← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 71

Sashe 60

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki bayyane akan fuskarsa yake kallon Ahmad sanda ya durƙusa yana gaisheshi dan daga nesa be gane shi bane ko kuma be kawo ze ganshi a irin lokacin bane yasa be kawo shiɗin bane.

"Fatima ce na kirata tana kuka tace mun bata da lafiya" Ahmad ya bawa Baffah daya tambayeshi ko lafiya ySa ganshi yanzu amsa. Baffah yayi shiru kafin ya tura ƙofar yayi ciki yana ce masa
"Bismillah"
"Aa Baffah ta fito muje Asibiti kawai kar a ɓata lokaci" ya bashi amsa kai a ƙasa. Baffah ya shige ciki ya tarar da Umma a tsakar gida tana yan kaye kayenta.
"Ina Afeeyah?" Ya tambayeta, ta nuna masa É—akin Afeeyar da hannu dan haushinsa takeji seda suka tafka mahawara jiya kafin sukayi bacci. Wai ya bawa Jafar sati biyu ya turo, data tambayeshi yasan shi ne ko yayi bincike a kansa da zece ya turo maganar aure sati biyu se yace mata

"Banji a jikina yaron nan ze aureta ba koda yana sonta shiyasa nayi musu haka kinga daga ita harshi babu wanda zece an tauye masa haƙƙi. Yace sunan mahaifinsa Abdullahi Tijjani Ɗan kasuwane kuma a unguwar Hotoro suke zaune zan sanarwa Malam Saminu seya bincika shine me mutane a shiyyar dan binciken Ahmad ma kinga shi yayi"

"Lallai Malam, wato bakaji a jikinka auranta zeyi ba? To idan kuma ya ƙaryata jin naka ya turo magabatansa se ayi yaya?" Umman da mamaki ya cikata fal ta faɗa Malam ya sake tamke mata kai daya ce
"Ruƙayya, duk wanda yake shine Alkhairi a gareta Allah ya tabbatar mata, Allah yaga zuciyata, idan son rai na ne Ahmad shi ze zama Mijin Mamana amma tace ba haka ba, bazan mata dole ba zan cigaba da bibiyar lamarinta da addu'a Allah ya zaɓar mata wanda yafi Alkhairi a cikinsu". Tsabar yanda ya kasheta da mamaki yasa ta gagara ce masa komai se kallonsa da ta ringayi, wato baze mata dole ba
"Ai shikenan" ta faɗi ta maida kai ta kwanta ranta fal da mamakin Malam Hafizu. Da sanin yau ta masa se tace kwaɗayin matsayin sabon yaron da Afeeyar ta kawo ne ya jashi to amma idan Arziƙine a Nigeria dai ai ba'a gayawa Audu Bechi uban Ahmad ba. Ta yuwu makauniyar soyayyar Uba da Ya ce tasa ze zama sullutu ya biyewa Afeeyar ta mayar dashi Ƙaramin mutum. Ta raya a ranta zata saka musu ido shi da yar tasa ne taga gudun ruwansu ba zata sake cewa komai akai ba, da wannan haushin ta kwana shi yasa da safiyar da yake tambayarta ina Afeeyar ta masa nuni da ɗakinta kawai taci gaba da sabgar gabanta.

Baffah ya kada baki ya kira Afeeyah dake kwance wurjajan tana kuka jin daɗi, yo jin daɗi mana babu duka babu zagi mutum ya ƙule a ɗaki yana kuka ai se wanda daɗi yaiwa yawa. Ta amsa tana goge hawayenta kafin ta fito tana kare fuskarta da Hijabi. Saboda karma Umma taji abinda ze hasalata yasa ta shigi kitchen ta basu guri, tana jin Malam na tambayar Afeeyah me yake damunta?
"Ahmad na tarar a waje yace kunyi waya yanzu kince masa baki da lafiya meya sameki" inji Baffah. Ta kalleshi da mamaki tana maimaita "Ahmad kuma?" A fili yace
"Eh shi, ko bakuyi waya ba"
"Munyi, amma ai bace masa nayi yazo ba kuma ni lafiya ta Ƙalau" ta faɗa a sanyaye.

