← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 71

Sashe 17

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hoton Ahmad kawai ta nemo ta miƙawa Badar data addabeta da waya, cikin Mamaki take kallonsa tace
"Ahmad Bechi? Wlh Afee kinyi Miji kinsan kirkin mutumin nan kuwa?"

"A ina kika sanshi?" Ta tambaya tana tsare Badar ɗin da ido wani abu da bata taɓa tsammatar zata jishi akan Ahmad ɗinba ya taso mata wato kishi.

"A IG mana, ai ina following É—insa" b
Badar ta bata amsa. Seta tsume fuska tace

"Shine har kika san kirkinsa daga ganinsa a IG kuma"

"Ai mutumin kirki baya ɓuya, kuma idan da kinsan yanda mutane suke yabonsa da bakiyi mamakin dan nace yana da kirki ba, kin san yanda yake taimako kuwa? Ke dai Allah yana sonki Afee, kinga ya canza miki da abinda yafi duk shegun da kika rasa Alkhairi wlh ki gode masa"

"Allah ya saka mu a danshinku Afee, ke kam Allah ya taimakeki da jinin manyan mutane, Bechi Family fa?" Ilham roommate É—insu ta faÉ—a nan suka shiga hirar caaa caaa kowa na tofa Albarkacin bakinsa.

Ahmad
Ƙarfe biyu ya fita ɗakko Jay wanda suka samu delay na jirgi daga Abuja zuwa Kano, tun daren jiya ya sauka daga London, ya biyo jirgin Abj to Kn na sha biyu da rabi na rana basu taso ba se biyu da wasu mintina uku saura suka sauka a Kanon. Beyi mamaki daya kira Yah Ahmad yace masa already yana cikin Airport ɗin ba. Be taɓa barin sa yayi jira muddin yana gari shi ze zo ya ɗaukeshi kafin Jirginsu yayi Landing Ahmad ya isa Airport wani sa'ilin har Abujan yake zuwa ya taro shi su taho Kanon Tare.

Cikin tsananin murna da É—okin ganin juna suka rungume juna kowanne yana jin soyayyar É—an uwansa na sake ratsa Jini da jijiyarsa.
"Kullum ƙara girma kakeyi da fresh, look at you, idan muka jera za'ace kai Yayana ne na uku ma" Ahmad ya faɗa cikin zolaya yana kallon Jay daya ɓata fuska irin na sangartattun yara wai yace masa tsoho. Kuma da gaskiyar Ahmad ɗin, A tsaye Jay yake gansansan kamar ya haɗa jini da samudawa koda yake jinin Binta da Audu fa kowanne ba baya bane a garin jiki.

Suna tafe suna hira gwanin sha'awa har suka isa gida. Hajiya na tsaka da shiri domin wannan karon ta rantse gayya zasuyi suje taro Jay ɗin se Kano gaba ɗaya ta san da ya dawo. Idan zezo gida babu wanda yake sani, ko a jirgi badda kama yakeyi saboda ya tsani irin taro da hargowar da mutane sukeyi duk sanda suka ganshi a cika guri ayita ihu ana ɗaukar hotuna dashi ayi blocking masu uzurirrika shiyasa kusan shekara biyar kenan ya canza salon zuwansa Nigeria, hatta da manager sa na nan wrong schedule yake bashi dan shi yake sanarwar Jay ɗin na tafe ya haɗa masa mutane shiyasa ya zaɓi boye zuwansa, Ahmad kaɗai yake gayawa se idan ya dawo a kwashi tsiya da tsiyataku da Hajjaju dan idan zezo Yau ce mata yakeyi se Jibi sedai ta ganshi kamar dirar kirsimeti.

