← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 71

Sashe 10

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya raya, ya kawo mata ta gari babu damuwa guda nawa kake so kuma kamar na wane kuÉ—i?"

"Haba Anty Sauda jiranki fa nakeyi shine zaki shiga wata sabgar kuma da bakizo ba waye ze zaɓar masa kayan? Duk ma'aikatan gurin nan ke kaɗai ya gani da zece ki tayashi ɗaukar kaya ko kuwai neman gurin zama?" Ƙanwar tata ta faɗa cikin bacin rai. A fili Ahmad yace
"Ikon Allah" yana kallonta yayarta me suna Sauda ta lafta mata harara kafin tace
"Wai ni dole na miki da ki biyoni ne ko yaya? Idan ba zaki iya jira nagama abinda nake ba FATIMA ga hanya yi tafiyarki mana"

Majid da se lokacin ya lura da Ahmad ne a gurin ya saki abinda yakeyi da sauri ya isa cikin ladabi yana cewa
"Ranka ya daɗe wani abun kake buƙata?"
"No, cigaba da aikinka kawai babu matsala ga Anty zata tayani zaɓa"
ya sallameshi.

Bata tafin ba se ƙara lafewa bango da tafi tana cika tana batsewa kamar fulawar dataji yeast. Anty Sauda kuwa ta cigaba da ɗaga kaya tana zaɓar nata dana Ahmad da yace kala biyar yake so.
"Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" yayi mata godiya, Majid ya karɓi kayan yayi masa gaba dasu shi kuma ya kalli Fatima dake dabda fashewa yace
"Ki zauna kar ƙafarki ta gaji bari a kawo miki ruwa me sanyi kisha".

Sanin idan ta buɗe baki ba zata bashi amsa me daɗi ba tasa tayi ƙwafa kawai ta sake tsumewa. Seda Antynta ta gama jan ranta iyaka kafin aka tattara mata kayan da ta siya aka kai gurin biyan kuɗi lokacin tuni Ahmad ya biya nasa an kai masa mota yana ƙarasa wani abu kafin ya fita, ko tsinke ya ɗauka a gurin seya saka kuɗin balle ma wani yayi tunanin zuwa yace ze ɗibi bati kamar yanda Salim yaso ya fara masa sanda yake zuwa seya kwaso Abokanansa su ɗebi abu ayita rigima dasu a gun biyan kuɗi yace shiya basu ba zasu biya ba securities su hanasu fita, seda Ahmad ɗin yayi masa kaca kaca a gurin sannan ya samu salama dalilin kuma daya saka Salim ɗin ya bar aiki a gun wanda daman Momy tayi masa dole.

Suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa, Fatima nata zabga Mita Anty Sauda kuwa ta mata shiru kamar bada ita take ba, iyakar zafin ranar dake ratsasu ya isa sunfi Awa guda cikin sanyin Raɓa kuma sanda suka shiga rana bata take kamar haka ba seda suka fito suka ganta ƙwal da alamun hadari ze iya haɗuwa zuwa jimawa. Wani abin takaici kamar an hana masu Adaidaitan hanyarsu zuwa duk wanda suka tare da sunce MARMARA zece ba nan yayi ba, wanda zasuje kuma da mutum a ciki su kuma ga kaya drop ma yaƙi samuwa kamar wanda akawa baki.

Suna nan tsaye kamar Fatima zata fashe ga rana ga babban abinda ya dameta ita, yanayin da take ji a jikinta ta tabbatar period ze iya zuwar mata a kowanne lokaci dukda gobe take saka ran zuwansa shiyasa ma bata fito a shirye ba amma suna shiga gurin nan taji jikinta ya fara sauyawa irin yanayin da takeji idan jinin ze zuba dan bata wani laulayi ko ciwon Mara sedai taji jikinta na mata wani Yamm kamar tana jin sanyi dataji haka tasan any moment ze iya zubowa to wannan yanayin takeji shiyasa duk ta takura tun shigarsu gurin Miskilanci kuma ya hana tayiwa Anty Saudan bayani se baƙin rai takeyi tana tsaki.

