← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 71

Sashe 18

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Billahillazi karka ɗauka kaci banza baka isa ka tozartani a banza Ƙawayena su tafi suna gulmata ba sannan na ƙyakela muje cikin"

"Ai wanan unnecessary drama taki ce zata saka a tafi ana gulmar taki, sabida Allah meye abin tashin hankali a nan? Daman banda ɗaurawa kai ke kika saba taroshi ko yaya? Wlh Yaya Binta bakya gudun abin magana da abin sakawa kai ciwon kai a duniyar nan, duk inda zaman lafiya yake kin ɓauɗe masa" Munira ƙanwarta da batayi niyyar magana ba sedai ganin Abin na Yayartata na neman zarce misali yasa ta fito tana mata maganar. Fuuuu Hajiya ta shige ɗaki Jafar ya kalli Ahmad yace
"I'm sorry Yah Ahmad ni na jawo maka"
"Kaidai jeka kafin Hajiya ta canza maka wannan fuskar taka babu ruwana bari naje wani guri bazan jima ba zan dawo" Ahmad ya bashi amsa yana juyawa ya fice daga gidan.

Dukda yayi ƙoƙarin danne ɓacin ransa Amma Jafar ɗin seda ya fahimta, ya sani dole kalaman Hajiyar su sosa masa rai shi kansa beji daɗi ba amma yasan idanyace wani abu baya ga kalmar lallaɓi da banbaki a yanzu ƙara tunzurata zeyi tayi musu zazzafar Tijara a gaban mutane.

Jiki a sanyaye ya bi bayan Hajiyar, Yaƙe kawai ya ringayi yana gaisawa da tarin matan dake zaune falon Hajiyar, ya so ya gane wasu amma ya manta sunayensu wasu kuma sababbin fuskane a wajensa dan Hajiya badai tara
ƙawaye ba ga Yayayensu da suka kwaso sekace Biki keyi yanzu da tana nufin waɗannan jama'ar zata kwasa su tafi Ɗaukoshi daga Airport ɗin?.

Abinda ya sake ɓata masa rai yanda Yayan Ƙawayen Hajiyar suketa wani abu kamar masu shafar Jinnu, se ɗaukar hotuna suke da video ana sakoshi a ciki wasu ma yaga kamar Live sukeyi a IG suna faɗin gasu a gidansu Jay sunzo taron shi. Ƙasa Ƙasa yake jan tsaki yana durƙushe tsakiyar Mata kowacce da kalar soki burutsun hirar da take jefa masa da tambayoyi kamar sun aikeshi ya dawo, ba Hajiyar ba ba Ƙawayen nata ba babu wadda tayi tunanin a gajiye yake ko yana da buƙatar yaje ya huta seda Hajiya Turai ta fito daga Kitchen taje tana shirya abincin da za'a rabawa Jama'ar da Hajiya ta tara abin Allah arziƙin Jay yau ba Ƙaramin Better tasa aka shirya a gidan ba harda Rago aka gasa.

"Kana tsugunne Jafar ai se Ƙafafunka su gaji tashi kaje ka huta kaida ka shawo tafiya" Turai ta faɗa, ya saci kallon Hajjaju da ta zauna ta haɗe fuska tana juya ƙafa da gani lissafa yanda zataci ubansu daga shi Har Ahmad ɗin daya rusa mata shiri takeyi.

"Tashi kaje mana kake kallona da wasu idonka irin na Ubanku" ta faɗa tana zaburo masa. Ya miƙe yana shafa kai, daidai nan Faisal Bechi ya shigo yana kwalawa Hajiya kira yana cewa
"An fa gama saita komai har Photographer ya iso Allah dai yasa ma a barku ku shiga Airport É—in irin wannan gayya se kace masu taro Governor.." Se kuma ya dakata saboda ganin Jay a gabansa, ya buga tsalle kamar yaro ya É—aneshi yana ihu.

"Get off me my friend, kai baka zaka girma da shirme ba ko?" Jafar ya faÉ—a yana tureshi. Bakin Faisal kamar ze yage yace
"Welcome brother, ni na sani sedai ba Jafar Bechi ba wlh se kayi disappointing Hajiya amma fa ka kwafsa kai kasan irin Grand welcome da aka shirya maka kuwa yau?"

