← Book details Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 71

Sashe 46

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Audu na kurɓar baƙin shayi daya sha spices, Girkin Hajiya Rabi ne ita ta dafa masa tana kawowa Hajiya Bintan tazo ta kankane gurin dole ta fita ta bata guri dan har ta fara sakar mata maganganu tana ci mata zarafi shi kuma Gwankin na zaune shirim bece komai ba. Ya gama sauraron Hajiyar kafin yace
"Oh ya samu mata kenan da yake ke zaki nemo masa auran shiyasa ya fara sanar dake?"

"Shi wa? Ummu nace maka ni a suwa Amadu ze faɗamun ya samu Matar Aure Aisha ce ni kowa?" Ta faɗa tana wani taɓe baki. Alhaji ya sake zuba shayinsa yana sha yace
"Shi ÆŠan naki nake magana"
"Wai Jafaru? Dama idan be gaya mun ba toh wa kake so yaje ya fara sanarwa ko yana da wata uwar ne bayan ni a duniya?"
"Aa bance ba, shi Ahmad É—in dake ya É—aukeni uba ai tun fara neman yarinyar da yakeyi ya sanar dani, kawai inda ya nemo auran ne be gama kwanta mun a rai ba shiyasa ma kika ga an kawo yanzu maganar bata tashi ba amma yafi shekara da sanar dani".

Har wani zullo tayi kamar zata kwanta a gabansa tace
"Ashe maganar ta daÉ—e? Daman Ummu tace anfi wata shida da zuwan nasu tun kafin lokacin bikin su Hafsatu to ashema ka sani toh naji kace gidan daya nemo auran ne beyi maka ba, da akwai matsala kenan?"

Da zuciya É—aya yace mata
"Yar wani Bakanike ce yarinyar Malam Hafizu akace sunansa a Alfindiki yake, a binciken da na saka akayimun dai Mahaifin yarinyar nace bashi da matsala mutumin kirki ne toh amma ita yarinyarce surutu yayi yawa akan yanda Samari suke zuwa gurinta wannan yazo wannan ya tafi gashi a matsayin mahaifinta irin rayuwar da akace tanayi ta wadata ya zarce ace shi yakeyi mata, kinsan yaran yanzu, zakiga Iyaye suna iyakacin ƙoƙarinsu gurin tarbiyya amma idan sun fita se abinda hali yayi musamman masu tafiya karatu wasu garuruwan ba gaban Iyayen nasu ba to wannan yasa na dakata kuma shima Ahmad ɗin tun maganar farko da mukayi be sake tayar mun da zancen ba dukda dai ina da labarin suna tare haryanzu kuma ita kaɗai yake kulawa ta yuwu yana jira ta kammala makaranta ne tunda ance shekarar ƙarshe take".

Tamkar me É—aukar karatu haka Hajiya ta naba'a tana sauraron Alhaji se gyaÉ—a kai takeyi har ya kai aya kafin cikin Jimami tace
"Ikon Allah, shi kuma Amadu inda ya tafi kenan? Nida nake ta sauraro naji ya samo yar gidan Ɗangwate ko BUA tunda suke abokanan goga kafaɗarka a ƙasar nan seya ɓige da yar gidan Bakanike? Toh Allah ya rufa asiri, ita dai ta Jafaru ance Balarabiya ce dan ya turawa da Munirah hotonta wai irin wanda ake kalla sau ɗaya ne shiyasa bata kwafa ba ta ajiye mana. Todai daya zo koma ya ake ciki zamuji, seka fara shirya wa'inda zasu nemo masa auran inajin dai baze wuce a Saudi Arebia ba ko Dubai"

Alhaji yace mata
"Toh, Allah ya kawo shi lafiya"
"Toh amma Alhaji ina da wata magana idan babu damuwa kuma ka bani dama in faɗa" yanda tayi maganar yasa ya tattara hankalinsa akanta dan yaji me zatace. Hajiya ta gyara zama kamar gaske kai a ƙasa tace
"Dama Alhaji akan mu'amalarka da yaran gidan nan ne naga ya kamata a gyara wasu abubuwan, ina nufin su Alhaji Babangida da sauran yaran da basa cikin gidan nan. Bana jin daÉ—in yanda kowa idan ya tashi yake É—ora mun laifi a ringa cewa ni ce na rabaka da yayanka.