Wata dalleliyar mota Ford fara tas ta giftasu se gata ta dawo da baya a hankali ta tsaya a gabansu, Ahmad ya sauke glass, fuskarsa me É—auke da murmushin yan Aljanna ta bayyana ya kalli Fatima suka haÉ—a ido yanda tayi seda ya kusa bushewa da dariya amma ya kanne ya maida dubansa ga Anty Sauda.

"Bari na rage muku hanya to nima cikin garin na nufa" Ya faÉ—a bayan da Anty Sauda ta masa bayanin sun rasa abin hawan hanyarsu ne, Fatima ta zabura tace
"Yi tafiyarka zamu samu" Anty Sauda ta galla mata harara ƙasa ƙasa tace
"Duk saboda ke yake wannan abun kiyi dagaske harya fusata ya tafi"

"Allah ya kiyaye ni beyi mun ba" abinda Fatiman ta faɗa ya isa kuma har kunnen Ahmad dake ƙoƙarin saka musu kaya a booth securities biyu da suka hangoshi suka taho da sauri suna tayashi. Murmushi yayi da jin furucin Fatiman, sam kuma ransa be ɓaci ba illa ma burgeshi data ƙarayi domin ta nuna ita ɗin Macece me ra'ayi wani abu da ta gani tattare dashi be ruɗeta ba dukda yasan basu da masaniyar shine mamallakin gurin da sukayi siyayyar.

Akan shiga motar ma seda akayi daga da ita Anty Sauda ta balbaleta da masifa Ahmad ya shiga tsakani yana bata haƙuri tareda lallashin Fatiman kan ta shiga su tafi, shikam Ajinta burgeshi yakeyi saɓanin sauran Matan da suke zuwa gurin kaga Mace har Mace amma babu Aji, wasu takanas suke zuwa ganin CEO saboda an san kusan koyaushe yana zaune a office ɗinsa indai yana Kano, wasu ma zuwa suke da ƙaryar kaya zasu kawo, ba kuma zasuyi magana da Sales Manager ba seda CEO kai tsaye da Ma'aikatan suka gane me yake kawo su se suka fara hanasu suce basa karban kaya a hakan wasu zasu zauna a waje jiransa muddin anga motarsa a Parking lot kiran waya kuwa seda ya maida layinsa private idan beyi saving Number ba kira baze shiga ba sannan ya samu Sa'ida, kuskurensa saka Main Line ɗinsa akan Banner su.

Suna tafe suna yar hira da Anty Sauda har suka isa bakin titi inda ze ajiyesu dan Mota bata shiga har cikin layinsu, Anty Sauda ta fita ta kira yara suka fara kwashe mata kayanta, seda suka gama tas ta kalli Ahmad tace
"Mungode sosai, Allah ya saka da Alkhairi"
"Amin Anty, Allah kuma ya raba lafiya, gashi banga gidan ba balle nazo cin naman suna"

"Seka karbi number waccen, idan na haihu seta sanar maka ko?" Cewar Anty Saudan. Ya juya ya kalli Fatima yana cewa
"Kodai ki bani da kanki, kalli fa yanda ta haɗa fuska Allah sa ba tunanin yanda zata shaƙeni takeyi ba , daman idan kin haihu karki bari ta fara ɗaukan Babyn kar yayo gadon rashin fara'arta
".
Fatiman na zaune tana kuma jinsu kamar an dasata a gaban motar, tasan me afkuwa ta afku shiyasa ta kasa motsawa daga inda take. Abinda ta guda da hawa lift ɗin kenan, idan da Napep suka hawo bakinta alaikum se samu hanyar kurɗawa ya kaisu har ƙofar gida data sauka ta afka kuma ba lallai kujerarsa ta nuna ba sabanin ta Ahmad da take fara tas ita kam yau ina zata kai wannan abin kunyar staining a motar jama'a daga Rage hanya?

