← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 71

Sashe 49

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har akwai wani la'ananne bayan ke ne Binta? Ke ce saboda rashin tsoron Allah zaki ce kin shirya abu da zuciya ɗaya saboda Audu ya samu daidaito da Yayansa ko ki sake farraƙasu? Kinyi ne da niyyar ki tozarta Ahmad da matar da yake son aure tun gabanin ta shigo cikin mu kina so kuma ki lalata kyakykyawar Alaƙar da kikaga ta fara ginuwa tsakaninsa da Mahaifinsa ta hanyar saka Audu ya hanashi abinda yake so daga nan ki saƙa mumummunan zare a zuciyarsa ko? To ba zakiyi nasara ba da yardar Allah duk wani sharri da kike yi bazeyi tasiri ba, duk wani sharri da kika niyyaci ƙullawa akanki ze ƙare.

Kin bawa shekaru hamsin baya, ubangiki yayi miki Arziƙin tsahon rai ya baki dama da zaki gyara kurakurenki na baya amma saboda kin rigada kin auri duniya shaiɗan ya gama samun isahshen guri a zuciyarki baze barki ki hango gaba ki tubarwa Allah ki gyara laifukanki na baya ba a kullum zuciyarki sharri ce a ciki shi kike ƙoƙarin aiwatarwa. Ni naji daɗin daya dake su, kuma da kaina zan bashi goyin bayan duk mara tarbiyyar daya sake taɓa martabar Mahaifiyarsa idan ya samu dama ya tsinke masa harshe, abu guda ne bazan lamunta ba rashin Ɗa'a ga ubanku, kome yayi muku tilas yaci arziƙin yin silar zuwanku duniya, in har da gaske yakeyi ya shirya neman sasanci daku ku bashi dama domin ubangiji ma muna saɓa masa kuma mu nemi afuwarsa ya yafe mana wannan shaiɗaniyar ita ce silar faruwar komai a rayuwar Abdulwahabu ku taru ku taimaka masa ku kaita ƙasa ku bata kunya tunda dai ita babu gyara a rayuwarta tamkar dabbar Daji take kullum ƙara nausawa dawa takeyi".

Alƙali Yakubu be damu da cewar a Reception ɗin Asibiti suke ba kuma da mutane suna ta kai kawo a gurin duk anyi cirko cirko ana sauraronsa ya wanke Hajiya Binta tas da soson kaba haɗi da klin da hypo, yanda yake maganar murya a sama zaka tabbatar da cewar yau zuciyar Mazan ta harzuƙa dab kuma yake daya kwasa mata mari muddin tace zatayi inkari akan abinda yake faɗa. Hajiya kuwa hannaye biyu ta aza akai tana kuka tana cewa

"Daman na sani kaf dangin Audu babu wanda ya tsaneni ya tsani zuri'ata irinka Yakubu, ni kake kira La'ananniya? Nice shaiɗaniya? To bari naje seya tashi ya Zaɓa koni ko kai. Idan kai ya zaɓa daga nan gidanmu zanyi dan babu abinda ze sake zaunar dani a inda ba'a san mutunchina dana Zuri'ata ba idan kuma ya zaɓeni wlh se dai ya rabu dakai ya zareka daga Al'amuransa tsaf babu mu babu kai. Shikenan kawai saboda kai matarka bata da zuciyar haifar Yaya Maza seka ringa baƙin ciki da ɗaukakar da Allah ya bawa nawa dana haifa? Ai nasan duk ba komai bane baƙin cikinka saboda Audu nada Magada kuma Yayana nane akan Dukiyar Audu yau idan ya faɗi ya mutu ko sillin gashi baka da gado a cikin tarin Arziƙinsa. Takaicinka kuma yanda kullum Yaya nane a gaba sunfi duk sauran yayan da aka haifa a gidan Ƙashin Arziƙi".

