Sashe 16
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki babu ƙwari ta haɗe kujerun ta ɗauke farantin ruwan da be ko taɓa ba daman tasan ba sha zeyi ba Umma ce tace ta kai masa. Iyayen nata na yar hirarsu ta shiga. Seda ta ajiye kujerun a mazauninsu kafin ta isa gaban Baffa ta Zube kuɗin da Ahmad ya bata.
"Wannan fa?" Baffan ya tambayeta yana kallon kuÉ—in, a sanyaye tace
"Shi ya bani wai bezo da komai ba danaƙi karɓa shine ya ajiye akan Kujera ya tafi"
"Toh madallah amma idan ya sake dawowa ki gaya masa na hana karki Ƙara karɓan kuɗinsa" Baffan ya faɗa ta amsa da
"Toh Baffa" kafin ta miƙe tsaye zata wuvmce yace mata
"Kwashe kije dasu ai ke aka bawa"
"Ni babu abinda zanyi dasu Baffa" ta bashi amsa tana juyawa.
"Zo nan Mamana, me yake damunki? Ko wani abu yayi miki?" Baffan ya sake dakatar da ita saboda lura da yanayinta sam ba daidai take ba, murmushi ta ƙaƙalo tace
"Babu komai Baffa kaina ne yake sarawa zanje na ƙarasa shirya kayana sena kwanta"
"Toh Allah ya sawwaƙa ki samu magani kisha kafin ki kwanta ɗin idan be dena ba da safe se kije Asibiti, sannu ko" Baffa ya faɗa cikin tausayawa. Seda ta shige sannan Umma ta gaya masa abinda take zaton shine sikar tsumewar Fatima. Yayi murmushi yace
"Ina ruwan Mamana, wato kunya ce duk ta dabaibayeta, to ya za'ayi abu ya rigada ya faru ta yuwu ma ya manta idan kuma ya ganota ya samu abin tsokanarta ai" tana jiyo Baffan daga ɗakiz harta hasaso Ahmad ya dawo da zancen ai lumewa zatayi a ƙasa kawai ta huta.
Harta bacci ya fara fizgarta wayarta ta tayar da ita, Data ta a buɗe yake dan haka taga sunan Ahmad Bechi a truecaller, kamar ba zata ɗauka ba se kuma zuciyarta ta kwabeta kan wulaƙanci babu kyau.
"Allah yasa ban tasheki a barci ba" ya faÉ—a bayan data amsa wayar, cikin muryar da bacci ya fara tasiri a cikinta tace masa
"Aa".
Ahmad ya gyara kwanciya akan Gadonsa, tunda ya shiga gida suke waya da Jafar daya kai masa ƙarar Hajiya wai ta kirashi akan seya Rantawa Faisal Kuɗi ze fara harkar Crypto kuɗaɗe kuma ba Ƙanana ba take cewa ya bashi ita lissafin Ribar da Faisal ɗin yace mata kawai za'a samu takeyi bata hango Risk da yake tattare da sabgar ba kuma wai rance bama kyauta take nufi harda bashi zuwa lokacin da ze turo kuɗin shine ya kawowa Ahmad ƙararta ita da Faisal ɗin se kace ze iya masa wani abu akai be samu sun gama maganar ba se yanzun yana ta Allah Allah kar tayi bacci ba suyi magana ba.
"Kara zakiyi mun amma muryarki ta fallasaki, kiyi baccinki toh in Allah ya kaimu da safe sena kiraki ƙarfe nawa kike tashi daga bacci?"
"Ko yaushe ma" ta bashi amsa cikin ƙaguwa, ya fiya tambaya take ayyanawa a ranta. Ahmad naso suyi hira dan so yake ta sake dashi da sauri amma kuma bayaso ya shiga haƙƙinta dan haka ya mata sallama akan ze kira da safe dukda bata gaya masa sanda take tashi ba ya kuma jaddada mata kan tayi saving number sa.
