← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 71

Sashe 51

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AHMAD
Yana tsugunne gaban Alhaji bayan daya gama ɓalla masa magungunansa yasha ya kuma gwada masa Bp da abinda Dr Hassan ya kawo ya kuma koya masa yanda ze ringa masa kullum da safe shi kuma da yamma yake zuwa ya sake dubashi, Sati guda kenan da dawowar Alhajin babu inda yake fita saboda jikin yaƙiyi masa yanda yake so, zuciyarsa a ƙuntace take, duk sanda yayi shiru abinda ya faru waccen ranar ne yake dawo masa dallah dallah. Wani irin abu yakeji a zuciyarsa da baze iya fasaltawa ba, Ɗansa na cikinsa a gabansa ya faɗi cewa mutuwarsa da rayuwarsa bata da banbanci a gurinsa shi kuwa wane irin bigire ya ɗora rayuwarsa akai? Anya idan ya mutu ze ringa samun kyawawan Addu'oi daga zuri'ar daya tara kuwa?

"Alhaji da akwai wani abun ne?" Ahmad ya sake tambayarsa karo na uku, yana ta masa magana amma ya zubawa guri guda ido yayi shiru. Yayi firgigit irin na wanda ya farga daga wani tunani kafin ya gyara zama yace
"Babu komai, fita zakayi ne?"
"Eh Alhaji, yau Jafar ze taso da daddare zasu sauka Abuja, ina tunanin na tafi can na jirashi da safe se mu juyo tare"

"Toh Madallah hakan yayi Allah ya kawo shi lafiya, nima dai inaga Abujar zan bika muje can na zauna na lokaci ko na samu jikina ya daidaita dan a nan mutane ba zasu barni da hayaniya na warke yanda ya kamata ba" Alhaji ya faÉ—a, Ahmad yayi murmushi, yasan da Hajjaju yake dan itace kamfanin hayaniya a gidan. Ba Alhaji ba hatta shi da yake yawan zama tare dashi idan tazo gajiya yake da sauraron maganarta kansa har ciwo yake É—auka inaga Alhajin da ba lafiya ce ta ishe shi ba?

"Ƙarfe nawa zaka tafi?" Ya sake tambayarsa. Ahmad ya duba Agogo yace
"Da jirgin shida kona tara nake tunani dan yanzu zanje gidan Baba Alƙali yace yana son ganina".

"Akan maganar neman auranka ne, kayi haƙuri da abinda ya faru ban shawarce ka tarko aka kafamun na shiga da kyakykyawar niyya bansan cewar wanda yayi shi da wata manufarsa ta daban ba. Mun tattauna da shi yace ze kiraka ku sake yin magana daga nan ze yanke rana da lokaci da za'aje masa neman Auran. Dama ina so naji zancen Muhalli ka tanada ne ko kuwa baka fara shirin komai ba game da auran?"

Ahmad yayi kasaƙe yana sauraron Alhaji, kalmar haƙuri da Alhaji ya fara da ita ta saka jikinsa sanyi laƙwas. Ya ringa tisa maganar Alhajin harya gama kafin ya fara tattaro amsar da ze bashi a zuciyarsa.

Shifa Fatiman nan sun kusa sati biyu rabon da suyi magana da ita tun ranar da Baffanta yace ya turo iyayensa be sake komawa ba haka be kirata ba itama bata neme shi ba ya kwanta jinya daga nan kuma wannan lamarin ya faru ya maida hankali ga jinyar Alhajinsu. Daman shi bashi ya tado da zancen aure yanzu ba Alhaji ne gashi yanzu har magana taja ana batun za'aje tambaya dukda cewar Mahaifinta ya bashi dama amma ai itama yana buƙatar amincewarta tunda dai da ita ze zauna idan bata sonsa baze samu farin cikin da yake fata a zamantakewarsu ba.