"Se kije ai ki sallameshi gashi can duk hankalinsa a tashe, wlh yaron nan tausayi yake bani Jarabta a so babban abu ne me wahalar gaske" Malam ya faÉ—i yana wucewa É—akinsa Umma data fito da tukunya zata tari ruwa a famfo ta koma kitchen ba tareda ta kalli inda take bama ita kuma Afeeyah tsoron abinda Umman zatace ya hanata tashi daga inda take har seda Malam ya sake mata magana.
Ahmad na jingine da ƙofar gidan, daka ganshi kasan yana cikin damuwa duk yayi wani iri yanajin an taɓa ƙofar ya juya da sauri sukayi ido huɗu.

Gabanta ya yanke ya faɗi ba tareda wani dalili ba, kai a ƙasa kamar wata farin shigar munafurci ta gaishe shi,
"Muje Asibiti Fatima me yake damunki?" Ya faɗa yana matsawa gabanta. Ta girgiza masa kai idonta na tara Ƙwalla tace
"Ciwon kai ne daman kuma ya sauka"
"Ciwon kan kikewa kuka haka Fatima? kalli fa yanda fuskarki ta koɗe yanayinki ya nuna ba lafiya ba sannan kice ciwon kaine kuma ya sauka" Ahmad ya faɗa yana ƙare mata kallo.

"Dagaske nakeyi maka ciwon kaina yana da zafi sosai har nakan gwammace nayi zazzaɓi akanshi"
"Kinga kenan kina buƙatar Dr's attention dan haka muje Asibiti kawai"
"Dagaske na warke nasa magananin da aka bani akan duk sanda ya motsa mun nasha Migraine ne" ta sake faÉ—a cikin tabbatarwa. Se tayi murmushi kallonta yace

"Kodai biko na kikeyi shine kika fake da ciwo saboda ki tasoni ko ban shirya ba?"
Tamkar tace masa tayi bikonsa a saboda me se kuma tayi shiru tana wasa da yatsunta murmushi ya kwafsa mata ta hanyar sakin kansa ba tareda ta shiryawa hakan ba. Ahmad yayi murmushi yana gyara tsayuwarsa yace

"Duk sanda nafara fitar da rai da tsammanin samunki se Allahya kawo silar da zata sake maido ni rayuwarki bakya ganin hakan bayinmu bane yin Allah ne? Ta yuwu akwai wani tanadi da yayi mana amma zukatanmu na nesan tamu da riskar wannan tanadin akan lokaci?"

Bata ce komai ba be kuma damu da hakan ba yaci gaba da cewa
"A yanzu na rigada na buɗe zuciyata, na sallamawa Ubangiji komai dukda dama a kullum cikin miƙa lamurana a gareshi nake. Tunda kince lafiyarki Ƙalau bari naje gida, se wani lokaci" be jira komai ba ya wuce ya barta a tsaye. Jiki ba laka ta koma ciki ta dasa jiran tsammanin samun kiran Jay amma har Azahar shiru babu shi babu labari.

Ahmad kuwa bayan ya koma gida ya tarar da Jay na shiri daya tambayeshi ina zeje yace masa Kaduna daga can ze wuce Abuja gidan Hajiya Ƙarama. A taƙaice yayi masa bayanin da Hajiya ta masa jiya, Ahmad ya jinjina Al'amari, Allah kenan me mutane iri iri. A haifi mutum amma tsabar shahara yace shi baze haifi wasu ba to Allah ya rufa asiri. Be ce ze bishi ba kamar yanda shima be nemi rakiyarsa ba za'a iya cewa wannan shine karo na farko da hakan ta faru ace Jay zashi wani guri ba taredaya nemi rakiyar Ahmad ba. Tareda Manager shi suka tafi shi kuma Ahmad bayan ya shiga gida sun gaisa da Momy da sauran mutane ya tafi Shago duk yanajin babu daɗi. Tabbas akwai abinda yake damun Jafar, amma menene wannan da har ya gagara tattauna matsalarsa dashi?