Tsaki tayi bayan ta kashe wayar baccin data fara ya gudu se ta shige WhatsApp tana duba saƙonni kafin baccin ya dawo. Dm na samari gasu nan babu Adadi unread messages ɗinta sunfi dari duk ta tsallake ta wuce kan number Badar dataga ta mata magana da ita suke hira daman baccin ya kwasheta.
"Al'amin yace inya kiraki wayar bata shiga, a WhatsApp kuma baki buÉ—e chat É—insa me yasa?"
"Blocking É—insa nayi" ta bawa Badar É—in amsa ganin tana online. Tana turawa kuwa ta buÉ—e ta shiga yi mata voice.
"Kina kuwa yanda ya gigice Afee zuwansa fa gidan nan biyu yau wlh se in kira masa ke a wayata na kira kuma bata shigo ba lokacin wai me ya haÉ—aku ne? Dan Allah ki tausayawa guy É—in nan wlh Al'amin yana sonki sosai fa" cewar Badar.
"Uhm duk ya gama haukansa can ya nemi daidai shi a gaba, wai ni Badar shikenan Namiji baze so ni saboda Allah ba se dan wata buƙata ta daban? Ki faɗamun tsakaninki da Allah ko da akwai wani abu da nakeyi mara kyau da yake Attracting yan iskan Maza zuwa gareni? Ni kenan duk wanda zece yana sona seya nemeni da lakata me nakeyi daya sa suke mun kallon Mara kamun kai Badar?" Fatiman ta mayar mata da Voice note muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka saboda zafin abinda take ji a ranta.
Allah ya mata farin jini bana wasa ba, bata taɓa fita ta dawo gida Namiji be tsaidata ko an biyota gida ba amma duk wanda ta kula take ganin kamar zasu samu daidaito da tafiya ta fara nisa se ya kauce layi ya shigo mata da wani zancen na daban. Tun abin baya damunta har yazo ya fara bata tsoro ta yaya za'ayi ace duk wanda yazo yana sonta seya nemi ya taɓa jikinta se kace ita kaɗaice Mace a duniya ko kuwa duk suma sauran Matan haka ake musu??
"Na gaya miki Afee wannan matsalar fa bake kaɗai ta shafa ba, abinda yasa kuke mun kallon Masifaffiya kenan na kasa tsaida saurayi ko ɗaya saboda ni bana iya shiru, mutum na zuwar mun da shirme a take nake tsigaleshi gara nayita zama single dina har Allah ya kawomun Mijin Aure na na gaske, ke kuma duk wanda yazo miki da suffar Salihai seki saki jiki se mutum ya nuna miki true color kizo kina ciwon rai kenan shima Al'amin ɗin shegene da gemunsa kamar Na Allah ai da kin gayamun da wuri wlh da daya zo ɗazun sena wulaƙantashi dan iska shege me ci da buguzun da fuskar Salihai" Badar ta hau spark daga nan suka cigaba da tattauna abinda yake damunsu ya kuma zama ruwan dare a zamanin nan. Samari sun zama abinda suka zama kawai, sun maida mata tamkar wasu Takalma da zasu ce se sun gwada sun samu wanda yayi musu daidai kafin su siya a irin haka waɗansu da ƙadda take hawa da wanda suke kasa jure jarabawar ubangiji yayi musu suga kamar idan Saurayin ya gudu ba zasu samu wani ba se su bayar da kai bori ua hau wanda daman samarin yan latsine da sun samu abinda ya kawosu su fece shikenan se a shiga lahaula da Innalillahi Allah ya rufa asiri.
