← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 71

Sashe 22

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaki ta zabga data kalli sumar kansa da tasha gyara irin na Yan Ball din nan itako yana daga irin abinda ta tsana dan duk girman mutum idan ta ganshi da irin Askunan nan kallon wanda be san kansa take masa ba. Tuna abinda yake gabanta yasa ta kauce ya sake tareta yana cewa

"Nayi sallama kin bini da tsaki ki amsa mana Ammata" ya faÉ—a da wata cukurkudaddiyar hausa yanda kasan wani Yare yake.

Tsakin ta sake masa tayi baya a tsiwace tace
"Ka matsa Malam ni ina da abinyi"
"Zan masa amma se kin mun abu uku, firstly ki amsa sallamata dan wannan dolene a musulunci kinsani then you tell me your name, lastly you give me your digits" ya ƙarasa yana irgawa da yatsunsa. Harara ta galla masa amma yanda ya bake hanyar tasan ko tureshi tace zatayi ko gezau bayi zeyi ba kuma duk inda tayi binta yake wannan yasa ta amsa masa sallamar a ƙufule tana cewa

"Se ka matsamun na wuce Malam tunda na amsa maka sallamar ai"
"Ai baki cika sauran sharuddan ba" ya sake faÉ—a se tayi saurin tareshi da cewa
"Nayi wanda zan iya"
"Baki isa ba, na miki rangwame cikin biyu you choose one, either you tell me ur name or you give me your contact, barshima, bari sunan, bani number kawai" ya faɗa yana miƙa mata wata tsadaddiyar waya da bata taɓa ganin irinta ba. Ta harareshi taa harari wayar tana cewa

"Ashema kai zaka zabarmun abinda zanyi? To sunana Afeeya, dan girman Allah ka matsa ka bani hanya dan ka rigada ka makarar dani"

"Kince Allah wuce Afeeyah, suna me kyau kamar yanda kike da kyau" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi ya harɗe hannaye a Ƙirji yana jifanta da wani kallo.
Tuni tayi masa nisa, a jikinta taji har sannan yana biye da ita bata waiga ba har ta shiga Department dinsu ta sauke numfashi ganin yan Ajinsu a waje suna hirarraki alamar Malamin bezo ba, ba tareda ta tsaya ba ta shige ciki abunta dan zuciyarta wani bugu take kamar wadda tayi tseren gudu.

Ta wutsiyar ido ta kalli window inda taji alamar idanun mutum akainta, yana nan tsaye kuwa ya harÉ—e hannayensa a
Ƙirji damatsansa sun ƙara fitowa kamar an aje duwatsu se tayi sauri maida kainta kan desk tana jin yanda zuciyarta take tsere, bata dade da zama ba Malamin ya ƙaraso, ya ringa zabga dictation suna rubutawa ajin awa biyu ne amma tsabar mugunta ya roqi next Lecturer da ze shigar musu ya ara masa lokacinsa tun takwas da wasu mintina bamu muka samu kanmu a hannun Dr Abolude be barsu ba se sha biyun rana zuwa sannan hannun kowa ya sage nata kam har sun kumbura gefen inda take riƙe da biro sunja ruwa daman haka yake mata duk sanda tayi dogon rubutu tofa se tayi jinyar hannu abinka da Jiki duk Madara inji Qawayenta.

Taimakon da Allah yayi musu da yace ba lokacin ze karbi note din ba Class rep ya hada ranar Wednesday ya kai masa kuma shine CA dinsu, tayi hamdala a fili dan rubutun nasu rabi da rabi tayi, idan tayi nata se ta kama na Badar duk a tsoron kar a tashi karɓa ta rasa gara ko yayane dai ta rubuta mata wani abu.

A mugun gajiye ta wuce Geography mosque dan Azahar ta kawo kai gara ta tsaya tayi sallah kafin ta koma Hostel ta É—an kwanta zuwa La'asar suna da wani Ajin. Seda tayi alwala ta shiga cikin masallacin tayi Nafila raka'a biyu kafinta nemi guri saitin fanka ta kishingiÉ—a tana jin kamar tayi bacci saboda gajiya ga bashin na daren jiya da batayi dakyau ba. Wayarta ta shiga Vibrating ta janyota daga cikin jaka, gaba É—aya ta sha'afa da ita.

Tun gurin ƙarfe Tara an kikkirata dukda bata duba ba tasan baze wuce Ahmad bane me kiran yanzun ma tana cirota kiran nasa na tsinkewa a nan taga missed calls ɗin daya mata guda biyar se Message da yake tambayar lafiya yana ta kiranta bata amsa ba idan tagani ta kirashi.
Tayi ƙaramin tsaki da batasan dalilin yinsa ba kafin ta danna kiran layin nasa ringing biyu tayi ya katse se gashi ya biyo baya dukda uban katin wayar da yake loda mata duk satin duniya amma idan ta kirashi baya ɗauka, ire iren halayensa na kyautatawa da suke son tursasa zuciyata sonsa kenan badan ta aminta dashi ba har ƙasan rainta.

Cikin muryarsa me sanyi amma ba kamarta mata bafa Aa irin ta Mazajen da hayaniya bata dame su ba yayi mata sallama, ta amsa kafin ta gaishe shi wannan tarbiyyar Ummansu ce gaisuwa ga duk wanda ya girme su ta kuma rigada ta zame mata jiki.

