excuse me sir, your order is ready" muryar wata waiter ta katse shi tana miƙa masa ledar kayansa ya amsa har sannan Fatiyyah na manne rabi a gefensa ya kalleta yace

"Let's go". A tare suka fito daga gurin, motar daya zo da ita suka shiga suka zauna Fatiyyah ta shiga É—aukansu hoto bayan daya zare facemask É—in.
"Ki bari muyi magana mana" ya faÉ—a yana kwace wayar ta sakar masa tareda maida hankali tana kallonsa harda yin tagumi da hannu biyu.
"Idanunta irin na Afeeyah" ya raya a ransa, ya san Fatiyyah tun kafin yasan ze haɗu da wata Afeeyah a duniya. Yarinyar CBN governor ce, a London suka haɗu, friend ɗinta ce Asali budurwarsa Maryam se kuma suka fara Ƙawance da Fatiyyan sosai daga ƙarshe ma Maryam ɗin tayi aure wannan yasa alaƙarsu ta fara canzawa da Fatiyyan saboda tana nuna so takeyi suyi soyayya. Yes tana da komai da ze saka Namiji ya sota amma beji yana ra'ayinta a lokacin ba, abinda ya burgeshi da ita har yasa ya kasa man tata yanda ta kama kanta taja ajinta ta rabu dashi tunda ya nuna baya ra'ayinta saɓanin sauran yammata da suke naci suna binsa yana wulaƙantasu kamar mayu. Kusan three years kenan basu haɗu ba suna dai chat jefi jefi se yau Allah ya sake haɗasu.

Sunata labari a mota har seda Maman Fatiyyah ta kirata dan tace zata siyo shawarma ne yanzu ta dawo kuma tajita shiru wannan ya ankarar da ita daÉ—ewan da tayi a wajen sukayi sallama ya rakata motarta, Shawarman daya siya ma bata yayi suka rabu akan zeje gidansu da safe kafin ya wuce saboda yace mata probably ya wuce France zuwa jibi.
Chapter 67 · 0% Book details