← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 71

Sashe 21

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad na Zaria Jafar ya tafi dan tarewa yayi a Hotel kullum haka ze je Samaru ya wuni a Faculty of Art yana bibiyar ta inda ze gamu da Fatima amma taƙi yarda su haɗu se ranar daya kwana uku ne ya samu nasarar ganinta sammako ya buga tun bakwai yaje ya zauna a bakin Class ɗin da zasuyi Lecture, a gurin wani Guy ya samu Time table ɗinsu bayan daya nuna masa hotonta ya tabbatar masa ya santa bata zuwa Class kwana biyu amma na goben ya tabbatar zata zo indai tana Makaranta dan Malamin baya wasa Individual Attendance yake ɗauka and is automatic carry over idan mutum yayi missing wannan tasa ya tafi da wuri, 8 zasu shiga amma 7 bata gama rufawa bama ya kafa ya tsare a bakin Ƙofa.

Yana tsaye a gurin suka zo ita da Badar da wasu yammata biyu, bata ganshi ba se Badar ce ta nuna mata shi tana cewa
"Kinga Ahmad"
"Ahmad?" Ta maimaita da mamaki tana kallon inda take nuna mata se gashi kuwa a tsaye ya zuba hannaye a Aljihu yana binta da kallo suna hada ido maganganun Jafar suka fara dawo mata tamkar a lokacin yake faÉ—arsu wannan tasa tayi saurin É—auke kanta ta doshi class É—in da sauri dan ba zata bari ya tareta ba amma kafin ta shiga yasha gabanta.

"Ka matsamun na wuce" ta faÉ—a ba tareda ta bari sun haÉ—a ido ba saboda yanayinsa da yake neman karya mata lago ya samu galaba akanta.
"Zan jiraki a waje ku gama" ya faÉ—a a sanyaye yanajin tamakar ya rungumeta saboda So, taja baya saboda kusancinsu yayi yawa tana cewa

"Karka jirani dan ko ka zauna bazan saurareka ba"
"Shikenan, zan shigo Ajin na roƙi Lecturer ya bani dama a gaban kowa nayi magana dake hakan ya miki?"

Yanda yayi maganar ta fahimci ze aikata abinda yake nufi dan haka tace
"Karka shigo, ka jirani a waje"
"Good girl" ya faɗa yana mata murmushin ƙarfin Hali, kansa ciwo yake masa be taɓa zaton haka so yake dagaske ba. Fatima ta wuce, Badar ta matso fuskarta ɗauke da fara'a, she is lively ko yaushe fuskarta a washe take kamar ta Ahmad ɗin muddin ba an tsokalota bane.

"Hi" ta faÉ—a tana waving masa,
"Hello Badar" ya mayar mata yana É—aga mata hannun shima bakinta har kunne jin ya ambaci sunanta, ashe dai Fatima ta bashi labarinta.
"Karka damu, just give me your number, kaje ka samu comfortable guri ka zauna i will bring her to you damun gama Class" ta faɗa tana bashi wayanta. Ya karɓa ya shigar da Digits ɗinsa kafin ya mayar mata yace
"Nagode Badar, i will be in Shinkafi Elite, zan jiraku a can"

"Ayt, se munzo" ta sake ɗaga mishi hannu kafin ta shiga Ajin ta zauna kusada Fatima dake leƙensu ta window, duk a kan Idonta Badar ta bashi wayarta tana ganin yanda suke ta wani Murmushi duk seta tsargu. Badar batace mata komai ba har akayi Lecture aka gama suka fito, tana lura da yanda take satar kallon gurin da alama Ahmad yake nema amma bata ganshi ba A zuci Badar tace
"Munafuka kawai tana so tana kaiwa Kasuwa".

Suna tafe duk Fatima bata da laka, tunani takeyi ko ya tafi? ƙila ya haƙura da itan kawai tunda har ya karɓi number Badar.