Jiyayaje gidansu wacce yake so basu samu sunyi magana ba balle yaji yaya sukayi tunda kafin ya shigo shi yayi bacci da safe kuma ya fita to kodai shima ya samu matsala irin tasa ance ya dakata ko kuma ma dai iyayenta sun rigada sun mata Miji? Tunanin da Ahmad ya ringayi kenan yana zaune a office ɗinsa. Ya ɗauki wayarsa ze kira Jafar sega kiran Fatima ya sake shigowa wayarsa. Mamaki kamar yayi me, Fatima dai yau meya sameta haka acw a rana da kanta ta kirashi har sau biyu wannan abu kamar Almara. Be sake rushewa da mamaki ba seda ya amsa bayan sun gaisa take tambayar ya yaje gida sannan ta bashi haƙurin tayar masa da hankali da kuma fito dashi da sassafe daga nan sukayi sallama dan ya gagara sakin jiki yayi mata wata Ƙwaƙwarar magana.

Allah sarki zuciya da abinda take so, ɗan wannan kiran yasa duk ya rikice ya cigaba da ɗora lissafin gobensa da Fatima, daya tashi daga Shagon daƙyar ya kanne ya wuce gida dan zuciyarsa nata uzzura masa da ya sake zuwa ya ganta ya kumayi mugun Ƙoƙari da be kirata ba. A daren Jay ya dawo, se yaga kamar sanda ya tafi yafi nutsuwa da kwanciyar hankali akan dawowarsa duk ya wani birkice kuma bece masa komai ba still shima ya kama bakinsa be tambayeshi ba.

A ɓangaren Afeeyah kuwa abu kamar almara haka aka wuni sur tun tana zaton Jay ze kirata harta fitar da rai ta shiga lalube da lissafin yanda rayuwarta zata kasance idan har da gaske Jay ya barta. Ta kirashi sau biyu wayar ta Ƙaraci ringing ba'a amsa ba kuma be biyo baya ba har dare, A ɗaki ta wuni, sunyi Chat da Badar bata ɓoye mata komai ba akan zuwan Jay na jiya, yanda sukayi da kuman zuwan Ahmad da safe harma da Stand ɗin Umma akansu biyu

"Allah na sonki Afeeyah, karki bari ki rasa damar da kike da ita a hannu wlh ba zaki maimaira kamarta ba. Bakoda yaushe abinda muke so a rayuwarmu yake zama Alkhairi ba haka kuma ba duk abinda muke ƙi ne yakan zama sharri tare damu ba. Kiyiwa kanki karatun ta nutsu ki kalli gidajen aurayen da suke a zagaye dake wanda akayisu cikin daɗin rai da sahalewar uwa da uba amma ba'a rabasu da ƙalubale da matsaloli inaga wanda akayi kan doron fushin iyaye? Yanzu ke zaki iya zaman aure da Mijin da mahaifiyarki ta nuna bata sonsa? Bana tsammatar zaki samu cikakkiyar nutsuwa balle kwanciyar hankali nidai irina wlh ko Yan gidanmu ne suka nuna basa son mutum muddin suna da hujja me Ƙarfi zan haƙura dashi saboda su dai dasu zan tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa idan babu goyon bayansu ina zan kai kukana?

Kina gani dai kina zaune Allah ya sake turo miki Ahmad a lokacin da abinda kike ƙulafuci yake ƙoƙar bari hannunki, idan kika sake kikayi wasa da damarki tana iya zama ta ƙarshe dan haka kiyi tunani kuma ki tattaro ki dawo School ki fuskanci karatunki semester ƙarshe muke karki bari kiyiwa kanki sawarwarar da zaki samu matsala a wannan lokacin tun wuri ki saki komai ki sake kama Allah ki kuma bar komi a hannunsa" abinda Badar ta gaya mata kenan da har yasa ta samu ƙwarin guiwar sake kiran Ahmad.
Chapter 60 · 0% Book details