← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 71

Sashe 23

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tare dashi ne kawai saboda karamcinsa amma a kullum cikin addu'ar Allah ya fiddo mata da Miji daidai da ita takeyi ba zatayi ɗage ba ta kai kanta inda bata isa ba domin daga abinda Jafar yayi mata ta saka a rant tana tareda babban Ƙalubale idan ta shiga zuri'ar su Ahmad domin ba ƙarya Jafar yayi ba ya faɗi gaskiya ita ɗin dasu akwai banbanci, tazarar dake tsakanin su tamkar ta sama da ƙasa ce ta fito daga gidan Talakawa amma masu wadatar zuciya, Babanta Bakanike ne Ummata kuma Tela ce basu da wani gata sena ubangiji saɓanin su Ahmad da suka fito daga babban Ahali tana nufin gidan da aka tara Arziƙi na Kuɗi dana Zuri'a, Mahaifinsu Babban Attajiri wanda duk mutumin daya kwana ya tashi a Nigeria baki ɗaya yasan sunansa.
PAGE 9
Bayan ta idar da sallah tayi addu'a tana shirin tashi Maman Minal ta shigo masallacin, Roommate ɗinta ce dan haka ta dakata ta jirata tayi sallar itama kafin suka rankaya Hostel. Tana hango Senate Building Gayen ɗazu daya tareta ya faɗo mata a rai, taɓe baki a fili tace
"Wani sangangan dashi kamar basamude, kai wannan duk yanda akayi ya hada jina ma dasu"
"Suwa?" Maman Minal ta tambayeta seta tsuke baki tana cewa

"Ai yau gamo nayi da safen nan in gaya miki" ta kwashe da dariya tace
"Gamo Afee, na Aljani kona soyayya?"
"Mutum Aljan dai, wani fa sangamemen mutum in gaya miki, wlh gani na nayi a gabansa kamar nida Ruth, kofa fuskarsa bana iya gani sosai saboda yanda yayi sama da yawa".

Tsabar dariya seda Maman Minal ta kware ta dage Niƙab din fuskarta dan tasha iska sosai idonta cike da hawaye tace
"Kinga kin sakani irin dariyar da babu kyau meye kuma Mutum Aljan ana zaune lafiya? Inaga irin yan Basketball É—in nan kika gani sune zabga zabga ni jiya da daddare da naga wani Yaro seda gabana ya faÉ—i, kinga tsayi? gashi siriri kamar ze tsinke".

"Wannan ba siriri bane gaskiya yana da yar ƙiba badai sosai ba amma fa dogone yanda kika san jinjirin samudawa" ta sake faɗa tana hakaito Jay a zuciyarta.

"Allah ya shiryaki dai Afeeyah a ina ke kika taɓa ganin jinjirin samudawan toh da har kike kiran wannan haka?"

"To dai yau na ganshi, Allah yasa mu sake haɗuwa zan muku video sa ku gani" ta sake faɗa tana Ƙoƙarin zaro Id card suka shiga hostel.

Sururat na maida shinkafar data tace cikin tukunya sukayi sallama, ta amsa tareda watsawa Afeeyah hararar wasa setaa ajiye jakarta akan gadotna tana cewa
"Whats up my love?"
"My dear, if u like call me Shahrukan but you must wash this plates" muka kwashe da dariya harda ita da tayi maganar Maman Minal tace
"Ƙarshen love kenan ba, amma dai a mata haƙuri ta huta yanzu, kinga duk ta rigamu fita da safe"
"Wlh Anty Zarah na you dey spoil dis girl, haba yarinya se gaye cinguli work she cannot do" Sururat ta cigaba da Mita, Afee ta rungumeta ta gefe tana dariya tace
"Haba sisi na kinsan fa zan wanke yanzun haka wlh kaina ciwo yakeyi, we had a boring class and i still have one more to go" mtsw tayi ƙaramin tsaki danda gaske kan nata ciwo yake mata.
Fuskarta Sururat ta nuna tausayawa kafin tace
"Eyya, let me finish cooking then you eat and get some sleep you will fell better, sannu kinji".

Afee ta wuce gaban gadona ita kuma taci gaba da hada Salad ɗin da takeyi, kayan jikita ta cire ta daura Zani harta zauna kuma kawai ta ɗauki Hijabi da Jakar kayan wankata da Bucket daya ta sauka ƙasa. A bathroom ɗin down floor tayi wanka ta ciko bucket da ruwa ta koma lokacin har Sururat ta gama abincinta zuba musu a babban Try kamar yanda suke ci yawanci idan kowa yana ɗakin yau su uku Badar na Kaduna tasan dai tana hanyar dawowa Ummi kuma se Five zata gama Lecture, Ruth tana kan gadonta duk yanda suke janta a jiki da nuna mata an zama ɗaya takan kama kanta musamman irin lokutan da suke cin abinci sedai ta ɗibi nata a plate daban amma ba zataci dasu ba.