A hanya Badar tace su biya ta Shinkafi su siya Chips tace ta ƙoshi amma Badar ta nace se sunje in yaso ta siya ita kaɗai.
"Kije can ki zauna kinga akwai layi kafin azo kanmu" ta nuna mata Table ɗin dake kusa dasu, Fatima tayi tsaki, can ƙarshe ta wuce seda ta zauna kafin ta lura da Ahmad ne a gurin. Zabura tayi zata miƙe ya dafe hannunta, karo na farko da hakan ta faru tsakaninsa da wata Mace da ba Muharramarsa ba. Cikin sauri ya saki hannun nata se kuma ya miƙe tsaye ganin tana shirin barin waje yace

"Kwana na uku ina yawo cikin makarantar nan, na kasa samunki a waya, idan na canza layi na kira ki da kinji muryata seki kashe daga ƙarshe kindena Amsa duk wata number dana kira da ita why Fatima? So kikeyi zuciyata ta buga na mutu kowa ya huta? Dame kike so naji? Da Matsalarki koda rigimar Jafar? Wlh ko ki tsaya muyi magana yanzu ko kuma ba biki har cikin Hostel, Bet me I'm fuc***g serious zaki sha mamakina yau".

Kuka Fatima ta fasashe masa da shi kawai ta zauna tareda kwantar da kanta akan Table ta shiga rera shi. Ahmad ya zauna ya harɗe hannaye yana kallonta ba tareda ya hanata ba. Badar kuwa saya karɓi order ta tafiya tayi Hostel.
Seda Fatima tayi kuka me isarta Ahmad na zaune ya na kallonta kafin ta tsagaita ta fara zazzage masa abinda yake ranta wanda Jafar Bechi yaci ace ta gayawa sanda yake zaginta amma ta huce akan Ahmad É—in.

"Kiyi haƙuri dan Allah kuma ki manta duk wani abu daya faɗa shima cikin fushine and he regretted everything he said, zan haɗaku a waya ze baki haƙuri komai ya wuce" Ahmad ya faɗa kamar zeyi mata kuka.

"Ni na haƙura sannan kaima na haƙura dakai, Brother ka ya gaya mun what i need to know about your Family, na sani daman ba zasu soni ba saboda ni Talaka ce amma ka sani ka kuma gaya masa tabbas mahaifina Talaka ne amma ba Matsiyaci bane domin yana da wadatar zuciya kuma sana'ar sa da yake zagi Halal yake nema Haram ba sannan ba yawon Maula yake gurin wasu mutane ba balle ya samu damar zaginsa ya Ƙasƙantar dashi. Nasan mutunchin Iyayena dan gaka bazan bari wani ya taka darajarsu ba, ko beyi rantsuwar bazan Aureka ba na rigada na yankewa kaina wannan shawarar sannan ka gaya masa Maita daya dangantamu da ita, nasan ko nayi shari'a dashi a duniya ba za'a bi mun haƙƙina ba saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma zamuyi shari'a a Katun da ba'a bada cin hanci" ta faɗa sababbin hawaye na sauko mata.

Duk yanda Ahmad ya zata abin ze zo masa da sauƙi ya zarce haka, taurin kaine da ita kamar mutanen farko ta riƙe maganganun Jafar Bechi se maimaitasu takeyi.

"Amma Fatima ko Allah daya halicce mu baya kama wani mutum akan laifin da wani daban ya aikata muddin ba sunyi tarayya a cikin aikata laifin ba. In har akan Abinda Jafar yayi miki ne na baki haƙuri kuma in har zakiyi mun Adalci kin san bani na sakashi ba, ki faɗi kanki tsaye cewar bakya sona, ba kya Ƙaunata kawai dan rajin kanki ba saboda abinda Jafar yayi miki ba. Na dade da fahimtar haka, amma na kasa cire rai dake bansan me yasa zuciyata ta kasa haƙura dake ba, ina Addu'a akan Allah ya zaɓa mun mafi Alkhairi a kullum kuma ji nakeyi tamkar ana Ƙaramin sonki, duk yanda nakeji akanki wlh zan jure kuma zan roƙi Allah ya yayemun muddin kika furta da bakinki bakya Sona ba kuma zaki aureni ba nayi miki Alƙawarin daga nan gurin ba zaki sake gani na ba zan kuma fita daga rayuwarki koda Sonki ze zama Ajalina zan haƙura dake Fatima".

