← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 71

Sashe 19

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yana nan da halinsa kenan be canza ba? Is high time da muma ya kamata mu mallaki gidan kanmu haka a dena zuba mana Iko, small thing ze fara badai a gidana za'ayi this ba? A gidana kuke mun that?" Jafar ya faɗa yana mimicking muryar Alhaji Audu. Ahmad dasu Salim sukayi dariya, dole ya fita ya sallami Fans ɗakyar kafin ya koma ciki Matan da Hajiya ta tara nata fitowa kowa na kama gabanta ya ɗauke kai kamar be gansu ba yanajin Yannatan na kiran sunansa amma ya share. Shi ko ƙawar hira be hango a cikinsu ba balle Alaƙar da iyayensu suke son ƙullawa dashi.

Bayan Magriba suka shirya shida Ahmad sukaje gidan Late Brigadier General Baballiya Bechi yayiwa Matarsa da yaransa Ta'aziyya, daga can Ahmad yace su biya gidan Baba Alƙali sukayi rashin Sa'a baya nan yana Abuja se washe gari ze dawo inji Mama Balaraba, dukda basu tarar dashi ba amma suka zauna har kusan 11 suna can dan idan sukaje gidan nan basa iya fita da wuri daman musamman da suka tarar da Fadlan ya fara caccakar Jay akan Premier League wai suna kwan gaba kwan baya, se sunyi sama se su diro ƙasa sun kasa yin abin kirki. Drama Jay da Fadlan daman bata ƙarewa tunawa da dokar Alhaji Audu ta hana kaiwa dare a waje yasa suka tafi a 11 ɗin.

"So we go cross fence today" Jay ya faɗa sanda suka tarar da Kantamemen Get ɗin gidan a garƙame, Ahmad yace
"Da rabon kayi kwanan Cell kuwa, gidan Alhajin Bechin zaka haura? To sauka nayi tacan farkon Layi karma yace tare muke" suka fashe da dariya suna tuna wani lokaci zamanin yarinta Jafar da yarbanzar ƙiriniya Hajiya bata nan ta kukke ɗakinta ya shiga ta window wai ze ɗakko Uniform ɗin Islamiyya ya shiga amma fitowa ta gagara a zatonsa bata saka key ba a Ƙofar ze buɗe ta ciki ashe ta murza Key abinta haka ya zauna
ɗaki har Magriba akayi sa'a Alhajin ya riga Hajiya dawowa akace ga Jafar can ya haura ɗaki ya kasa fitowa Alhaji ya tubure se an kirawo yan sanda kafin a buɗe ƙofa se su tuhumi Jafar dalilin daya saka ya haura masa gida dakyar fa Aka bashi baki ya ɗauko spare key ya buɗe shi amma yaci duka a gurinsa ranar.

Horn Ahmad ya danna, Issa ya leƙo ganin motar Ahnad ya buɗe Ƙofar,
"Da alama Alhaji baya gari" Ahmad ya faÉ—a bayan da ya ajiye mota. Issa yace
"Aa, mun faɗa masa kunje gidan Alhaji Soja kuma kunayin dare acan shine yace idan kune a buɗe, idan ba ku bane kowaye ya kwana ga waje, kuma Alhajji Yaƙubu bayaga gida? Ko bashi a Kano baki ɗayane?" Ya tambayesu.

"Ohna manta ko banga Yah Yakub ba, ko baya nan?" Jafar ya faÉ—a Ahmad yace
"I'm not sure da safe dai mun haÉ—u, ta yuwu yayi tafiya ko kuma Gidansa ze kwana kasan Yah Yakub ya zama jan wuya Alhaji ya saka masa ido kawai"
"Kodai Hajiya ta tsaya masa ba?" Inji Jafar daga nan suka wuce É—aki, yana so yaje gurin Hajiyar amma yasan tashin hankali ze siyo da se ta hana kowa bacci a tsanake gara ya bari ayishi ido na ganin Ido.

