Sashe 12
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
PAGE 5
MARMARA GIDAN MALAM HAFIZU BAKANIKE
Jiki a sanyaye kamar kazar da ruwan sama ya buga ta shiga gidan bakinta ɗauke da ƙaramar sallama. Anty Sauda na tsaye bakin fanfo tana wanke hannu bayan ta gama jajjefa ɗan waken da Ummansu tayi abincin rana, giftawar Fatiman kawai ta gani ta shige ɗaki dan bataji sallamar ba, bata daɗe a ɗakin hannunta riƙeda Kwandon kayan wankanta se zani da ledar pad har sannan tana sanye da Hijab ɗin daya mata kyau matuƙa ta raɓe Anty Saudan zata shige banɗaki
"Ina kika samo Hijabi kuma?" Antyn ta tambayeta ta shige ba tareda ta bata amsa ba. Taci Sa'a ruwan fanfo yazo ta tara bokiti dukda bata son wanka da ruwan sanyi kwata kwata komai zafi dole haka ta watsa dan babu lokacin da zata tsaya ɗumama ruwa yanzu. Bayan ta gama ta wanke rigar ta da kayan cikin da suka ɓaci, faɗin irin yanayin da take ciki kan wannan abin kunya daya sameta ɓata lokacine, tunani takeyi wa ze gyara kujerar da ta ɓata? Da kansa ze goge ko car wash ze kai? Ita kam yau taga ta kanta Period ya kwafsa mata wai ma Allah yasa ba idon sani bane babu lallai su sake haɗuwa yanzu da be bata Hijabin nan ba ya zatayi?
"Ko ina ya samu Hijab ma oho" ta faÉ—a a fili tana shanya kayanta akan igiya. Anty Saude tayi rashe rashe cikin barander ga Zobo me sanyin gaske gabanta tana sha tana kallon Fatiman ta sake shigewa É—aki, seda ta kimtsa kanta sosai kafin ta fito har sannan ranta babu daÉ—i ta zauna kan Tabarmar kusada Anty Sauda.
"Wai wane isakanci ne yake damunki AFEEYA ina ta miki magana kina mun banza, wani sabon raini ne yake neman shiga tsakaninmu ko yaya?" Anty Saudan ta faÉ—a a É—an fusace. Idanun Fatima sukayi rau rau har muryarta na rawa tace
"Toni me zance miki? Duk bake kika jawo mun ba ina tace miki mu taho gida kikaƙi har seda kikaja na ɓata jikina shima na ɓata masa mota"
Anty Sauda ta buÉ—e baki da mamaki tana kallonta kafin tace
"Lallai yarinyar nan, duba nakeyi da zansan matsakarki ko kuwa É—inke miki baki akayi da bazaki gayamin abinda kike ciki ba? Yanzu staining kika masa a mota? Innalillahi Afeeya kin tafka abin kunya staining a motar saurayi haÉ—uwar farko gaskiya abu beyi daÉ—i ba ka kujerunsa farare tab" bata gama rufe baki ba se ga hawaye sha sun fara zubowa Afeeya kamar an kunna fanfo abin ma se ya bawa Anty Sauda Dariya ta cigaba da Tirata tana faÉ—in ta kwafsa
"To waya baki Hijabi kuma?" Ta tambayeta cikin kukan Afeeya tace
"Shiya bani mana, harda cewa wai meyasa tun a can gurin ban tambaya an bani pad ba?"
Anty Sauda cikin jimami kamar gaske tace
"Ai gaskiya ne, kinga ranar Gayu ai gobe ma idan kina Al'ada ki sake saka kaya masu haske ki fita babu Hijabi, ni wannan daya bakin ma É—inkin yamun kyau, idan ya kiraki ki tambayarmun shi inda ya siya".