"Fatima! Lafiya ina ta kiran wayarki tun da safe baki ɗauka ba?" Ya faɗa bayan daya amsa mata gaisuwar. Taja numfashi saboda Fatiman daya kirata, bata so amma ta rasa ta yanda zata gayawa Ahmad ya dena. Sunan Innar Baffansu ce kuma sunan Kakarsu data haifi Ummansu sannan Babbar Yayar Baffansu wadda ita ta riƙeshi itama sunanta Fatiman. A hannunta ya girma bayan rasuwar Iyayensu, su uku kacal suka haifa daga Ita se shi se ƙaramar ƙanwarsu Umma Halima ita Umma Faɗima wadda ta riƙe Baffa ta girme musu sosai dan shekaru bakwai ta bawa Baffansu shi kuma ya bawa Umma Halima shekaru biyar, wannan tudu ukun da naci na sunana FATIMA yasa kowa yake jin nauyin faɗarsa se AFEEYAH Laƙabin da Baffa ya bata ko a makaranta a rigister kaɗai ake kiranta da Fatima amma kowa da AFEEYA ya santa banda Ahmad da bata tsammanin ma yasan ana Kiranta da Afeeyah.

"Kinyi shiru, kina jina kuwa?" Ya sake faÉ—a abinda ya maidota daga tunanin data tafi ta sauke numfashi kafin tace
"Ina jinka, ina Class tun 8 bamu jima da fitowa ba na shigo masallaci kenan daman yanzu nake so na kiraka" tayi masa ƙarya badan tana da niyyar kiran nasa ba. A tausashe ya sake ce mata

"Ayya sorry love, gaskiya Malaman nan suna wahalarmun dake da yawa amma kun gama gaba É—aya yau koh?"
"Aa fa ina da wani Ajin 4-6 ma" tabashi amsa, cikin jimami ya sake cewa
"Toh Allah ya bada sa'a, in sha Allah kamar yau ne zaki ga kun gama ai sedai ki ringa tuna baya kina kewa. Nima daman É—azun na shigo Zaria na É—auki Jafar yanzu haka ma muna hanya zan kaishi Abuja ze koma London. Naso mu haÉ—u amma babu komai in Allah ya kaimu se Wednesday zan juyo ko Thursday zan tsaya kafin na wuce Kano na ganki.

"Allah ya tsare hanya ya maido da kai Lafiya" ta faÉ—a, cikin tsokana yace
"Shifa Jafar, baki yi masa Addu'a ba? Ko na bashi wayar ku gaisa harda ma fa saboda shi naso mu haÉ—u yau dai Abokanan faÉ—a suga juna"

Cikin sauri tace "Allah ya kiyaye ko Inuwarsa bana fatan Allah ya nunamun ballantana wai mu gaisa dashi, idan so kakeyi na sake faɗa maka na tsaneshi fiye da yanda yake tunanin shi baya sona" cikin tsiwa take maganar tareda fushi tana tuna kalaman Jafar ƙanin Ahmad, shekara guda kenan amma ta kasa manta abinda yayi mata.

Murmushi Ahmad yayi haka kuma ta jiyo wani dogon tsaki daga cikin wayar wanda ta tabbatar da Jafar É—in ne yayi ai ko a fusace ta É—aga murya tace
"Allah ya tsinewa tsaka ma ballan tana kai abin banza"
"Fatima" Ahmad ya kira sunanta se tayi shiru amma bata amsa masa ba yaci gaba da cewa
"Ni nake Driving, idan na isa zan kiraki Ok?"
"Allah ya tsare ka kula mun da kanka kaji" ta fada bawai har ranta ba sedan tabbatarwa da tayi wayar a speaker take kenan tunda yace shi yake tuƙi Jafar yana jin duk maganar ta keyi shi take so ta bawa haushi".
"I will, you take care too I love you" Ahmad ya sake faÉ—a tana jiyo Jafar É—in cikin fushi yana cewa

"Wlh Yah Ahmad either you cut this call ko kayi dropping nawa a nan, da wata muryarta ta Villagers ko Turanci bata iya ba"

"Tunda ba karatun fatiha na kasayi ba ai da sauƙi, kaida Turancin yake yaran Babarka ai se kayi tayi" ta faɗa bata jira amsarsu ba ta kashe wayarta tana jan tsaki daidai nan kuma aka fara kiran sallah.
Fita tayi ta ɗaurayo bakinta ta dawo ranta na suya, Bata taba haɗuwa da mutumin dayaci mutuncinta yaci na iyayenta irinsa ba ita kuwa bata da babban maƙiyi daya wuce wanda yace ze keta Alfarmar iyayenta a duniyar nan, za'a iya takata ta shanye amma fa kar a taɓa mata Iyaye Jafar kuma ya keta wannan Alfarmar ya zagesu shiyasa bashi da sauran mutunchi a idonta balle ta raga masa.

Shi kansa Ahmad ɗin Alfarmar Baffanta yaci da har taci gaba da kulashi dan yace ba laifin Ahmad bane ba ba kuma shi ya saka Jafar yayi abinda yayi ba dan haka ko a gurin Allah laifin wani baya shafar wani ta haƙura taci gaba da saurararsa amma wannan dalili yasa karɓuwar daya fara samu a gurinta a baua ta wargaje kuma har zuwa yanzu tsayin shekara daya da faruwar abun ta kasa mantawa haka zuciyarta ta gagara yarda da Ahmad ɗari bisa ɗari har yanzu.
Chapter 22 · 0% Book details