"Kayi shiru baka ce komai ba" Alhaji ya faÉ—a yana kallonsa, ya shafa kai yace
"Dama Jafar nake jira yazo tunda shima da tasa maganar se mu shawarta inda zamuyi gidan"

"Toh yayi, da akwai filaye dana siya nan bayan Sufi Mart, kuje kuga gurin idan yayi muku se ku zaɓi biyu a gina" Alhaji ya sake faɗa.
"Mungode, Allah ya ƙara girma" Ahmad yayi godiya kafin ya tashi ya fita. Gidan Baba Alƙali yaje, har number Baffansu Fatima Alƙalin ya karɓa a hannunsa da zummar ze kirashi ya basu lokacin da zasuje haka ya bashi dan bakinsa ya kasa buɗuwa ya fayyace wa kowa halin da suke ciki da Fatima. Idan yana da rabon auranta ya sani ze samu, idan ba rabonsa bace in sunje Mahaifinta ze musu bayanin komai, baya so ya faɗi har yanzu basu samu daidaito da ita ba saboda kar daga baya Allah yayi faruwar auransu ya zama yan uwansa su ƙi karɓarta yanda ya kamata.

Ya faɗawa Alƙali Yakubu filayen da Alhaji yace suje su gani in ya musu shida Jafar.
"Lallai kun gode, toh amma idan akace gini za'a tado zeja lokaci fa ta yuwu sama da shekara kafin ace anyi Auran nan dan nidai kunsan bana son wannan ginin burbur na zamani da akeyi wata shida ace ko ƙasa da haka kaga anyi gini har an tare ruwa be daki bulo da ciko sun zauna da kyau ba, in dai ba kuna so a saka auran da nisa ba shekara zuwa da rabi ba kamata yayi ace an nemi ginannen gida ko kuma cikin waɗanda aka fara ba'a kammala ba in ma tsarin ginin akwai abinda be muku ba kwaskwarima zatafi sauƙi akan ace a tada sabon gini".

Ahmad ya jijjiga kai dan yayi na'am da maganar tasa Alƙali Yakubu ya sake cewa
"Zan same shi zamuyi maganar" daga nan suka sake tattaunawa har bayan la'asar sannan ya koma gida. Ya zata da wasa Alhaji yake da yace zashi Abuja seda ya koma ya tarar dashi da Hajiya Rabi a shirye wai tare zasu tafi. Jirgin ƙarfe shida suka bi, A katafaren gidan sa na Abuja sukaji zango, gidane da bayyana tsaruwarsa ma ɓata lokacine. Bayan shi yana da gidaje da bazasu irgu ba a Abuja Manya da ƙanana banda Estate da Plazas da sauran Kadarori da iyalansa ma basu san da wanzuwar wasu daga ciki ba.

Manya Manyab Mansions ɗin da barin su da akeyi babu kowa ciki se masu aiki da suke kula da gidajen tasa yayi shawarar bayar dasu haya suka zama Masaukan Manyan baƙi tunda da komai na more rayuwa a ciki mutum sedai ya shiga yayi iyakar zamansa ya fita. Wannan gidan kaɗai ya ajiye yake sauka a jiki idan yaje Abujan, duk zalama da son duniyar Hajiya Binta ya rasa yanda akayi bata taɓa nuna sha'awar tana so ta koma Abujan da zama ba, a Shekarun baya dai Aisha ce ma ta ringa nacin daya raba musu gida, kodai ya maida Hajiyar wani guri daban ko su ya fitar dasu amma daya shawarta da Abokanansa akan hakan suka ce masa Aa, a girmansa da shekarunsa be kamata ace ya rarraba kan iyalansa ba, ai duniya ma se tace be isa da gidansa bane shi yasa ya kasa haɗe su a inuwa guda wannan ne ya daƙile maganar.

