Sashe 70
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
PAGE 25
"Ga Lesunan a Legas nan masu kyau dubu Hamsin dubu sittin duk dai Ƙure gayu ai sun isheta" Hajiyar ta faɗa, saboda takaici Turai bata iya bata amsa ba se Hajiya Zainab ce tace
"Haba Binta, a lefen Jafar za'a saka Lagos Lace? Ke kin taɓa ganin yarinyar da Ƙaramar sutura balle ki ringa lissafo mata Lashin dubu hamsin dubu sittin? To ai wlh ko Ahmad da yake shirin auro ɗiyar Talakawa Lefe Hajiya Aisha ta zage tana haɗawa na garari. A gurin *Maryam Hassan 07088361522* fa take siyan Laces matar nan kuma indai Lashi ake magana bata kawo na banza dama kin so gaskiya ne se kice a tafi gurinta a samo Lasuna na fita taro a ci da buguzun dan gasu nan kala kala iyakar kuɗinka iyakar shagalinka"
"Kuma suna kaiwa nawa?" Binta ta tambaya tana gyara zama, Hajiya Zainab tace "daga Ƙana dubu goma sha haka har zuwa ɗari da ɗoriya"
"To a samu yan Hamsin sittin ɗin a gurinta kawai a mayar da waɗannan wannan Almubazzaranci har ina ai se Allahya kamamu" Hajiyar ta sake faɗi. Data ishi Turai seta dena ma kai mata kayan idan an siya tun randa tace zata kwasa da kanta taje a musanyo tunda ita taƙi mayar da hankali.
"Ai gara a rage kuÉ—in ko Gona ce a siya masa tunda shi baya maida hankali gurin tara kadarori yanzu da zeyi aure ai yaci ya fara" Hajiyar ta faÉ—a, Turai tace
"Dake shi ba irinki bane ai da baki da buri sena ki tara baki ci ba baki bawa wasu sunci ba gara ki ajiye su yi diddiga a share".
Ta gefen Momy ma shirin biki suke da yan uwanta babu kama hannun yaro, lefe gangariya suke haɗawa suma Ahmad ya saki bakin Aljihu sosai suna abinda ya dace tun bayan daya tabbatar da Alhaji ze basu gidaje wanda seda akayi Ƙwarbai da Hajiya Binta Alƙali yazo har gida yayi mata cin mutinci kafinaka samu magana ta mutu. Tun bayan daya wa Alhaji Audun zancen ya bawa Ahamd gida lokacinma maganar Jay bata tashi ba bece masa komai ba, ana kai Kuɗin auran Jay Hajiyar ta shiga ta fita akan ai se Alhaji ya bashi gida dukda dai ba zama zeyi ba amma ya zama idan yazo yana da muhallin da ze sauka da iyalansa. Ta kwarkwanceshi tas kamar kuma yanda aka saba yabi ta tatan yace Naziru ya duba masa duk gidan da yayi ya shiga ya zauna labari na isa kunnen Alƙali ya wanko Ƙafa yazk har gida yayiwa Audun tatas yace
"Wato ana zatonkura tayi lafiya ashe kama kan bakanka na nuna banbanci a tsakanin Yayan cikinka ko Audu? Shi Ahmad Agolansa Aisha ta kawo maka da tunda mukayi maganar gidansa da kai baka ce komai ba se Ɗan da Binta ta haifa shi ne cikakken Ɗa a gurinka da zakayi masa abinda ya dace uba yayi? To ahir ɗinka, karka kuskura ka lalata tsaftatacciyar Alaƙar da ita kaɗai tayi saura a gidanka, karka janyo abinda ze kawo rabuwar kai tsakanin Ahmad da Jafar, karka yarda Ahmad ya fara tunanin ka faifita Jafar akansa domin muddin ya juya maka baya ba zakaji daɗi ba, duk wata sa'ida da salama da kake ji a cikin gidan nan yanzu dalilin yaron nan ne, shi yakw faɗi tashi gurin ganin gidanka ya saitu to wlh karka bari komai ya lalace".
"To ai uwarsa tace ya fara gini har ya kusa kammalawa sun siyi fili shida Ɗan uwan nasa ya fara gina nasa tunda shi wancan ba shiga ciki zeyi yanzu ba" Alhaji Audu ya faɗa tamkar duk beji kashedin da Alƙali yayi masa ba. Cikin takaici Alƙali yace
"Ai saboda shi ba me matacciyar zuciya bane kuma be dogara da kowa ba shiyasa ya tsaya da ƙafafunsa yake abubuwansa da guminsa, to a matsayinka na ubansa nace ka kira Ahmad ka bashi damar ya zaɓi duk gidan da yayi masa daga jerin gidajenkana Kano ko duk State ɗin da yayi ra'ayi se ya zaɓa sa'annan ka baiwa Jafar dama shima ya ɗauka dominAhmad na gaba dashi, umarni ne ba shawara ba idan kuma ban isa ba se in sani" yana gama faɗar haka ya tafi abinsa dake da sauran burbuɗin girma da mutunchinsa da yake gani se kuwa gashi yaji maganar.