Ya miƙawa Anty Sauda wayarsa ta sanya masa number Fatima wadda tare suka siyi layin banbancin lambobin ƙarshene kawai da tata shiyasa ta riƙe kafin ta sake masa godiya ta shige layi ba tareda tabi takan Fatima ba.

"Ko ba tare kuke ba?" Ahmad ya faÉ—a yana karantar fuskarta, dukda be santa ba amma wannan fuskar tata da akwai abinda yake damunta ba iyakar Miskilanci bane".

Fatima ta yunƙura domin babu amfanin zaman da takeyi a cikin motar. Ta kalli kan layinsu dukda tsakiyar ranace ƙwal amma munafukai yan saka'ido na nan suna bin inuwar gefen Titi a haka zata ratsasu ta wuce?
Jakarta ta buɗe da dabarar kiran Anty Sauda ta bada Hijabi A Miƙo mata tazo mata, da zasu fita harta saka Hijabinta haka nan ta canza kaya ta saka Abaya Light blue ashe rabon abin kunya ya jata da Hijabi ne Asirinta a rufe kota bata masa kujera shamiƙewa zatayi ta tafi dan ba sake haɗuwa zasuyi ba balle taji kunya. Takaicinta ya ƙaru sanda ta zaro wayar taganta a mace, ita dai yau bata fito da sa'a ba.

Ta kalli Ahmad fuska a marairaice, so take tace ya bata aron wayarsa amma ina hali irin nata na shegen Miskilanci ya hanata se kawai ta rungume jakarta jin ya yiwa motar key da alamun ya gaji da jiranta ne ze tafi da ita ko yaya ta kama murfin motar ta buɗe, tana zura ƙafafunta waje Ahmad dake lura da duk motsinta yaga abinda take boyewa, da saurin gaske ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta da ƙarfi. Ta dakata ɗin tareda kallonsa yace mata

"Me yasa tun a Mall bakiyi magana an baki pad kin gyara jikinki ba? Da a haka zaki keta titi ki wuce waɗannan Mutanen?" Mutanen daya faɗa ta kalla. Suna nan tun tsayuwarsu a motar suka baza idanuwa suna naɗar rahoton gulma da munafunci wanda sukafi ƙwarewa akai. Fita yayi daga motar ya buɗw booth, tana tunanin Pad ɗin ze ɗauko mata ko me? Koda yake a yanzu ai pad bata da amfani a gurinta ta samu abinda zata rufa ta isa gida kawai take da buƙata kuma wayar tasa dai itace mafitarta. Tana saƙa abinda zatayi ya dawo da leda a hannunsa ya miƙa matata karɓa ganin kamar yadin Hijabi ko Abaya.

Hijabi ta gani data warwarshi har bata sanda ajiyar zuciya me Nauyi ta kwace mata ba, ta zura a jikinta kafin ta saci kallonsa kamar mara gaskiya tace
"Nagode"
"Babu damuwa, but next time idan kina cikin yanayin buƙatar taimako kiyi magana bakiyi ɓacin rai kina kumburi ba"
"Toh" kawai tace masa kafin ta fita tana waiwayen inda ta zauna ya baci sosai kuwa kamar ma da gayya Jinin yazo da yawa dan ya kunyatata.

Murmushi Ahmad ya rakata dashi harta ƙulewa ganinsa, harya tada motar se kuma wani tunani ya saka ya gyara parking ya sauka yabi cikin Layin da sukayi. Beyi nisa da yawa ba ya tambayi wasu yara gidansu Fatima sukace basu santa. Ya riƙe ƙugu yana kallon Lokon da ya tabbatar idan ya ƙureshi ze tsinci kansa ne a wata unguwar daban ba wadda yake ciki ba, hagu da dama kuma layukan duk basa ɓulla ya tabbatar gidansu na daga cikinsu, harya haƙura ze juya tunda ya samu number wayarta sega wani saurayi ya fito daga wani gida da bokitin Markaɗe ya tareshi yana tambayarsa gidansu Fatima.
Chapter 10 · 0% Book details