← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 71

Sashe 64

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can gefe gaba kaÉ—an da inda Jay yayi parking Matasa guda uku suna zaune akan Benci suna cin gyaÉ—a. Gida daga cikinsu yace
"Waccen motar tafi minti Ashirin a tsaye anan kuma a kunne", na kusa dashi ya keɓe baki kamar wata mace yace
"Kai da ganin motar ai kasan lalatattun Yayan masu kuÉ—in nan ne baze wuce budurwa ya É—akko yazo nan yana lalubeta ba, yar iskar saboda ma bata da daraja a gunsa baze iya kama mata hotel ba a mota ze latse ta" yanda yake maganar seka rantse da Allah a idonsa yaga ana abinda yake faÉ—ar, na farko daya fara magana ya cafe yana cewa

"Kuma fa haka ne, wlh yanzu haka shegun suke daman indai kaga mota da dare me baƙin gilashi an zuge shi tsaf kuma motar a kunne to wlh Iskanci sukeyi".

Na ƙarshen da tunda suka fara maganar saka musu baki ba se sannan yace
"Haba Lawan, me yasa ba zaku kyautatawa mutane zato ba? Yanzu idan ranar lahira aka tsayar dakai ta yaya zaka kare kanka akan wannan shaidar daka bayar tamkar ya faru a gabanka? Me yasa a koda yaushe zuciyoyinku suke hasaso sharri a maimakon Alkhairi a kusa? Ba ku tunanin lalura ce ta tsayar da me motar nan? Ta yuwu kiran waya ne ya shigo masa shiyasa ya tsaya dan ya amsa domin yafi Alkhairi akan ya ringa tuƙi yana amsa waya.." Wanda ya kira da Lawan ya katse shi yana cewa

"Ji wannan Bashir É—in wace irin wayace sama da minti ashirin kuma ya bar mota a kunne se kace a gidansu ake siyar da mai?"

"Kai kuma me wannan motar ne zaka yi tunanin mai ze zama matsalarsa kalleta fa ni banma san sunanta ba" Wanda ya fara takalo maganar ya bashi amsa, Bashir yayi murmushi yace

"To sa ace ba waya yakeyi ba idan kuma lalurace fa wani abu ne ya same shi a cikin motar?"

"Kamar yaya?" Lawan da Idris suka haÉ—a baki gurin tambayarsa, Bashir yace
"Kwanaki naji labarin wata mata kamar haka tana tafiya a mota ta gangara gefen titi ta tsaya tun mutane basu damu da tsayuwarta ba har dai suka fara tunanin wani abu ana duba motar aka tarar ashe Allah ya mata rasuwa tana kwance kan sitiyari" Lawan ya zabura ya tashi hannu akai yana cewa

"Innalillahi muje mu duba kar gobe mu zama mu zamu bada labarin a radio" ya durfafi motar Jay Idris na take masa baya sannan Bashir. Sau biyu suka Ƙwanƙwasa masa glass, seda ya goge fuskarsa da Tissue idanunsa sun kaɗa sunyi jajir kafin ya zuge glass ɗin gefen da yake gaba ɗaya ta yanda suna iya hangen gefensa zuwa bayan motar. Bashir ya masa sallama kafin yace
"Afuwan ranka ya daÉ—e munga kana tsaye ne tun É—azu shine mukayi zaton ko ba lafiya ba"

Murmushi Jay yayi yace
"Lafiya lau, nagode da kulawa"
"Kai wannan ai Jay ne" Idris ya faɗa cikin ƙaraji tuni kuma Jay yaja motarsa ya bar gurin Idris da Lawan suka haukace suna cizon yatsa, Jay ne a gurin sama da minti ashirin amma basu sani ba
"Kai amma fa naga idonsa sunyi Jaa, kodai shaye shaye yake a motar?" Lawan da be daddaraba ya sake faÉ—a.