"Matsa na wuce" Jafar ya tureshi jin yana neman ɓallo masa sabon ruwa Faisal yabi bayansa yana kyalkyala dariyar mugunta yana gaya masa irin shirin da Hajiya tayi. Ɗakin Momy ya wuce, tana zaune kan kujera da waya a hannunta tana dannawa Khadija, Aslamiyya da Maimuna duk suna falon suna kallon Tv duk Drama da aka kwasa suna zaune basu fita ba balle su tanka Jafar ya shiga da sallama suka amsa masa a tare kowannensu fuskarsa na faɗaɗa da murmushi.

Gaban Momy ya wuce ya zauna dab da Ƙafafunta yana kallon Step sisters ɗinsa fuska ɗauke da murmushi.
"Barka da dawowa Sheikh Jafar" Momy ta faÉ—a cikin raha.
"Mun same ku lafiya Momy?" Ya mayar mata ta amsa da
"Lafiya lau, ya ka baro abokanan sana'arka da gurinsu Yaya Muhammadu?"
"Duk suna lafiya suna gaisheku"
"Madallah sannu da zuwa" ta sake faɗa kafin ta miƙe ta shiga kitchen, bata jima ba ta fito me aikinta Amira na biye da ita da babban Try ta ajiye a gaban Jay kafin ta gaishe shi ta koma.

Ya miƙawa Nu'ayma Babyn Khadija hannu ta tafi kamar zata faɗi dan tafiyar tata batayi kwari ba, Khadija, Maimuna da Aslamiyya suka haɗa baki gurin yi masa sannu da zuwa ya amsa musu kafin yace da Khadija
"Yaya Khadija ya yara? Ina Alhaji?"
"Yana Islamiyya se sun tashi idan an É—auko shi zasu biyo ta nan mu wuce".

"Kasha ruwa, ga mutuminka nan Coconut Juice" Momy ta faɗa ganin yana ta wasa da Nu'ayma be taɓa abinda aka ajiye masa ba.
"Yah Jay sha kaji dan Allah ni nayi fa" Maimuna ta faɗa cikin zumuɗi ta sauka ƙasan ta tsiyaya masa a Cup ta bude kwanon da aka zuba kayan maƙwalashe tana cewa
"Har small chops É—in ma ni nayi fa"
"Kice kin zama Chef babu labari? Me ya samu wayarki na dena ganinki Online?" Ya faɗa yana karɓan Cup ɗin da ta zuba masa Lemon, seta kalli Momy, Momyn tace

"Kya kalleni? Ki gaya masa abinda kikayi Ahmad ya kwace wayar mana"
"Ai base ta faÉ—a ba ma Momy tunda kikace Yah Ahmad ne nasan tayi abu mara kyau ne, Any Juice É—in yayi daÉ—i sosai, and this too" ya nuna Chocolate cake dake hannunsa.

"Thank u, shine Yah Aslamiyya yace ba zakaci ba wai beyi daÉ—i ba"
"Zanci mana har Token zan baki ma for the good job".
Gwalo tayiwa Aslamiyya Momy da Khadija na musu dariya FaÉ—an sako da sako sukeyi kamar kaji.

A cikin zuciyar Jafar kuwa abinda ya sabaji a duk sanda yake cikin ɗakin Yauma yaki, ina ma ace shima ɗan ɗakin ne? Duk sanda ya zo Nigeria irin wannan tarbat yake samu a gurin Momy. Ita zatayi masa maraba ta bashi abinci Hajiya kuwa se Hayagaga ta cikashi da tambayoyi da ƙorafe ƙorafe, ruwa seya tambaya kafin zata tuna ya kamata a bashi babu ruwanta da duba daga wani guri me nisa yazo yana da buƙatar hutu da kulawa Aa matsalolinta kawai sune a gabanta.