Alƙali Yakubu yayi wata dariya, da alamu ya mance da inda suke shiyasa yake zaro maganganu duk yanda sukayi masa. Kallonta yayi sama da ƙasa yace mata
"Ina Alfahari da Yayan da ubangiji ya bani Mata, Namiji gudan daya bani ya fiye mini taron Yuyuyu irin wanda ke kike iƙirarin kin haifa. Ke har kinyi haihuwar da zaki bigi ƙirji kiyi Alfahari da ita Binta? Arziƙin yayan da yake cuɗanye da na sata da na ƙazantacciyar harƙallah? Bari kiji, wlh idan naso jirkita rayuwarki a cikin taƙaitattun sa'oi se kin bazama neman inda zaki boye a cikin ƙasar nan, kije ki fara gyara tarbiyyar Yayan da kike tinƙaho dasu kafin su zama abin Alfaharin, ina mai tabbatar miki Binta da raina ko na mutu akwai ranar da baƙin cikin waɗannan yayan da kika cuta kika gurbata musu rayuwa kika koya musu zalama da rashin wadatar zuci irin naki se sun saukar miki da Ciwon da in bakiyi wasa ba shi zeyi Ajalinki"

"Dan girman Allah Baba kayi haƙuri, ba anan ya kamata ayi maganar nan ba, Ahalinmu sanannu ne yanzu se kaji zanje yana tashi a Kafafen sada zumunta daga nan Allura seta tono garma" Dr Hassan daya matsa kusada Baba Alƙali ya faɗa yana kama hannunsa, shiyasan me Alƙalin yake magana akai.
PAGE 18
"Gara Allurar ta tono garmar ai ko wannan Mahaukaciyar da ubanku yake zaune da ita shekara da shekaru zata nutsu tasan Annabi ya faku" Alƙali Yakubu ya sake faɗa, Ahnad da Dr Hassan suka rufu suna bashi baki yayinda Binta take kuka tana kiran ita yake cewa mahaukaciya yau tilas Audu ya zaɓa ko ita ko shi.

"Hajiya Dan Allah kije waje kina damun marasa lafiya da suke kwance" Wata Nurse ta faɗawa Binta, a maimakon ta fita kamar yanda aka bata umarni seta doshi Amenity ward inda Alhaji Audu yake tana kururuwa da hayagagar zata taso shi ya zaɓa ko ita ko Yakubu securities suka mata burki, Alƙali yace
"Ku barta ta shiga, kai Hassan kira É—an uwanka kace ya maza yazo Asibitin nan ga wani Aikin Allah ya samu".

Abin dariya abin takaici sega Hajiya ta taka da gudu ta fice daga reception shi kansa Alƙali Yakubun dukda yanda ransa ya ke a ɓace seda ya dara suka wuce office ɗin Dr Hassan suka cigaba da tattaunawa. Hajiya kuwa Adaidaita ta tara ta koma gida, tana sauka Hajiya Rabi suna fita da Direba bayan ta gama haɗa abubuwan da Alhajin ze iya buƙata a Asibiti dan Momy cewa tayi ba zataje ba.

Kamar yanda Baba Alƙali ya bada umarni haka zuri'ar Audu Bechi maza suka sake taruwa a gidansa da daddare banda Naziru wanda yake can kwance gadon Asibiti da Zakariyyah shi an sallameshi bayan da aka bashi magunguna seya wuce gida ya kwanta dan ba wai ya gama komawa hayyacinsa bane ga bakinsa daya suntume an tabbatar dai babu komai a sannu kumburin ze saɓe. Kaca kaca Baba Alƙali yayi musu inda ya fi dora laifi akan Alhaji Babangida da yace shine babba.

"Yau idan Abdulwahabu ya faɗi ya mutu kaine madadinsa kuma duk lalacewarsa sunansa baze taɓa canzuwa daga ubanku ba kuma har a gaban Allah baku da wata hujja ta saɓa masa ko muzantashi, idan kuna riƙe da abinda yayi muku ko yayiwa iyayenku a baya tambayarku zanyi ta ina abinda ya faru ya rageku koya tauye rayuwarku? Shin luɗufin da ubangiji yayi muku a yanzu ba sakayyar wahalar da kuka sha a baya bace ba? Waye a tagayyare duk a cikin ku? Kafataninku kuna zaune lafiya kuna rayuwa cikin wadata me kuke nema? Ta ina rashin kulawar da ubanku ya nuna muku ta rage ku a yanzu?"