Soyayya ta ƙullu tsakanin Fatima da Ahmad ko ace farashin soyayya nata hauhawa a zuciyar Ahmad domin abinda yakeyi yafi kama da One sided Love sedai ya kasa fahimtar hakan. Kwana uku tsakanin zuwansa na farko ya sake komawa daga nan kuma ya mayar da zuwan nasa sau biyu a sati bayan nan kuma kullum a ƙalla ze kirata waya sau uku yaji ya take, kulawa da tattali duk irin wadda yasan zata farauto masa da zuciyarta yana mata amma ko a jikinta shan ƙamshin nan ma ƙaruwa yake ko a waya idan suna magana yanayin da take amsawa tamkar bata so amsarta bata wuce Eh ko Aa shi zeyita zuba surutu inya gaji yace tana jinsa tace Wh bata da abin cewa ne shi yasa tayi shiru hakan kuma yake jurewa baya fushi yana cigaba da lallaɓata.
A cikin haka suka koma makaranta wanda taji daɗin hakan sosai saboda ko babu komai zata huta da zuwan da yakeyi sannan zata samu uzurin da zata ringa gujewa wayarsa yanzu dan a gida Idan ya kira Umma data fahimci Ahmad ɗin be samu karɓuwa gurin Fatiman ba ita take takura mata tayi ta mata faɗa idan ta bar wayar tana ƙara ko yazo ta tsaya nuƙu nuƙu taƙi fita. Ta kance mata wulaƙanci babu kyau, bata san abinda Allah ya tsara ba kuma ita bataga makusarsa ba da zatace beyi mata ba dan a zuwansa na biyu ya shiga har ciki ya gaidata itama data ganshi ta fahimci nutsuwa da Kamalar da Malam yace yana da ita. Yaro ne amma Allah ya hore masa nutsuwa da dattako daya zarce shekarunsa kuma duk wasu iyaye na kwarai tabbas zasuyiwa Yarsu sha'awar samun Miji me kulawa tamkar Ahmad ɗin.
Bayan sun koma makaranta haka zeyita kiranta ba zata ɗaga ba, tun su Badar basu sanda Ahmad ba dan bata gaya musu ba har suka gane dalili wata raba ya kirata tana sallah Badar ta amsa wayar suka gaisa ya kama sunanta shikenan hira ta ɓarke, Fatima bata so ba domin muddin Ahmad yayiwa Badar tasan ta shiga uku, takura kam ko ruwa me daɗi ba zata barta tasha a dalilin Ahmad ba shiyasa take ta ɓoyewa gashi yanzu Badar ɗin ta ganoshi.
"Dukda banga guy É—in nan ba tun daga voice É—insa nasan ya haÉ—u, wato Afee kin iya catching Big Boys matsalar duk yan iska ne in disguise Allah yasa dai wannan na Allah ne dan wlh daga magana a waya harya burgeni yana da nutsuwa ga kirki, waye shi? A ina kuka haÉ—u" Badar ta tambayeta bayan ta gama waya da Ahmad ta bashi uzurin abinci zataci shi kuma ya shaida mata ze fita Jafar ne yazo ze É—auko shi daga Airport.
"Ya samu hutu ne shine yazo Gaisuwar Rasuwar Brigadier General Baballiya Bechi, ƙanin Alhajinmu sa sukayi Hatsarin jirgi last two weeks ai kinji labari ko?" Abinda ya gaya mata da duk ya saka taji kunya kenan. Sanda akayi rasuwar ta gani a SM, kuma anyita surutun a gari kan set up ne akayi musu ba wai Accident bane ba ance akwai wani sirri da suke shirin bankaɗawa na wata badaƙala data faru shine kafin nan masu laifin suka kawar dasu, tunda taga Bechin a ranta ta kawo yana da alaƙa da Ahmad kuma ta gani ya saka a Status harya tura mata cewar an masa rasuwa kunyar data ji yanzu irin gaisuwar da tayi masa ta
"Allah ya jiƙan rai" kawai tace, babu wani sympathy babu nuna concern na cewar Kawunsa ne na kusa ya rasu tana ganin shiyasa yanzu yake gaya mata Jafar yazo dan tasan Mutuwar me muhimmanci ce a gurinsu tunda har na wata ƙasar ya taho ita kuwa ba wanda ta gayawa a gidansu ma balle ko a waya su masa gaisuwa.