"Bari naje nayi sallah an kira La'asar" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy tace
"Tam, zasu Miƙo maka abinci Gas ne yayi mana tsiya amma an gama ƙarashene kawai"
"Nagode, Yah Khadija kafin ki tafi kimun magana" daga haka ya fice daga falon. Seda ya leƙa Hajiya Rabi, a mutunce suka gaisa se sannan Yaranta suka samu sukunin yi masa sannu da zuwa suma, ya kama hannun Zayyad suka fita tare zuwa masallaci.

"Idan kina Ƙaunar Allah Binta ki zauna, mene haka? Waike bakya kunyar idon mutane ki ringa abu kamar wata zararriya?" Turai ta faɗa tana tare Ƙofar uwar ɗakin Hajiya dake shirin fita ta raba hali, Jafar na fita tacewa Aidah, Jikarta Babbar Yar Nazira ta bishi taga inda zashi ilai kuwa tace mata ya shiga ɗakin Momy ta zabura zata fita Turai ta hanata shine ta turata ɗaki suketa tata burza tun dazun lokacin daya ɗauka a ɗakin be fito ba shi ya saka Harzuƙata, ta window taga fitowarsa da shigarsa Gurin Hajiya Rabi shine ta zabura zata tareshi ta tsigaleshi taji tsakanin Aisha da Rabi ko da akwai wadda ta tayata ɗaukar cikinsa ko ɗawainiyar rainonsa ne bata sani ba dayafi mutuntasu da girmama su akanta?

"Turai kirabu dani, ni ban iya haɗiye baƙin ciki ba sena Amayar dashi, ke ni fita ki sallami kowa ma ta wuce gidanta zaman me kuma za'a mun tunda wanda ake taron danshi ya watsa mun ƙasa a ido, sallami kowa dan Allah na samu sararin huce fushina yanda ya kamata" Hajiya ta faɗa a fusace tana fuzgewa daga riƙon da Turai tayi mata.

"Kamar ya in sallamesu ni na tara miki su ko yaya? Sannan Ai kya jira su gana cin abinci ko ba'ace su tafi ba kowa kama gabanta zatayi tunda ba yinin Biki bane balle ace se rana ta faɗi idan kuma zaki fita ki korasu daman ba baƙon abu bane a gurinki ai siyar da hali" Turai ta mayar mata itama a fusace kowa ta kalli Bango tana hura hanci.

Jafar kuwa daƙyar ya ƙwato ya fito daga Masallaci, ɗakinsu shida Ahmad ya wuce. Ya saki murmushi ganin yanda aka canza tsarin ɗakin daga zuwansa na last year ya canza musu Gado da Labulaye da Carpet harda penti aka sake sabo ga kyawawan Food warmers da Jug a ajiye yasan aiken Momy ne. Seda ya sakawa Ƙofa Key kafin shiga wanka. A cikin kayan Ahmad ya nemi marasa nauyi Three quater Kaki da Armless shirt ya saka ya dirarwa Abincin.

Tuwo ne da Miyar Agusi, taji Wasulla na ruwa dana ƙasa wato Momyn kamar tana shiga zuciyarsa duk zuwa seta tareshi da abinda yake da burin ci idan yazo gida. Sosai yaci tuwon ya sha Juice ta ture kayan gefe ya kishingiɗa jikin gado yana jin jikinsa ya cika da yawa, shida abinci me nauyi kamar tuwo se yazo Nigeria shina baya ci da yawa saboda Diet ɗinsa. Wayar Ahmad ya kira,
"Ina Get" Ahmad ya faɗa bayan daya amsa wayar dan idan be ɗaga ba Jay kira zeyi tayi baze barshi ba. Ragowar Abincin daya rage Ahmad yaci suna hira Salim ma ya shigo se Lawal da Mu'allim da suka shiga suka gaida shi suma suka kuma gaya masa mutane na jiransa a ƙofar gida.

"Ka ce musu na fita" Inji Jafar. Ahnad na siÉ—e hannu yace
"Sun fika sanin whereabouts ɗinka ai, garama ka tashi kaje kafin Alhaji ya dawo ya tarar da taro a Ƙofar gidansa ya dirar maka daga dawowa"
Chapter 18 · 0% Book details