Ƙofar falon Alhaji da suka gani a buɗe tasa suka fahimci yana ƙasan dan haka suka shiga sedai suna saka kai duk su biyun sukayi dana sanin shiga a lokacin, Hajiya na zaune da akama su take jira, Jay ya juya ze koma Ahmad ya rufa masa baya ta tashi da hanzari ƙiris ya rage ta hantsila tana cewa
"Gasu nan, ka gani ko ya janyeshi sunfita ze fara koya masa yawon Iskancinda yakeyi, wlh tallahi kayi mun tsakani da Aisha da zuri'arta ta fita a sabgata idan ba haka ba ta bari na waiwaya kanta wlh na lahira se ya fita jin daÉ—i.

Banda tsabagen an juyar masa da hankali Jafaru ne zezo ƙasar nan ya shiga sabgoginsa tamkar na mutu baya tunawa dani? Kalleshi fa, kai da gani kasan ba a hayyacinsa yake ba to na rantse da Allah duk abinda mutum yake taƙama dashi na dameshi na shanye kuma se na nuna muku ku baku san komai ba ƙananan yan banza ne ku, dallah wuce ka bawa mutane guri kana wani sunkuyar da kai kamar na Allah kai kuma shigo nan" ta dakawa Ahmad tsawa. Daman neman hanyar tsira yake dan haka da sauri ya wuce ya bat Jafar a gurin.

A gurguje yayi shirin bacci yana sake gwada kiran Fatima. Tun da rana da sukayi magana yace mata ze É—auko Jafar ya sake kiranta kusan sau huÉ—u bata amsa ba, sanda suka fita tareda Jafar ya kirata tace she will call him back tana abune amma shiru yanzu kuma neman abinda ze hana maganganun Hajiya tasiri a zuciyarsa yakeyi shiyasa ya kasa jirn ta kirashi kamar yanda tace yake sake kiranta.

Ko dazun ma da rana sanda ya ɗauko Jafar fita kawai yayi daga gidan ya tafi can bakin titi daya gwada wayar Fatima be samu ba ya zauna yana ƙirga motocin da suke wucewa har zuciyarsa tayi sanyi shine ya dawo gidan.

Yaja tsaki yana cilli da wayarsa akan gado dalilin kiranta daya sakeyi sau biyu bata ɗauka ba, wlh da ze iya cire sonta daya masa kamun kazar kuku daga zuciyarsa daya haƙura da yarinyar. Duk wasu alamu na nuna rashin karbuwarsa a gurinta ta gwada masa, ya rasa Aibunsa daya saka Fatima ba zata so shi ba, shiɗin da Mata suke bi kamar ƙuda da Alawa shi Mace take wulaƙantawa gaskiya So baya kyautawa sam.

"Lafiya kake tsaki Yah Ahmad ga wayanka kuma a ƙasa?" Jafar daya shige fuska tayi jaa ya faɗa, Ahmad ya kalli ƙasan dayace, ashe wayar can tayi tsalle ba kan Gadon ta tsaya ba. Ya sake yin tsaki ya ɗauka, Screen ɗin ya tsage, sabuwar wayace Dal Samsung ƙirar shekarar Kwanansa huɗu da bareta, guda biyu ya siya ze bata ɗaya idan sun dawo hutu ko yaje Zarian ko screen guard be saka mata ba gashi takaicin Fatiman ya saka ya fasata. Dannawa yayi ya tabbatar iyakar Screen ne faɗuwar ta taɓa be shafi Sensor ba dayaga lafiya lau take ya ɗorata kan Bedside ya kwanta.

Jafar daya gama shan Rap a gurin Hajiya abin takaici Alhaji na zaune yanajin yanda take aibata Ahmad tana ɗora masa Alhkin wai son ya rabata da ɗanta amma ya gagara cewa komai harta gaji ta barshi ya taho. Wanka yayi ko ze samu sauƙin bacin ran da yake cikiz Ahmad daya kasa bacci abin tausayi ya sake ɗaukar waya yana gwada number Fatima tana ta ƙara amma bata ɗaga ba. Tashi yayi ya shige banɗakin da Jafar ya fito.