Zuwansa na ƙarshe waccen shekarar na buɗe Shagon Ahmad daman bata san da zancen ba ganinsa kawai tayi, ta zabga tijara ta kuma ce Alhaji yayi mata tsakani da Ahmad ya fita a sabgar Ɗanta, ta yaya za'ayi idan ba mugunta ba ya saka ya baro gurin sana'arsa dan yayi Asarar miliyoyin da ake biyansa? Ta kuma ce zancen Ahmad shi kaɗai ya ɗauko shi daga iyafot ya kau, duk in ze sake zuwa zuga za'ayi dangi da Abokanan arziƙi aje a taroshi jama'a su san yana da gata ba wai ace kamar shi sananne a duniya idan zezo gida ya ringa shigowa kamar Ɗan fashin da ake fako a kama.

Shine dalilin daya saka ta haɗo Jama'a kenan dangi da Abokanan Arziƙi, jira takeyi ayi La'asar su ɗebi motoci a tafi Iyafot ɗauko Jafaru, yau ɗin har kwalliya taci, ta saka Sabuwar Atamfarta Super Sheraton, kusan shekarar ta uku a ɗinke, da siyanta kuma zatayi biyar ko Shida ta sallah ce da Alhaji yayi musu sauran da yuwuwa sun dade da bayar da tasu amma ita se Yau Allah ya nufa zata saka shima da fari wani Lace ta saka, sabone amma ajiya tasa ɗinkin ya fita a yayi, tun ana style me Umbrella da hannu me ɗorin Kafaɗa, ga wata uwar boader Lace da aka tattara a wuya da bakin Hannu, da ace Zallar Lace ɗin aka ɗinka mata ko ya shekara goma zata saka abinta dan babbane, Design ɗin Lace kuma baya tsufa sedai ɗinkin jikinsa ya nuna shekarunsa.

Turai ce ta kalleta sanda ta fito ala dole ta ƙure gayu ga Sarƙar Zinare irin design ɗin Saudiyya damɓasheshiya ta sauka har kan ƙirjinta, jan hannunta Turai tayi da sauri suka koma ɗaki tana cewa

"Haba Binta, yanzu saboda Allah da wannan shigar zaki tafi tarar Jafar É—in se kace wadda ta fito daga riga? So kike ki ja masa abin magana a É—auke ku hoto a yaÉ—a a a duniya duk suturunki keko ki rasa wanda zaki saka se wannan Matsiyacin Lace É—in dan girman Allah ina zaki kai ubannin suturun da kike dasu ne?"

Hajiya ta yamutsa fuska tana kallon Turai tace
"Karki gaya mun mara daÉ—i mana, me Leshi na yayi? Ina a gurinki na siyeshi ko a lokacin ai ya haura É—ari balle yanzu indai ba cutata kikayi ba kuma"

"Shekararki nawa da siyansa? Ni wlh har na manta da nayi irin Leshin nan bana zaton wadda na bawa ma har yanzu yana nan be zama tsumma ba, yanzu dai duk ba wannan surutun ba su Hajiya Rafi'a da Hajiya Zuwaira duk suna falo yanzu suka iso se kin raina kanki idan kikaga kwalliyarsu, yayayenau kansu da sukazo dasu bakiga yanda suka sha kwalliya ba se ke da ake taron saboda ke ce zaki fita a haka kamar mara kan gado dan Allah wuce ki sauya Kaya, ki nemo na mutunchi wannan rakwacam ɗin sarƙarma kiyiwa girman Allah ki tattarosu muje gurin Alhaji Mansur a narkasu, a maida miki ƙirar zamani".

Badan taso ba shine ta canza da Atamfar dukda itan ma Turai tace ba tayi ba, gafa kayan nan a jibge amma ta bari ta zaɓa mata ma tace Aa, da babu gara babu daɗi Atamfar Ɗinkin doguwar rigane an mata Bead work a wuya da bakin hannun, Sarƙar ce dai tace ba zata cire ba, tilas Turai ta barta, a neman mayafi kuma aka tafka abin kunya dan Hajiya dai bata da Mayafin fita Taro, ƙarshe se a gurin Momy Turai taje da kanta ta Aro mata Jaka da Takalmi kuma aka samu a gurin Hajiya ƙarama.

"Wlh Binta ki canza hali, wannan tsumulmula har ina? Kuɗi kina dasu kamar su kasheki amma ace ko jikinki ba zaki iya kashewa ba wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu tsabagen zubar da ƙima Gyalen da zaki saka ki fita kunyar Ɗanki ma baki dashi se an aro a gurin kishiya wannan abin takaici har ina?"