Kuka AFEEYA ta dage tanayi kamar yarinya tsa tsani raini yanzu ga ƙarshen raini can wani Namiji yaga jinin Al'adarta ita kuma Anty Sauda harda cewa wai ya kirata, ai wlh koya kira blocking zatayi babu ma zancen ko gaisawa suyi balle ya tuno abin kunyar da tayi a motarsa. Sallamar Ummansu ce tasa ta tsagaita kukan da takeyi, bata ma san bata gidan ba se yanzun data shigo. Umman ta zare Hijabin jikinta ta saƙale jikin igiya tana kallom Afeeyan tace
"Uwannan lafiya? Meya faru kike kuka? Ina kuma kika tsaya Yayarki ta rigaki shigowa gida?" Se maganar Umman ta sake tunzurata kukan ya ƙara ƙarfi, ta gaya mata bata son wannan sunan wai Uwannan amma Umman taƙi bari kamar da gayya ma take kiranta haka dukda Baffa da kansa yace ta dena amma taƙiji.
Anty Sauda ce tayi mata bayani, Umman ta haÉ—iye dariyarta tace
"To kuma shine abin kuka? Lalura ce shima ai ya sani. Kima godewa Allah daya sa yana da abinda ze baki ki suturta kanki, kina kukan dan shi kaɗai ya gani to da kuma kin keto Titi da abin ashe ba zaki sake fita ko ƙofar gida ba saboda kunyar yan unguwa" maganar Umman Gaskiya ce wannna tasa ta haɗiye kukanta ta zubo abimci tana ci tana sauraron hirar Umman da Anty Sauda. Har dare ta kasa sakewa duk motsi seta tuno Ahmad da yanda ya ringa kallon gurin data ɓata Allah kaɗai yasan tunanin da yakeyi a ransa.
Da Mijin Anty Sauda yazo zasu tafi haka suka sake kinkimar kayan da suka siyo É—azun aka kai Mota, Afeeya nata mitar mema yasa ta kawo su gidan da se ta barsu acan su mata Delivery kai tsaye ba seta wahalar da mutane anyi É—auka biyu ba. Har Anty Saudan ta zauna a motar ta yafito Afeeya tana cewa
"Ya kiraki kuwa?"
"Wa?" Ta tambayeta kamar bata gane wanda take nufi ba. Anty Sauda ta lafta mata harara tace
"Saura ki masa wulaƙancin da kika saba yiwa samari"
"Ai daman na gaya miki beyi mun ba" amsar data bata tana tura baki ta koma gida. Dagaske take har ranta Ahmad beyi mata ba a matsayin saurayi. Bashida makusa a halitta domin kyakykyawane daidai misali amma magana ta domin Allah yayi mata ƙarami shi ba wani tsayi can ba kuma bashida jiki sannan da ganinsa sanyi ƙalau ne se yanda mace tayi dashi kuma ya fiya Fara'a gaba ɗaya be kama hanyar Mijin da take buri ba.
AHMAD
Yar matsala suka samu ta rikicewar lissafi a Shago wannan ya ɗauke masa hankali haryasa be samu damar kiran Fatima ba har akayi sati guda da haɗuwarsu badan ya manta da ita ba ko bata ransa Aa sedan yana da buƙatar nutsuwa gurin warware abinda yake a gabansa. Seda ya samu komai ya koma kan layi kafin ya dawo lissafin Fatiman har yayi niyyar kiranta sedai kamar Almara ya nemi number da yayi saving da hannunsa sama ko ƙasa ya rasa. Yayi mamakin yanda akayi ta goge amma ya godewa Allah daya sa yayi basirar bincikar gidansu tun waccen ranar.
Da Magriba ranar Juma'a bayan ya dawo daga sallah ya niyyatu zuwa gidan idan yaso ya sakw karɓo number dan dagaske yakeyi yaga fure kuma bazeyi saken da zata kufce masa ba. Fuskar daya gani a gurin Yayarta ta tabbatar masa Fatiman a kasuwa take, ma'ana wani bai rigashi ba ko ba'ayi mata baiko da wani ba domin yanayinsu basuyi kama da wanda zasuyi kwashe kwashen samari ba.