Ahmad yafi gane sauka a Hotel idan yazo Abuja amma yanzu saboda Alhaji tilas ya shiga É—aki ya kwanta yanajin duk babu daÉ—i, Sha biyu da rabi na dare su Jafar zasu sauka amma Alhaji yace yayi kwanciyarsa in ya dawo ya kwana a Aiport da safe ya taho gida babu wanda ze fita É—auko shi a daren nan baze yi masa musu ba ya kwanta yana ta jiran kiran Jay aikuwa ÆŠaya saura se gashi ya kirashi ta WhatsApp wai ya fito yana ina?

"Alhaji yace ka kwana a Aiport seda safe ka wuto gida" Ahmad ya bashi amsa yana dariya dan ya san abin seya zafafi Jafar aikuwa ya shaƙa yayi tam yace
"Amma fa ce mun kayi zaka zo ka jirani a Abuja yanzu kuma kana cewa Alhaji yace menene Allah Yah Ahmad ko"

"Toh ai ina Abujan, tare muka zo da Alhajin shima ze tareka"

"Ya samu sauƙi kenan? To nidai gaskiya ka saci hanya ka fito ina jiranka" cewar Jafar, Ahmad ya girgiza kai yace
"Kayi haƙuri ka zauna zuwa Asuba zan fito kasan yanayin gari yanzu yan one chance fa sun takura shiyasa naso na zauna nan na kama mana ɗaki amma da muka iso yace dole mu wuto gida tare". Saboda Haushi Jafar kashe waya yayi be cewa Ahmad komai ba ya ringa kiransa kuma yaƙi ya ɗauka duk ya damu ya kasa bacci.

Can jimawa seji yayi ana buɗe Get, ta window ya leƙa yaga Jafar na fitowa daga mota filin gidan tarwai yake da haske dan haka yana iya hango yanda ya cukule fuska. Masu gadi ne suka biyoshi da Back pack ɗinsa wadda daman ita kaɗai yake ruƙowa idan ze yau kuma ya ganshi da saitin Akwati me biyu da Kit, daga sama yake hangosu kuma dare ne amma a hakan yaga kyansu, bakinsa har kunne dan ya san wannan tsabar Masoyiyar da ake wa kowa rowarta ce, lallai Jafar da gaske yakeyi, a saninsa be taɓa ruƙowa wata Mace tsaraba.

Falon ƙasa ya sakko tarbar sa nan ya tarar da Alhaji da alama motsin buɗe ƙofa ne ya fito dashi shima. Jafar ya gaida Alhaji yana hararar Ahmad wanda ya gumtse dariyarsa jin Alhaji na cewa
"Ka karya mun dokar gida kana sane ko?" Shiru yayi Alhaji ya juya ya koma ciki se sannan Jafar ya farawa Ahmad mita suka wuce sama tare.

"Kai baka san dare bane wai ka bari da safe se kayi surutun naka mana" Ahmad ya faÉ—a yana zama a gefen gado. Jafar ya shiga cire kayan jikinsa wayarsa daya ajiye kusada Ahmad ya shiga ringing.
"Toh fa, ruhi na kira" Ahmad ya faɗa cikin sigar tsokana yana miƙa masa wayar ya karɓa yana wani tura masa baki kamar yaro. A speaker ya saka wayar, muryar Afeeyah dake cakuɗe da bacci ya ziyarci kunnuwansu a lokaci guda.

"Love, ka isa gida?" Ta faɗa, Jay ya wani langwaɓe kafin yace mata
"Yes Bae na iso gida, waifa Alhaji cewa yayi na kwana a Aiport ba za'azo a É—auke ba"

"Kai! haba dai" ta faÉ—a" tana ware ido, yace
"Wlh fa, but na dawo, na gaji da yawa wanka nake so nayi yanzu, I'm sorry for keeping you late na hana kiyi bacci"

"Haba mana, kana zaton zan iya bacci Alhalin kana hanya ban san ka isa gida ko Aa ba?"
Chapter 51 · 0% Book details