Kaga girma ya cin maka, ya kamata ace zuwa yanzu ka fara sakin wasu abubuwan ka bari Manyan yayanka suyi maka".

Alhaji yayi tagumi yana kallon Hajiya Binta data sake gyara zama tana cewa
"Ba harkar kasuwancinka nake nufi ba, wannan ai kana da magada daka rigada ka koya musu komai kuma suka goge akai ina nufin kamar harkokin aure, kaga daga kai har Yakubu kun manyanta ya kamata ku zauna ku huta ku fara sakarwa Yayanku suna jan ragamar abubuwa".

"Wato ba zaki ringa karanta sunan Yakubu ba, Idan beci darajar girmata da yayi kin kirasa da Yaya ba ai kya bashi sunan da kowa yake kiransa dashi Alƙali" Alhajin ya tareta. Ta lanƙwashe kamar yarinya tace
"Allah baka haƙuri saboda faɗa ne uffararan Baba Alƙali nake so nace, to da kai dashi duk ku huta ka kirawo Yayanka gaba ɗaya ka zaunar dasu kuyi maganar nan, ka ware wanda zasu ringa zuwa tambayowa Maza aure da kuma wanda zasu ringa karɓan na mata idan an zo. Amma kafin nan ya kamata duk wani abu daya taso ka ringa tarasu kana shawara dasu, ta hakane zaka jasu a jiki suma su sake dakai a hankali se kaga duk sun dawo gida a dena zagina a gari ana cewa na raba yaya da ubansu".

Alhaji ya sakeyin shiru yana nazarin maganarta, Alƙali Yakubu ya taɓa yi masa makamanciyar magana irin wannan, yace ya kamata ace ya ringa janyo Yaransa a jiki domin ya gyara kuskurensa na baya. Rayuwarsa ta fara zuwa gangara, be kamatu ace ya mutu ya bar kan iyalansa a rarrabe kamar yanda suke a yanzu ba. Maganar Bintan se ta sakashi Nazari, tabbas abinda ta faɗa gaskiya ne domin Abokanansa masu Manyan Yaya kamar nasa da yawa yanzu a kwance suke suna hutawa komai da masuyi musu, ze gwada shawarar tata koda akan zuwa batun Neman aure ne da karɓar ze saka su yasan babu wanda zece bazeyi ba a cikinsu.

"Kamar yanzu da zancen auran Ahmad dana Jafarun nan musamman na Ahmad da kake da kokwanto akan yarda ko akasin haka, ka tarasu, ka nemi shawararsu kaga zasuji daÉ—i suga ka mutuntasu kuma su sun fika sanin kan duniya yanzu se kaga an samu maslaha ai ko?" Ta sake faÉ—a. Alhaji ya jijjiga kai da alamar gamsuwa, tayi murmushin cin nasara sannan tace

"Toh amma fa karka gayawa matanka ko Yan uwanka shawarata ce dan ka san cewa za'ayi da wata manufa nayi ni kuma Allah yaga zuciyata babu komai face Alkhairi so nakeyi ka shirya da yayanka ka haɗa kan zuri'arka", bata tashi daga gurin ba seda ta gamsar da Alhaji Alfanun abinda tace yayin ya kuma yarda da hakan. Babu ɓata lokaci a daren ya kira Alhaji Babangida, umarni ya bashi akan ya haɗo masa kan Yan uwansa daga Babannan zuwa Mu'allim, banda Matan da kuma Zayyad da Abdallah da basu isa ayi wannan shawarar dasu ba. Alhaji Babangida ya shiga mamakin ko lafiya wannan kira haka da Alhaji yayi musu amma babu damar tambaya. A washe gari ya sanarwa da waɗanda yake da numbers ɗinsu a waya ta hanyar Text message yace su sanar da sauran. Ya sake kiran Alhaji domin ya manta be tambayi ranar da yake da buƙatar ganinsu ba.