Ahmad ya kasa zaune ya kasa tsaye a bakin Gate yana jiran dawowar Jay, baze barshi ba yau se ya masa kaca kaca , yana nan zaune bayan ya kira Fatima tace masa kan da sauƙi sega motar da suka fita da ita ta kunno kai, yanda yake tuƙi ya sake fusata Ahmad dan da gudu ya shiga gidan tamkar me wasan mota. Jay be lura da Ahmad ba dan haka yana kashe motar ya fito yana rangaji ya nufi bangarensu, a daidai barander Alhaji Audu juwa ta kwasheshi kamar wanda iska ta buge se ganinsa sukayi yif ya faɗi a ƙasa Ahmad daya taho a fusace se gashi yayi kansa da gudu cikin tashin hankali, kardai kuma shaye shayen Jay ya fara be sani ba? Tambayar da yakeyiwa kansa.

PAGE 23
"I'm fine, i just missed a step" Jafar daya yunƙura ya tashi da taimakon Ahmad ya faɗa. Ko kusa Ahmad be kama zancen wai lafiya yake ba domin idanunsa sun ƙaryata hakan sannan damuwa ta nuna ɓaro ɓaro akan fuskarsa dukda a lokacin be karanci yanayin nasa a matsayin damuwa ba, to wace damuwa ce haka zata samu Jafar. Yana riƙe da hannunsa kamar yaro gudun karya sake faɗuwa su ka kai ɗaki duk yanda Jafar ke ce masa ya barshi ze iya tafiya be saurara ba. Ahmad yayi mamakin da Alhaji be leƙo ba duk salatin da ma'aikatan gidan suka ringayi kuma yana zaune a falo ya tabbatar ma ya hango me yake faruwa dan a buɗe Ƙofar take, Jay ya kwanta akan gado tareda juyawa Ahmad baya, gani yake idan suka cigaba da haɗa ido ze karanto abinda yake ƙoƙarin dannewa ba kuma ya so ya fahimta.

"Meya sameka Jafar? What did you take?" Ahmad dake tsaye akansa ya tambayeshi, Jay ya juyo, kafin ya kai ga bashi amsa aka banko ƙofa, tashin muryar da sukajiyo gabanin buɗe ƙofar yasa suka gane wacece
"La'ilaha illallahu shikenan magauta sunyi nasara akaina na shiga uku ni Binta na lalace jifa ya tarar da Jafaru" ta faÉ—a hannaye biyu dafe da kai tana jijjiga. Jay ya tashi zaune Ahmad kuma ya matsa gefe can ya jingina da bango yana kallon Hajiya seta kuma juya a fusace kansa tana cewa

"Aniyarka ta bika wallahi tallahi duk wani mugun abu ya ƙare akanka, wato ka ƙunsheshi a ɗaki kana jira ya mutu seka fito dashi ko?"

"Haba Hajiya wai meye haka kikeyi? Wace irin magana kike haka dan Allah?" Jafar ya katseta cikin ɗacin rai, ko wane munafuki ne yaje ya gaya mata se Allah, salon tazo ta Ƙara masa damuwa kan wadda yake ciki. Hajiya ta juya kansa tana cewa

"Banza sallamamme dabe san ciwon kansa ba, wato ya tattareka ya kaika ta yuwu ma tuni ya sadaukar da kurwarka shine yau ya kai musu kai su lashe, to billahillazi kurwarka ɗaci ne da ita ba zata ciwo ba sedai ya musanya musu data tsohon ubanku da dama yaci yanzu ya matsa ya bar mutane su sarara, taso muje ai inada sauran Tazargade da tsakin kuka yanzu zan turara maka su koma wane shegen maye yayi gigin taɓaka sedai ya cinye kurwarsa wlh" ta matsa ta shiga janyo ƙafafunsa kamar wani yaro ƙarami. Da iyakar ƙarfinta take jansa hakan yasa ya miƙe dan dole yana mata mitar abinda takeyi. Ko a jikinta ta tasashi gaba, ta waiwaya ta gallawa Ahmad dake nan tsaye yana kallon ikon Allah harara kafin tace

