← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 71

Sashe 5

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah Hajiya kiyi ƙasa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faɗa,
Yakubu daya haɗo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a manaƙisar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an ɗebi kuɗin ba ya zata lissafi kawai suka ƙara masa. Kwankwaɗe shayinsa yayi ya taso yana cewa

"A fitar dani ko wallahi na fasa ƙwai"
"Dan uwarka ka yanka Kaza ƙarewar fasa ƙwai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haɗe seka gane baka da wayo wlh"

Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace
"Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ƙishin ƙishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa".

Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ƙulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruɗe se kokawa take da waya

"Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta miƙa masa wayarta tana cewa
"Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ƙullata".

"Aikuwa ba zaki same shi a waya yanzu ba dan suna da wasa ƙarfe sha daya, lah lokaci yayima an fara ina tsaye bari kawai na kalla a nan" Yakubun ya bata amsa bayan ya dire mata wayarta a gabanta ya matsa gaban Cinema Tv bango guda wadda Jafar ya sakawa Hajiyar saboda tace wai bata ganinsa dakyau a tsohuwar tata.

Tv na daidaita kuwa kamar me daukar hoton wasan Kwallon da ake yasani ya haskowa Hajiya Binta fuskar JAFAR BECHI tarr kamar ze fito ta cikin gilashin Tv. Zabgegen saurayi irin ƙirar Yayan AUDU BECHI, dogone sosai jikinsa nada ɗan kauri dukda ba za'a sakashi a layin masu ƙiba ba amma a murɗe yake koda gani ba se an gaya maka yana motsa jiki dakyau ba. Fatarsa nada haske sosai dukda ba fari bane sedai hutu da zaman Turai ya bashi wata kala me kyau kuma me wuyar samu a cikin mutane, ba wani shahararren kyan fuska yake dashi ba Aa daidai Misali ne irin na Maza gayu da yanayin muhalli da wankan da yakeyi ne yasa har Mata suke iya sakashi a jerin Maza masu kyau wanda ake gwarama kai akansu , ga duk wanda yasan Hajiya Binta Musamman a zamanin ƙuruciya kai tsaye ze tabbatar da JAFAR din jininta ne dan zubin fuskarsu daya idan ka cire Idanun Gidan BECHI daya samu se labbansa wanda Binta tace irin na Alhajinsune, duk tana jika dai da itan yake kama kenan.

Jafar ɗin na tsaye a coner ya take kwallo da ƙafarsa ta hagu idanunsa kuma na kan saitin inda yake so ya bugata. JC ce a jikinsa Jaa me ratsin fari ta club din Arsenal wadda ke dauke da Number 7, a bayan rigar an Rubuta JAAY, wani murmushi yake saki daidai sanda Referee ya busa whistle gaba ɗaya yan ƙwallo suka shiga tara tara kowa na jiran ya jefo ta inda yake ya kama, baya yaja kaɗan ya buga ball ɗin daga inda yake ta ringa kurɗaɗawa ta tsakakanin ƙafafuwan yan wasan aka rasa wanda ze taketa har seda ta dangana da cikin raga shikansa Goalkeeper kamar an riƙe masa hannu da ƙafafuwa ya kasa tareta har ta shige, ihun yan kallo na cikin Tv tarefa na ZAKARIYYA BECHI da YAKUBU BECHI ya cika falon, Hajiyavkanta da take cikin ruɗu fuska a ɗaure bata san sanda ta saki dariya ba tana cewa

"Ai na sani, sedai idan ba Jafaru na ba be taba kama kwallo ya saka ba tareda ya kaita raga ba, kai Allah dai yacigaba da tuntuɗo maka Albarka ɗan nan Allah ya cigaba da tsole idon maƙiya" Ɗa guda tilo kenan cikin rayayyu tara da take dasu wanda take ɗaga hannu ta roƙar masa nasara a gurin Allah ta kumayi masa addu'ar fatan nasara tareda saka Albarka, yana kuma ganin hasken hakan domin Uwa duk yanda take Uwa ce kuma tasirin harshenta nada girma.

Jafar ɗin me shekaru Ashirin da bakwai a duniya yanzu ya kai matsayi mai girma a duniyar kwallon ƙafa. Matashin Dan wasa ne da ake ji dashi a faɗin duniya wanda kowanne Club suke zawarcinsa, idan ka cire Messi da Ronaldo JAAY shi yake take musu baya a duniyar kwallon ƙafa a yanzun. Ubangiji ya hore masa baiwar sarrafa kwallo, duk rintsi duk tsanani idan JAAY ya karbi kwallo seya kaita ga inda ya hara kafin ya haƙura, juriyarsa da Nacinsa da kuma ƙoƙarinsa na haɗakan Yan Team ɗinsa Abokanan taka ledars shiyake ƙara masa ƙima a idon duniya domin kowa ya shaida wannan jajircewar tasa ce ƙashin bayan cigaba da Nasarorin da duk wani club dayake taka leda a ciki yake samu.

Cikin farin ciki suka haÉ—u suna kallon Wasan, harda Hafsatu da Sarah dake bacci ihun su Yakubun ya taso su ko karyawa basuyi ba suka haÉ—u aka cigana da kallon.