Turai ta dasa mata mita, Binta dake kiciniyar Rataya Jaka a hammata ta buÉ—e baki zata bata amsa suka jiyo ihun Yara ana oyoyo Uncle Jay, Hajiya ta zabura tayi waje dan ta tabbatar da abinda take jiyowa, Jafar É—in da ta gama haÉ—a jama'a da motoci zasu tafi tarowa ko kuwa wani daban suke nufi????
PAGE 7
"Jafaru, ni uwarka ka yaudara wannan karon ma kace mun biyar na yamma jirginku ze sauka seda na gama tattara jama'a zamu tafi taronka mu nunawa Duniya gatanka shine zaka tozartani Ko La'asar bata rufa ba ka diro a gidannan wato ka sanar da Amadu shi da yake ƙanin ubanka yaje ya dauko ka ko?" Hajiya ta faɗa tana zarewa Jafar idanu. Sakin Yaran Yayyensa da suka ruƙunƙumeshi suna masa oyoyo yayi ya nufeta fuska ɗauke da murmushi cikin shagwaɓa yana cewa

"Haba Hajiyata, dawowana lafiya ai shine komai yanzu, maimakon ki tareni da warm hug se ki farayi mun faÉ—a kuma?"

"Ka matsoni sena kwasheka da mari wlh, kai kuma me kama da dido dido, sau nawa zan faɗa maka ka fita daga sabgar Jafaru? Shin wai Aisha ta haifamin shine ko Yaya? Nace ka fita daga sabgata data Yayana Amadu amma kaƙi kaji shin ana dolene? To kaji da kunnenka duk bala'i da tuggunku sedai ya ƙare muku amma babu tsafi ko Asirin da zeci Jafaru wlh balle har kuga ya samu nakasu. Ɗaukaka da cigaba a rayuwa yanzu ya fara ganinta duk nasan shirinku da liƙe masan da kakeyi ba wai ban sani ba Asirin da kayi ka lashe masa zuciya ma ina kan karyashi kuma idan na juyo takanka ba zaka ji da daɗi ba"

"Haba Binta wannan wane irin abune kikeyi dan girman Allah? Meye amfanin wannan faɗe faɗen da kikeyi? Jafar dai gashi ya dawo lafiya me kuma kike da buƙata?" Turai ta katse Hajiya daga Hauragiyar da takeyi se kuwa ta zabga mata harara tace
"Babu ruwanki Turai, idan ba zaki tayani ba to kija bakinki kiyi shiru"

"Allah ya sawwaƙa miki, Sannu da zuwa kaji Jafar yi wucewarka can Ɗakinku, idan kuma zaka fara shiga ku gaisa da iyayenka da suka zo tarbarka toh, sannu da hanya" Hajiya Turai da bataji kashedo ba ta faɗa tana nunawa Jafar Palour Binta wanda jama'ar ciki sukayi shiru suna saurar abinda yake faruwa a wajen, Mutan gidan kuwa daman sun san za'a rina dan haka abin bezo musu a bazata ba. Jafar ya kalli Hajiya dake tsaye kamar sojanniya se numfarfashi take tana dannanwa Ahmad da yayi ƙasa da kansa harara, cikin sigar rarrashi Jafar ɗin yace mata

"Please mana Hajiyata, ki saki fuskarki, change of schedule muka samu na flight and na manta ban sanar miki ba. Believe me Yah Ahmad ma be sani ba seda na sauka Kano. You Know i Miss you so much shiyasa ba zan iya jira ba kuzo da yawa ba shiyasa kawai na kirasa nace yazo ya ɗauko ni amma ba laifinsa bane Allah nike da laifi amma kiyi haƙuri bari na koma Abuja kawai gobe sena dawo kizo keda jama'arki ku taroni" ya faɗa bayan daya isa dab da ita. Hararar da takewa Ahmad ta mayar kansa kafin tace
Chapter 17 · 0% Book details