Sashe 15
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu fa kake cewa ka shirya facing kowanne challenge amma kace ba zaka iya yiwa Alhaji Maganarta ba kaga kenan kaida kanka kasan maganar bame yuwuwa bace Alhaji baze karɓeta ba, kuma ni yanzu da kake so nayi masa magana idan nayi and it turns out Negative response nasan ni zaka ɗorawa laifi saboda na nuna maganar batayi mun ba, kayi haƙuri for the fist time bazan iya maka abinda kake so ba, kamar yanda Momy tace ka sameshi da kanka, Yah Ahmad is high time you stand for your self. Alhaji fa ba Dodo bane bare ka ce tsoronsa kake ji, go meet him ka gaya masa buƙatarka but it should be you and him alone, karka bari maganar nan ta fita asan wa kake nema,
Allah ya bada sa'a but i will pray you change your mind kafin ka sameshi because magana ta Allah banji yarinyar tayi mun ba" matsayar Jafar akan zancen Fatima kenan.
A karon farko Ahmad yayiwa wani mutum ƙarya, ya kasa samun Alhajinsu da maganar se kawai ya yanke komawa gidansu Fatima ya kuma tabbatarwa da Mahaifinta yayi magana da nasa Iyayen kuma sun yarje masa daya nemi auranta. A zuciyarsa ya tabbatar Allah baze bashi kunya ba tunda Aure yake so yayi ba wani mugun abu ba, kafin sanda zasu buƙaci ya turo ze san yanda zeyi da Alhaji, idan ma bashi ba Baba Alƙali ze kaiwa maganar Auransa kawai.
"Amma da akwai magana guda, Mamana Karatu takeyi, ta ƙare shekarar farko zasu shiga ta biyu yanzu suna hutu ne saura yan kwanaki su koma A can Jami'ar Zaria take Karatun" Malam Hafizu ya faɗa masa. Ahmad dake durƙushe yana faman sunne kai yace
"Babu komai Baffa, gidanmu gidan Karatu ne. Idan Allah ya nufa zamuyi aure Fatima tana cikin makaranta bbau damuwa zanyi duk abinda ya kamata gurin ganin bata takura ba ko Karatunta be samu matsala ba, sannan idan ta zaɓi har seta kammala kafin muyi Aure zan iya haƙuri na jira lokacin, fatana kawai na samu Amincewarta da taku"
"Allah ya shige mana gaba ya sa a ƙulla Alkhairi, bari na shiga ciki na turo maka ita" cewar Malam Hafizu daga nan ya shige gida.
Tun zuwan Ahmad na farko Malam É—in ya sanarda ita daya wassafa mata kamaninsa ta ganeshi tunda ba sanin sunansa tayi ba. A lokacin ji tayi kamar tacewa Baffan nata ya sallameshi kawai yace ya mata Miji, tsakani da Allah be mata ba, kuma ita da wanne ido ma zata sake kallonsa bayan wancan abinda ya faru shi ma ya zeyi mata haka ya dawo? Dataji shiru be kirata a waya ba ta zata ya janza shawarane ashe shi me gaba É—aya ya shirya mata biyowa ta hannun Baffa.
Tana jin yanda Baffan yake ta yabon Kamalarsa da hankalinsa sannan ya gayawa Umma yanda sukayi da abinda yace masa, Jiki a sanyaye ta fita, Dogon Hijabin datayi sallah dashi ne a jikinta, bata tsaya gyara fuska ba balle akai ga fesa turare ko sauran Al'adu da yammata sukeyi idan zasu fita hira haka ziƙau ɗinta ta fita abinka kuma da jiki kalar Madara a hakan ma tayi kyau abinta.
A cikin gida kuwa bayan fitar Fatima Umma tayi jugum kafin ta kalli Malam tace
"Ban tsammaci yaron nan ze dawo ba, Anya kuwa Malam ba'a yi ɗage da yawa ba? Ɗan gidan Alhaji Audu Bechi yazo neman Auran Afeeya, wannan fa ba irin Mijin Yayarsu bane idan ma ana maganar masu Arziƙi irinsu Alhaji Audu a ƙasar nan Sirikin Saudatu inaga ai ko gurin baze leƙa ba, gaskiya ni koda da sahalewar Iyayensa ba zanso wannan Auran ba, Malam kafa san irin zamanin da muke ciki yanda Aure ya zama ƙwarya tabi ƙwarya duk kuma wadda tayi kuskuren faɗawa gurbin da ba nata ba zata fusakanci ƙalubale"
Ki kyautata zato ki kumayi Addu'a Allah ya zaɓa mata binda yafi zama Alkhairi, sannan ki tuna shi yaga Afeeya yace yana sonta bawai tura masa ita akayi ba, Nutsuwa da Kamalar yaron ta burgeni idan har Allah ya zaɓa matashi a matsayin miji zanyi mata murna kwarai dan daga ganinsa mutumin kirki ne" inji Baffa. Umma ta nisa tace
"Toh, Allah ya zaɓa mafi Alkhairi amma dai Alhaji Audu Bechi fa.."