*************

A YEAR LATER

Gudu gudu sauri sauri take tafiya saboda ta kusa makaraz fata takeyi Allah dai ya rufa mun asiri ta samu ta shiga Ajin nan kafin Dr Abolude ya rufe, ba rasa ajinsa ba wannan banzan halin nasa na marking note se kace a primary ko secondary school shine abinda yake bawa kowa haushi dashi balle ita yau da rubutun ya zamar mata biyu, ga nata gana Badar dole taje da wuri ta samu sit a gaba, layin wanka ne ya bata mata lokaci saboda Monday ce kusan kowa na block dinsu nada Ajin safe.

Qiris ya rage ta hantsila daidai Basket ball court saboda wani mutum da tun fitowarta daga Amina Hall ya zura mata ido kamar me shirin ganin yayan hanjinta, taja tsaki ta dauki Jakarta data zame ta fadi a ranta tana mitar wannan kallo haka taci gaba da zabga sauri a karo na biyu ta sake yin gaba tana shirin gangarawa daidai Senate building saboda mutumin dazu data gani tsaye gabanta kamar Aljani. Batasan sanda ya biyota ba harya tare mata hanya, zuciya ta harziqomata amma bata tankashi ba ta sake rabeshi ta wuce a kato na biyu se ji tayi daga bayanta ance

"Sihh, jimana yammata". Raita ya ninka da baci, a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce irin wannan kiran wulaqancin da maza sukeyiwa yammata ba, se kace wata mota ko Mashin a ringa maka wani Sihh wasu tantiranma har fito suke kamar masu kiran kare. Taci gaba da tafiyarta kamar zata tashi sama ga haushin mutumin ga na bata mata lokaci da yake tayi dan ta tabbata yanzun kam ta makara sedai ta maqale a bakin window idan batayi sa'a ba. Karo na uku ya sako fadowa gabanta, wannan baƙar ɗabi'a ta mutumin da abin takaici take baya ko tunanin zata iya faɗuwa tunda batasan da shi ba ya ringa diro mata kawai kamar wani jifa.

"Dan Allah ki saya" ya faɗa yana kallonta se a sannan ita ma ta kalleshi fuskarta babu alamar rahama amma can ƙasan ranta seda ƙirjinta ya buga saboda se yanzu ta kalleshi da kyau. Wani zabgegen mutum me ƙirar ƙarfi jiki a murɗe dan a yanzu da yake tsaye gabanta shigarsa ta nuna motsa jiki yakeyi, rigace Armless jikinsa da wandonta wanda da kaɗan ya zarce guiwa kayan suka qara bayyana surar ƙarfinsa, bata tantance fuskarsa ba dan bata kalleta sau biyu ba, yanda ya kankane mata hanya yasa ta raina kanta da tsahon da take taƙama dashi dan wata yar firit ta ganta a gabansa.

"Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faÉ—a da sautinsa daya sa ta gaza tantance wane yare ne shi, sake daga kanta tayi ta sake kallon fuskarsa, a zubi za'a kirashi Bahaushe ko kuma Hausa Fulani amma a zubin jiki dai yafi kama da Irin zabga zabgan Igbiran nan ko Inyamurai haka fatar jikinsa da take da haske dukda ba fari bane amma a goge take tar yanda kasan ya hada jini da fararan fata.
Chapter 21 · 0% Book details