Washe gari ya cewa Ahmad yaje bayan Sufi mart, da akwai gidaje da aka gina an gama komai abinda ya saura ba shida yawa, fentin katangar waje ne se saka kayan wuta wanda komai yana nan a ajiye daman. Gidaje ne gida biyu aka gina masa su, gini badai gini ba, duk sanda ya zagaya yaga gidan nan har wani nishaɗi yake ji a ransa se yaji kamar ya samo wata yar shawalwalar yarinya ya cike ta huɗu da ita ya samu inda ze ringa zuwa yana hutawa da kayaniyar duniya shine fa da Hajiya ta samu labari ta ringa tashin hankali tana tijata akan me za'a bawa Ahmad gida kuma wannan gidan da ita da yayanta duk bin Ƙwaƙwƙwafinsu basu san dasu ba ba'a isa ba ta ringa rashin mutunchi shi kuma Alhajin kamar wanda ta ɗaurewa baki ya gagara cewa komai be dai ce ya fasa kyautar ba kuma bece ba haka ba da abu yaƙi ci yaƙi cinyewa Hajiya Rabi ta kora Hajiya Balaraba a waya ta ce dan Allah ta cewa Alƙali yazo gidansu babu lafiya saboda Hajiyar shiga tayi har falon Momy tana zaginta tana cewa seta warware tsafin da taje tayi daya saka Alhaji yake ɗaukar abubuwansa masu Daraja ba tareda shawara da kowa ba ya mallakawa Ahmad.
Abinda be taɓa faruwa ba se gashi Momyn ta biye mata suna faɗi in faɗa Hajiya har tana cewa zata daketa tace da rabon idan batayi kwanan Kabari ba yau zatayi na Asibiti idan kuma tana musu ta gwada kai hannu jikinta. Muryoyinsu har Baban Compound ga Alhaji baya nan babu kuma wani takamaiman tsayayyen Namiji da ze iya tsawatar musu seda Alƙali yazo ya tarasu yaji ba'asi nan ya buɗrwa Binta wuta ya mata kaca kaca yace tunda Ake fifita Yayanta ana musu abubuwa waya taɓa ɗaga ido ya kalla se itace da hassada ta cikawa zuciya bata da burin sedai ita ko Yayanta su mori Audu shine yasa zatazo tana tada masifa akan dukiyar da ba ta ta ba
"Amma ubane sila" ta faɗi abinda ta saba duk sanda aka sako zancen dukiyar Audu. Alƙali yace
"Allah ne ya bashi ubanki ne sila amma da guminsa ya tattalata harta kai haka ko kuwa taki ya ringa zubawa abinda uban naki ya bashi yayi ta yaɗo yana ƙara yawa? Ke matsalata dake bama mutum ya tsaya yana magana dake ba ba fahimta zakiyi ba dan kin rigada kinci kai inyi miki ta yan zamani, to wlh ko ki bari hankali ya kwanta ko kuma ayi tashin hankalin na gaske. Yakubu, Zakariyyah da Naziru duk se sun fita daga gidajen da suke zaune tunda na Audu ne na sani sarai domin koda sakarai ne amma be manta ni Ɗan uwansa bane baya ɓoye mun komai daya ke ciki, su fita idan yaso ku jira idan ya mutu aka raba gado kowa seya amfana da rabonsa" ya mata fes ta fita tana kuka sannan ya juya kan Momy itama ya mata faɗan biyewa Hajiya.
"Ƙureni tayi, amma nayi nadama kuma bazan sake ba in sha Allahu" ta faɗa ya sallameta ya tafi shikenan magana ta mutu amma Binta bata haƙura ba har seda aka bawa Jafar gidan da yake jere dana Ahmad ɗin dan dama guda biyu ne dukda sun rigada sun zaɓar masa wani katafare a cikin Nasarawa GRA wanda ya shallake zaman Matashi me mace ɗaya dai Mansion ne danƙarere har an canza takardu shikenan Jay ya ci tudu biyu abinsa. Da taso mugunta se cewa tayi wai gidajen sun zarce ya basu kyautarsu sedai Aro shida Jafar ɗin duk wanda yake so ya mallaki nasa ya ringa biyansa a hankali dan baze yuwu ya ringa kwashe kadarorinsa yana kyauta dasu ba babu Adalci tunda beyiwa sauran Yayan ba yace mata Toh.
Kwanaki na tafiya sati na wucewa a kace duk abinda aka sakawa rana ze zo se gashi anci watanni uku lokaci yayi su Fatima sun kammala makaranta wanda kuma yayi daidai da wata uku kenan saura kwanakin auransu da aka saka. Zuwa sannan za'ace an samu cigaba sosai tsakaninta da Ahmad domin tayi surrender, takanyi iyakar yinta gurin kwatanta bashi kulawar da ya kamata ace ya samu a gurinta. Dukda cewar Ahmad ɗin bana da bane domin shima ya canza, ya rage rawar jiki akanta ya koyi kamewa da jan aji. Wannan lako lakon da maida kansa kamar wani sakarai da yakeyi mata ya dena, a yanzu idan ya kirata ta bashi uzurin tana wani abu ze barta amma fa baze sake kiranta ba har se idan ita da kanta ta kirashi sannan zasu cigaba da abinda suke kai. Sannan yawan zuwa gidansu akai akai da yakeyi a baya shima ya dena, koda ta dawo gida a yayi ƙoƙari jaye sau biyu cikin sati, tun abin baya damunta harya fara ci mata rai ga kwanakin aure suna matsowa tunani takeyi karfa ace lambo lambo Ahmad ya mata a baya, yanzu da ya tabbataemr da zata zama tasa shine ze fara fito mata da true color nasa idan ya zamana bayan sunyi aure yace ze rama irin cin kashin data masa tsayin shekaru uku ai ta shiga uku ta lalace bata hango inda zata tsoma kanta taji sanyi ba.
Har Badar tayiwa maganar akan sauyin Ahmad
"Badar tsoro nakeji kar ya ƙullaceni jira yakeyi daman ya samu damar da ze rama abinda na masa a baya"