Kallonsa sukayi kowanne da magana a bakinsa, shi ɗin ba wani sakakan mutum ne da zasu iya mayarwa da martani shiyasa sukayi shiru. Ya gama musu faɗa kafin ya koma nasiha yana janyo musu Ayoyi da hadisai da suka tilasta musu yin biyayya ga mahaifansu ba wai ganin dama ba, Umarnin Allah da Manzonsa ne kuma kaucewa hakan babban laifine, yace suyi iyakar iyawarsu su rabu da mahaifinsu lafiya, baya musu fatan daga su harshi su tashi gaban Allah rataye da haƙƙoƙin juna da suka kasa saukewa a duniya. Ya roƙe su da suyiwa Mahaifinsu uzuri, ko babu komai albarkacin silar su duniya da yayi har suka taka matsayin da sukejin sun isa ja dashi a yanzu ya isa yasa su Yafe masa kura kuren da yayi musu.

"Kayi haƙuri Baba, amma wata shari'ar se a lahira, banajin zan iya manta abinda Alhaji yayiwa mahaifiyarmu, harta koma ga mahaliccinta da ciwonsa a zuciyarta. Duk sanda na ganshi hotunan yarintarku ne suke yawo a idanuna shi yasa na zaɓi dana zauna a Bechi nayo nesa dashi, idan ka tursasamun kace na yafe masa ko na faɗa iyakar fatar baki ne be zama lallai har zuciyata ina nufin abinda na furta ba" Alhaji Babannan ya faɗi kansa a ƙasa yana direwa Hussain ya cafe cikin ƙunar rai yace

"Mufa shegantamu yayi, ƙila da bamuyi kama dashi ba da har yanzu muna watangaririya a duniya baze karɓe mu ba".

Se Alƙali Yakubu ya rasa abin sake cewa kuma, a sanyaye yace
"Kuyi haƙuri, ku yafewa Ɗan uwana. Na sani yana cike da nadama da dana sanin wani bari na daga rayuwarsa ta baya kuma nasan a shirye yake daya gyara kuskurensa ku bashi damar haka muddin ya nema karkuce zakuyi masa bore".

Taro ya tashi jikin wasu ya sanyaya yayin da na wasu ya zama kamar Baba Alƙalin ya tado musu da tsohon tsumi ne. Hussain sarkin ɓarota cewa yayi
"Dama duk kaika haife mu bashi ba"
"Dani dashi duk abu guda ne, jarabawa ya gamu da ita wadda ba kowanne mutum yake iya tsallaketa ba itace ta rashin dace da Macen ƙwarai, shi yasa a koda yau nake muku nuni da ku ajiye komai idan aka zo gaɓar neman abokiyar zama ku dubi tarbiyya, Addini da nagarta tareda Asali ku bar duk wani ƙyale ƙyale da kwaɗayi domin gujewa maimaita irin kuskuren da mahaifinku ya tafka" Baba Alƙali ya sake tunasar dasu nan ne Faisal yaso ya gwada halin daya tsotso a Nono ya karkace zeyi fitsara yana cewa
"Auran mahaifiyarmu ne kuskuren da yayi kenan Baba ko wa?" Kafin ma Baban yace wani abu Yakubu ya bige masa baki har seda leɓensa ya fashe. Haka dai aka tashi taro kowa ya kama gabansa.

Kwanan Alhaji Audu uku a gadon Asibiti, jininsa ne ya hau ƙololuwa, yanda bincike ya tabbatar da ace faɗuwar da yayi a ƙasa ne tabbas babu abinda ze hanashi gamuwa da cutar shanyewar rabin jiki. A kwanaki ukun nan da yayi a gadon Asibiti idan kaji sautin muryarsa toh da Alƙali Yakubu yake magana se ko Dr da Hajiya Rabi dake jinyarsa wadda itama jefi jefi yake mata maganar. A ɗan taƙin yayi rama, tsufansa da jindaɗi yayiwa kwaskwarima jinyar kwana uku ta fito masa da ita. Kana kallonsa zaka fahimci cewar yana cikin wani yanayi mara daɗi, yawan shirunsa ya tabbatar sa tunani yakeyi wand kuma hakan yasa jikinsa yaƙiyin yanda ake so.
Chapter 49 · 0% Book details