Tsaf ya shirya cikin Manyan kaya ya kafa hula shida kansa yasan yayi kyau ya ringa murmushi yan fesa turare yana hasaso fuskarta ya zata karɓeshi? Da tace beyi mata ba dagaske takeyi har ranta ko kuwa dai irin abin nan na yammata ne?
Wayarsa dake ajiye ce ta ɗauki ƙara ya janyota ya duba Momy cw take kira dan haka ya ɗaga da sauri yana sallama.
"Yaya Ahmad wai ni ina saƙona daka karɓomun kai baka ce mun gasu ba nima na sha'afa fin sati se yanzu da nake so nayi amfani dasu na tuna" Momy ta faɗa bayan data amsa sallamarsa. Tana cewa saƙo ya gane wanda take nufi, Hijaban daya karɓo mata ne a gidan *UMMU-MAHEER ME HIJABS ƊIN YAN GAYU* wanda harya ɗaukarwa Fatima a ciki.
"Yanzu zan kawo miki Momy na mantane wlh" ya faɗa da sauri kuma ya ɗauki muƙullin motarsa ya fita daga ɗakin suka kusa yin karo da Lawan, Autan Hajiya Binta a Maza ya taho hannu biyu riƙe da Tab yana buga game kamar wani yaro ƙarami yayi diri diri shi bai kauce ba be kuma matsa bayaba. Haushi ya ƙume Ahmad, ga sauri yanayi a fusace yace masa
"Ni zan kauce maka ka wuce kenan?"
Lawan ɗin yayi muimui da baki kafin ya raɓe gefe, Ahmad yayi ƙwafa ya wuceshi dan yana da abinyi yanzu amma tabbas se koma ta kansa wannan rainin da yaron ya ɗauko baze zuba Ido ya barshi ya tashi a haka ba kamar sauran Yaran gidan idanba haka fa Zayyad da yake ƙarami a gidan duka shima haka ze taso da Tarbiyyarsu, Matan tasu rashin kunyar da sauƙi da wuya suyiwa Mazan sedai a tsakaninsu amma su waɗannan da suke tashi yanzu shida Mu'allim jin kansu suke daidai dai da uban kowa daman Salim Da Faisal sun rigada sun ƙafura tuntuni.
Ledar Hijaban ya É—auka, guda goma ne ya bawa Fatima É—aya ya wuce ciki a tsakar gida suka ci karo da Hajiya idanuwanta akan Ledar hannunsa tamkar zata huda tashiga taga abinda yake ciki haka take kallon Ledar ko gaisuwar da yake mata bataji ba balle ta amsa dan haka yayi gaba shina ya kusa shiga É—akin Momy ya jiyota tana cewa
"Au Amadu, kana kallona ka wuce ko gaisheni ba zakayi ba"
"Ya fa gaisheki Hajiya kinata kallon Ledar hannunsa" Sarah ta bata amsa aiko ta kai mata duka ta kauce nan ta shiga sababi tana cewa
"Dan uwarki dake nake? Ko kin koma Amadu bansani ba shegiya me shegen shishshigi a abinda ba'a sakata ba kuma da idon ubanki kika ga ina kallon kayan hannunsa?"
Hajiya Rabi na daga cikin falonta inda ta idar da sallah tana lazumi hayagagar Hajiyar ya na neman ya raba mata hankali dan ta jikin window ta take tsaye, rabon ayi yasa ta leƙa kaɗan tacewa Hajiyar tayi haƙuri tayi shiru nan ta juya kanta ta dirar mata cin mutunchi da gorin da bata gajiya dayi mata.
"Itama Rabi banda neman magana waya kaita tanka mata? Yau Allah ya taimakemu tun safe kunnuwanmu shiru rabon dai se an mana na dare" Momy ta faɗa sanda Ahmad ya dire ledar hannunsa a ƙasa ta jata gabanta tana fito da kayan ciki. Hijabai tara ta gani, ta fara ciresu daga ledojinsu tana duba yadin, fuskarta a washe tace
"Kaji laushin yadin nan ga kyau a ido waye zece ba ÆŠan Egypt É—in bane?"