Jay ya zauna a bakin gado ya ɗauki wayar Ahmad. Tunda suka fita ya lura da yana ta trying qata number idanbata shiga ba yayi tsaki ya ajiye waya har a gidan Baba Alƙali hankalinsa rabi baya tare dasu shida Fadlan ya barsu sunata surutu. Call log ya shiga sunan FATIMA ya fara cin karo dashi da wata Red heart a gaba. Yaja tsaki a fili yace
"She must be that Mechanic daughter, har take da guts ɗin wulaƙanta Yah Ahmad".

Haka kawai ya sake danna kiran number zuciyarsa na tafarfasa addu'a yake Allah ya bashi sa'a ta ɗaga, cikin ikon Allah kuwa ringing uku yaji an ɗaga, Fatima tsaye a gefen Tukubar Sambo me Mac Dee tana jiran a sallami Badar. Test garesu har biyu a gobe dan haka tunda yamma suka fita karatu. A silent ta saka wayarta shiyasa bata ji kiran Ahmad na farko ba, da sukaje sallar Magriba kuma taga missed calls, fa sukaje sallar isha ma ya sake kira tace she will call back amma ta manta bata kirashi ba kamar yanda Badar tace saboda baya gabanta shiyasa har take mantawa da abinda ya shafeshi. Kiran da yake tayi mata na yanzu kuma ta na gani dan wayar na hannunta da ita take karatu ƙyuyar ta tashi ta fita daga class ɗin ta amsa wayar ya saka taƙi dagawa ganin yanata kira yasa tayi rounding off suka fito dan daman Badar tace ta gaji bacci takeji, suna tafe seda suka wuce FSLT Badar tace wai yunwa takeji zataci Mac Dee shine suka zarce gurin Sambo a gaban Social Centre tana ta Allah Allah a sallamesu ta shiga hostel ta kirashi sega kira ya sake shigowa wannan dalilin yasa ta ɗauka muraya a sanyaye cike da gajiya da bacci tayi masa sallama.

"Dallah riƙe sallamarki Malama, who the hell do you think you are da har zaki ringa wulaƙanta mutum kamar Ahmad? Do you even deserve to date someone like him? Koda yake daman haka kuke Yayan Talakawa yayan Matsiyata ku ba kowan kowa ba se shegen girman kai da isa kamar wasu sarakai. Imagine Yar Mechanic, bawai me Gyaran Mercedes Benz ko wata Lambo or Tesla ba just a common mechanic may be ma Motorcycle yake gyarawa not even cars shine kika samu damar raina Ahmad Bechi saboda he stop so low yace yana sonki. I even began to think anya ba Asiri kikayi masa ba?
Ke koma dai Mayyace ke because they way Ahmad is behaving yafi kama da someone that is possed.

"What ever you have done to him bear it in your mind bazaki Aureshi ba, in har ina raye i will make sure that ko Inuwar Ahmad baki tsaya tareda ita ba balle har kiyi tunanin Auransa. Look for your mate ki kuma sakar masa Soul idan kuma ba haka ba zanyi maganinki, ni Jafar Bechi i will be the end of you akan Ahmad zan iya sacrificing life É—ina kuma bazan saka ido ina kallo yayi wasting rayuwarsa on worthless thing like you ba ku....."

"Jafar..." Ahmad daya fito daga wanka ya kira sunansa cikin ƙaraji kafin ya kwace wayarsa. Ya duba screen tabbas da Fatima yake magana ita yake faɗa wannan kausasan maganganun daya taraddashi yana faɗa. Na ƙarshen ma yaji Allah kaɗai yasan me yace mata daga farko.
Chapter 19 · 0% Book details