"Ranar Asabar É—in nan" Alhaji ya bashi amsa. Alhaji Babangida yace
Zan sanar dasu ranar, amma naji Jafar yana tafe ranar Talata, ba za'a iya É—age taron a jirayi zuwan saba?"
"Aa, duk abinda aka tattauna idan ya dawo zaku sanar dashi" da haka sukayi sallama. Ya gayawa Alƙali ze zauna da yaransa duka ya kumayi murna da hakan domin an samu cigaba kenan Alhaji Audun ya shiryi samun daidaito tsakaninsa da Iyalansa.
PAGE 17
A bisa dole Iyalan Alhaji Audu suka amsa goron gayyatar daya aika musu dashi. Ba kalar mitar da basuyi ba amma haka suka zo domin koda basa ga maciji da mahaifin nasu sun sanshi sarai baya É—aukar wargi, farillan rashin mutumchi kuwa sala sala yanadasu wanda yake amfani dasu gurin ladabtar da duk wanda yace zeyi masa giggiwa.

A cikin su daman wanda yafi kowa taurin kai Alhaji Hussaini ne, da Dr Hassan ya sanar masa da kiran Mahaifin nasu take yace masa
"Bazanzo ba, inada abubuwan da suka fi muhimmaci da sauraron kalaman son rai da wannan tsohon ze faɗa mun in kuma ya fara tafiya gargara ne yake so ya bada wasiyya ka karɓa harda tawa ka riƙe na bar maka in ma mutuwa yayi ni wlh na yafe gadonsa tuni". Seda Hajiya Zubaida Mahaifiyarsu tayi masa kaca kaca bayan da Dr Hassan ya sanar mata da abinda yace tace kuma tilas yaje idan kuma ya isa ya tsallake umarninta daman ita kaɗai take maganin Iya shegensa, yana son mahaifiyarsu yana tausaya mata yana kuma riƙe da abinda aka labarta musu cewar Alhaji Audun yayi mata tun kafin haihuwarsu da bayan zuwansu duniya.

Ƙwato su da yayi ya maidasu gidan ya zube su a tsakar gida shine abun daya ƙara ta'azzara tsamar dake tsakaninsu. Yanda Hajiya Binta ta ringa yi musu, kalar azabatarwar da tayi musu har gobe yana addu'ar kafin ta mutu in sha Allahu seta ɗanɗani sama da baƙin cikin data shayar dasu. Matan da akace banda su dalilin irin wannan taro da ba'a taɓa yin irinsa ba suka san lallai da akwai wani babban Al'amari a ƙasa wannan tasa kowacce ta wanko ƙafarta ta taho ranar taron. Momy da Hajiya Rabi basu san wainar da ake toyawa ba har s ana i gobe taron da suka tsinkayi muryar Hajiya Binta na bada umarnin abinda za'a girka gobe da yawan wanda za'ayi. Lokacin Salim na falon Momyn yana cin abinci yayi tsaki yace
"Wai me matar nan take shiryawa ne? Dan dai Alhaji bashida wata shawara tasa ta kansa se abinda tace masa"

"Wani abu ya faru ne?" Momy ta tambayeshi shine ya faÉ—a mata kiran da Alhajin yayi musu. Tayi shiru, ita tayi girki jiya yauma itace amma ace Alhajin bega ya kamata ya sanar mata da komai ba ai shikkenan. Bata masa zancen ba har washe gari da Asuba kafin ta baro bangaren nasa taji yana waya da wani abokinsa yana sanar masa baze samu zuwa wani É—aurin aure ba shine bayan ya gama yake ce mata wai ze gana da Yayansa duka akan maganar aurab Ahmad.

Cikin mamaki tace "maganar auran Ahmad kuma? Yaushe zancen ya taso da ni ban sani ba? Sannan naji kace zaka tattauna da Yayanka akan maganar daman haka kakeyi idan auran yayan naka ya tashi ko kuwa wani sabon salo ne ka tsiro dashi da za'a fara akan Ahmad?"
Chapter 46 · 0% Book details