BECHI FARM
Kamar yanda Alhaji Audu yace Ahmad ya sameshi a gidan gona haka ce ta kasance, Alhajin ya riga Ahmad isa saboda baƙi da yayi ze gana dasu acan wanda shine musabbabin daya saka yace Ahmad ya tarar dashi a can ɗin, sanda ya isa Alhajin na tsakiyar tattaunawa dan haka yayiwa kansa masauki a daya daga cikin falukan da suke gidan gonar idan kaga tsaruwarsu zaka ɗauka a cikin gida kake ba wai gidan gona ba. Yana zaune cikin zullumi rungume da takaddun tsarin abinda yake so ya gudanar, zuciyarsa fal wasi wasin yarda ko akasin haka daga gurin Alhaji, idan Alhajin be yarda da buƙatarsa ba a ina ze samu gurin da ze aiwatar da aikinsa tamkar wanda yake nema a gurin Alhajin?

Gajiya yayi da zama da tunani ya tashi ya fita yana zagaya gidan gonar, sashen tsuntsaye ya tafi, acan ya shantake yana kallon Halittun ubangiji, tsuntsaye gasu nan kala kalanda Alhajin yake kiwo danginsu Dawisu, Aku, Kanari da sauran tsuntsaye masu tashi kala kala a keji nan su ga kuma tattabaru nan irin ƙasashe daban daban Jikinsu kaɗai abin sha'awa. Kukan tsuntsayen da surutun masu kula da gurin ne ya ɗebe masa kewa har besan lokacin daya ɗauka ba seda wani daga cikin yaran Alhajin yayi kiransa.

Masaukin daya tarar da Alhajin yafi kowanne haɗuwa a gidan gonar, yana zaune kan Luntsumemiyar Rolar chair two sitter irin zaman da yayi da suturar da take jikinsa kamar wani basarake seya cike kujerar gaba daya kwarjininsa ya cika falon. Tamkar beran da ruwa yayiwa duka haka Ahmad ya raɓe daga gefen kujera yana gaida Alhaji.

"Ka tashi ka zauna a sama, meye haka kakeyi kamar wanda yazo Maula?" Alhajin ya faɗa cikin muryarsa me razana Maza. Ahmad ya sake yin ƙasa dakai cikin tsantsar ladabi yace
"Aa Alhaji nan ma yayi, be kamata kana zaune akan kujera nima na zauna ba"

"Umarni na baka ba shawara ba" ya sake faÉ—a a dake, wani sashi na zuciyarsa kuma yana tsinkewa, Ladabin Ahmad daban ne kaf a cikin Yayansa 28 yayi zarra wanda yake take masa baya kuma Jafar ne wanda zama da Ahmad É—in ya washsheshi shima ya rabautu da kyawawan É—abi'u.

Kamar wanda ya zauna akan wuta haka Ahmad ya ɗosana mazaunansa akan kujerar jininsa yana sake tsinkewa, falon yayi shiru, motsin ƙofa da aka buɗe ya saka Ahmad ɗin zabura kamar mara gaskiya ganin Kuku ne ya shigo yana tura abinda ake ɗoro abinci akai yasa ya maida kansa ya sauke Ajiyar zuciya a hankali. A nan tsakiyar falon kan Ledar da Kukun ya shimfiɗa ya jera abincin daya shigo dasu. Seda ya gama ajiye komai daya kamata kafin ya juya ya fita bayan ya sanarwa da Alhaji komai ya kammala.

Alhajin ya sauka ya zauna a ƙasan ya tokare hannunsa ɗaya da Tum Tum ya shiga serving kansa abincin Ahmad yayi sauri ya sauka ya karɓa. Ganin duk ire iren abincin da Alhajin yake ci yanzun ne dangin Alkama dasu Acca se kayan ganye sakamakon Sugar daya gamu dashi ya saka masa komai madaidaici yanda ze iya ci kafin ya koma ze zauna Kukun ya sake shigowa da madaidaicin Tray ya ajiye a gaban Ahmad ɗin ya sake fita.

"Ga irin naku nan" Alhaji dake cin Funkaso da akayi da garin Alkama da wata miyar tantaƙwashi ga shayin Goruba yana kurɓa ya faɗa.
Ya buɗe baki da niyyar yace ya ƙoshi amma kallon da Alhajin yayi masa ya saka ya buɗe abincin. Soyayyar jollof din Basmati ce se kaza guda gasashshiya da kuma coslow. Favorite ɗin Ahmad kenan shinkafa balle ga Kaza mutuniyarsa a gefe daman be karya ba ya fito dan haka tuni ya manta da surukutarsa da Alhajin ya hau zuba loka. Seda suka ƙoshi ƙat, Kuku ya sake zuwa ya kwashe komai ya dire musu kayan marmari da tataccen ruwan Inibi me sanyi, Alhaji nata satar kallon Ahmad kamar yanda shima yake satar kallon Alhajin.

Dukda wata magana bata shiga tsakaninsu ba har suka gama cin abincin amma duk su biyun yanayin ya musu daɗi domin wannan shine karo na farko da suka taɓa haɗa muhallin cin abinci tun tasowar Ahmad ɗin sedai su hangeshi sunaci da Hajiya tareda Yayanta, sanda suna yara idan ta kira Jafar yazo suci abinci suka tafi tareda Ahmad ɗin haka zatayi ta zaginsa ta koreshi shi kuma Jafar ya saka kuka yabi bayansa wata rana haka da duka zata tisa Jafar ɗin seya zauna dukda bazeci abincin ba domin basa raba kwano da Ahmad da suka fara girma kuma da lokacin cin abincin wanda sukafiyi da dare ya kusa ze ja Ahmad su bar gidan ma doke ta haƙura ta barshi kuma duk abinda akeyi Alhajin be taɓa magana akai ba, ashe haka cin abinci tareda Mahaifi yake da daɗi? Ya raya a ransa.
Chapter 5 · 0% Book details