Tsaf suka cinye abincin data saka musu suna santi dan Sururat ba daga nan ba gurin iya girki, ta wuce wanka da sauri dan tana da aji ƙarfe biyu ita kuma Afee ta tattare gurin ta haɗe kwanukan dattin duka a bokiti ta sauka dasu ƙasa. Wata Mama da take kai munu ruwa da wanke wanken wasu lokutan n
Ta bawa kwanukan na koma É—aki. Maman Minal tace mata

"Afee bari naje dakinsu Nnenna mu Ƙarasa Assignment ɗin nan"
"Sannu Eng girls" ta faɗa tana hayewa gado. Tana ganin Ƙoƙarin Maman Minal wato Anty Zahra, Mechanical Engineering take aji biyar. Matar aure ce harda yaranta uku kuma da auran nata ta fara karatun lokacin tana da cikin fari gashi a shekara hudu tayi yaya uku kuma cikin luɗufin ubangiji bata taɓa samun carry over ba Allah ya taimaketa ya bata Miji me fahimta da son tayi karatun duk dashi ba dan boko bane hasalima iyakarsa secondary school amma be tauyeta ba kuma iyayensa sun bata gudummawa Yaranta uku duk a hannun uwar Mijin suke yanzu da sun shekara zata ce ta yaye su taji da karatunta suna can Kaduna ita kuma ya kama mata daki a Off K tun Level one ba kuma ya gajiya da kawo mata ziyara A final year din nan ne ta dawo cikin makaranta gaba daya da zama kuma a nan suka haɗu ɗaki ɗaya da ita sedai idan Mijin zezo ne zata buɗe
É—akinta na Off K ko idan matsalar rashin ruwa ko wuta ta faru a cikin makaranta zasu tafi can duka. Ita ce ta zama Kamar Babbar Yayarsu duk abinda taga zasuyi mara kyau zata tsawatar musu tsakani da Allah take zaune dasu shiyasa suke bata girma sosai.

Bata san tayi bacci ba seda Ƙarar Alarm data saita ta manta wayar a saitin kanta ya tayar da ita, a firgice ƙiris ya rage ta faɗo daga gado. Ta ringa tsaki kamar wani ya aje mata wayar, ganin tsakin baze kai ta ba ta miqe. Duk sun fita se ita kaɗai ashe, a gurguje ta sake watsa ruwa saboda yanayin garin da akwai zafi tayi Alwala, Riga mara nauyi me spagetti hannu ta saka ta zame ribbon ɗin kanta, tafi kwana uku bata taje kan ba sedai ta saka hannu ta warwareshi dan bata son jan gashin ta koda kanta ne balle wani yaja mata shiyasa bata kitso ta kwantar sa gaban da bruah kafin ta saka Chantilly cap ta zura Jilbab kalar Maroon me duhu tun wanda Ahmad ya bata haɗuwarsu ta farko, Son Hijabin take kamar rai, dukda ya sake siya mata wasu har Number matar da takeyi wato *UMMU MAHEER 07061838488* Ta karɓa a gurinsa saboda duk wanda ya gani se yace yadin masa kyau a ina ta siya shine kawai Ahmad ya bata shawarar ta fara siyarwaq sosai kuma take cinikin Hijaban a cikin Campus.

Ta kalli kanta a Mudubi, gani tayi tayi haske fau da yawa kamar wata Zabiya yau hakan yasa tayi saurin cire Hijabin ta lalubo wani Fari ta saka, Badar ta tsani Hijabin, na Anty Sauda ne da tayi Umarar Azumi dashi ta karbo duk sanda ta saka se Badar tayi tsaki tace "se kace fatalwa" ita kuma son Hijabin takeyi.

A gurguje ta fita, tana shirin kulle Ƙofa Badar ta hawo saman da ubannin ledoji tana nishi, ta banka wa Afeeyah Harara ita kuma ta fashe da dariya saboda yanda ta rungumo kaya kamar irin haɗamammun Yaro boys da ba zasu bari wani ya samu ba mayafin tama a Ƙugu tayi ɗamara dashi.

"Dole kiyi dariya mana tsabar rashin mutunchi ashe kina nayi kiran wayarki yafi sau nawa baki amsa ba" ta fada tana zube kayan a bakin ƙofar. Ta buɗe mata ƙofa tace

"Wlh banji ba ina ta sauri karna makara me yasa baki ƙwalo mun kira daga ƙasa ba to se nazo na tayaki"
"Na gama shan wahala tun daga Bakin Hostel se na tsaya wani jiran ki dallah gafara na wuce" ta faÉ—a tana tureta, Badar rigima, ta matsa mata ta shige ita kuma ta ajiye jakarta ta fara shigar mata da ledojin tana cewa
"Sannu da hanya, da naji shiru na zata ma se gobe zaki dawo".
Kayanta ta shiga cirewa tana cewa
"Neman magana dai, kwana biyun ma kamar Momy zata cinyeni kinsan da yanda ta barni na kawo yau da cewa tayi jiya komai dare se na taho ai"
"Allah sa ba tayi fushi ba da banje ba?" Afeeyah ta faɗa tana aje ledar ƙarshe se Badar ta zare ido tace
"Ai gara da bakije ba, inaga da muna shiga zata ce mu juyo, ƙarshe ma gori na jawa kaina tana cewa ita so tayi ta haɗa mu dukka ta huta shegen baqin jinina yasa seta sake kashe kuɗin kama gurin biki daban harda fa cewa ƙawayenta wai idan sunji wani na neman mata gani".

Afeeya ta dinga kyalkyala dariya har seda taazauna, wato Momyn su Badar character ce me zaman kanta matar nan ga kirki ga zafi babu abinda ya shalleta tas zata maka akan gaskiyarta. Seda ta gama dariyar ta miƙe tana ce mata
"Toh na Jira ki ko na tafi?"
"Ai ko HOD ne zeyi Aji yanzu dai ba zani ba wlh gara ma ki tafi kya samu ki mana Attendance" ta bata amsa tana zuba ruwa a bokiti Afeeya ta fita a ranta tana mamakin Yau batayi mata Ba'ar Farin Hijab ba ilai huwa se ji tayi tace
"In kika mutu a hanya an huta nemo likafani kaiki kawai za'ayi".
Chapter 23 · 0% Book details