"Waya sani ma ko kaima har sun lasa maka, to wlh nafi ƙarfin ƙaramin maye irinka manyan ma nan zasu ganni su barni". Dariya ta bashi dan har seda ya murmusa kafin ya zauna akan gado bayan da suka fice ta tasa Jay a gaba. Kwanciya yayi rabin jikinsa na kan gadon Ƙafafuwansa na ƙasa ya tallafe kansa da hannu biyu ya zubawa POP dake ɗakin ido. Meya samu Jay? Wane abu ya fara ko kuma yake aikatawa daman can dabe sani ba? Meya janyo sauyawarsa tun bayan daya dawo yake abubuwa ba tareda ya sakashi a ciki ba? Shi damuwarsa ba rashin including nasa da Jay bayayi a sabgoginsa bane ba Aa yanda yake abubuwan a Ƙudundune ne kamar mara gaskiya. Jay da ko Ƙofar gida muddin yana nan baze fita shi kaɗai ba seya rakashi amma shine ya iya tafiya har Abuja ba tareda rakiyar Ahmad ɗin ba, wannan be bashi mamaki sosai bama akan zuwa gidan Baba Alƙali da yayi nan ma shi kaɗai. Yanzu sun fita lafiya ya dawo cikin wani yanayi daya kasa fassarashi. Babu wata alama a tattare dashi da zata nuna maye ko wani abu makamancin haka sannan daka kalle shi kasan baya cikin hayyacinsa, Fargabarsa da damuwarsa yasan menene yake damun Ɗan uwansa a yanzu.

Fatima ta faÉ—o masa a rai ya zaro wayarsa daga Aljihu ya kirata dan yaji ya anta ciwon kan amma bata amsa ba se ya soka wayar a chaji ya tashi, seda ya cire T shirt É—in jikinsa ya mayeta da Jallabiyya kafin ya fita dukda goma ta gota ya shiga cikin gida. Momy da Maimuna tareda Sarah autar Hajiya Binta suna zaune a falo, Momyn na kallo su kuma suna aikin filling Samosa.

"Manyan yan kasuwa" ya zolayesu bayan daya zauna suka gaishe shi. Sarah tace
"Dan ma Yaya kaƙi ka bari mu fara kaiwa Mall ɗinka ai da wlh da yanzu munfi haka"

"Wannan jagwalgwalon ze bari ku kai musu?" Momy ta faÉ—a se yayi saurin cewa
"Haba ba jagwalgwalo bane Momy gyare gyare mukeyi shiyasa ma ban amsa musu ba amma da mun gama bayan frozen har soyayye zasu ringa kaiwa ai naci naji da daÉ—i kuma na yarda da tsaftarsu".
Sarah da Maimuna suka tafa cike da jin daÉ—i kafin suka shiga tattare kayan aikinsu dan daman sun gama suka wuce kitchen. Bayan shigewarsu Momy ta kalli Ahmad tace

"Ina kukaje da Jafar ne uwarsa ta shigo ɗazu tana ta hayagaga da faɗar maganganu?" A taƙaice ya bata labarin fitarsu zuwa dawowarsu da kuma abinda ya faru yanzu a waje. Momy tace
"Allah ya rufa asiri toh, ta yuwu ko bashida lafiya musamman tunda ya dawo be zauna guri guda ba yana ta stressing kansa ga Ranar kwanakin nan da zafi ba irin wadda ya saba da ita bace, daman É—azu ina falon Alhaji Babanku ya kirashi yake gaya masa Jafar yaje gurinsa akan maganar zuwa tambayo masa aure ko?"

"Eh haka ne" ya bata amsa ta sake cewa
"A ina ne?"
"Wlh ban sani ba, yau mukayi zamuje kuma ya tafi ya barni"
"Au kaima baka sani ba? Koda yake ai na fuskanci kwanakin nan uwarsa ta matsa masa ni tunda ya dawo ma sau biyu ya shigo falon nan
"Uhm" kawai yace mata jin haka yasa itama tayi shiru da maganar can ta sake cewa
Chapter 64 · 0% Book details