"Ai kingama magana tunda kika miƙawa Allah zaɓi sedai mu zuba ido muci gaba da Addu'a kawai" Baffan ya sake tareta.
Seda Fatima tafi minti biyar tsaye a soro kafin ta hada courage ta fita, wata irin kunya da nauyin sake haɗa ido dashi takeji tasan yana ganinta wancan abun ne zero faɗo masa a rai, da dai taga babu sarki se Allah yasa ta fitan, Ahmad na jingine jikin katanga ta raɓe gefensa tana yar siririyar sallama kai a ƙasa tamkar wadda ya kama tana gulmarsa.
Murmushinsa me kyau yayi ya amsa mata sallamar kafin ya tsaya dakyau yana fuskantarta, har sannan kanta a ƙasa murya a sanyaye ta gaidashi
"Hajiya Fatima, se yanzu sarautar ta sakeki kenan har ina shirin na ƙaraso soron na taroki ai" ya faɗa cikin raha. Bata tanka ba haka nan bata ɗago kanta ba, ya waiwaya ya kalli Dakalin gurin kafin ya kalli mutanen da suke wucewa kamar an basu gadi duk wanda yazo seya zura musu ido sannan ya wuce se ya kalleta yace
"Mu zauna a nan ko mu tsaya cikin soron?"
"Bari na kawo maka abin zama" ta faɗa kafin ta juya cikin gidan ranta babu daɗi, shi gurin zama ma yake nema, ita data fita da niyyar su ƙarƙare kuma yana neman yaja maganar da tsayi.
Kujerun roba ta kawo guda biyu ta saka a Soron ta koma ta dauko pure water da Zobon da Ummansu take siyarwa ta haɗo masa da ƙaramin kofi dukda bata da tabbacin zesha. Seda ta aje komai kafin tace ya shigo, yana ta doka murmushi kamar sabon Ango ya zauna, kallonta kaɗai nishaɗi yake bashi musamman yanda take sunne kai yasan meye dalilinta naƙin haɗa ido dashi amma a ganinsa wannan ai ua wuce, banda abinta idan Allah yayi wata rana na jikinta ma ai wanke mata zeyi balle gurin da ta ɓata. A taƙaice yayi mata bayanin kansa da dalilinsa na zuwa gurinta.
"Kema se ki bani taƙaitaccen bayani akanki" ya faɗa yana ƙarewa fuskarta kallo.
Kyakykyawace Masha Allah komai na fuskarta ɗan daidai hasken fatarta kuma ya ƙara ƙawata kyan nata, tana da tsayi dan ko ze fita da kaɗan ne sannan ba ramammiya bace kuma bata da ƙiba, baze iya ƙiyasta shekarunta ba saboda suffarta irin wadda bata nuna shekaru ce, se kayi wa mutum kallon yaron idan kaji ainihin shekarunsa kuma kayi mamaki. Yanayin zubin jiki da fuskarta yafi kama dana Jajayen Buzayen Niger ko kuma Fulanin Mambila, sannan daga yanayin goshinta ya fahimci tana da kufar gashi, kuma irin me Laushin nan dan gashin goshin nata a kwance yake luf kamar na Jariri sabuwar haihuwa gashi baƙi siɗik.
"To ai kasan sunana Fatima kuma nan ne gidanmu" maganarta ta maido shi daga tunanin daya tafi. Ya saki murmushi, jan Ajin nata ya fara yawa, ya zata kuma tunda har yaga mahaifinta kuma zata É—an sake masa tasan dai bada wasa yake yi ba. Ya gyara zama yace
"Nasan sunanki Fatima kuma naga gidanku amma ai ni ba iyakar abinda na faÉ—a miki a kaina ba kenan, na gaya miki mena karanta, aikina har adadin yan gidanmu da wanda nafi so seda na gaya miki fa"
Tayi shiru tana jinsa, idanun daya zuba mata su sukafi damunta da alamu kuma idan ba magana tayi ba baze dena kallonta kamar ze hango yan cikinta ba dan haka tace
"To ai ni banida wani abu da zan gaya maka ne, amma dai kamar yanda nace maka nan ne gidanmu, mu uku ne ai kaga Anty Sauda itace babbarmu se Yah Malam.."
"Jafar? wanda yayi mun sallama da Baffa?" Ya katseta, kai ta É—aga masa kafin taci gaba da cewa
"Shi nake bimawa, ni kuma banida ƙani ko ƙanwa, ina makaranta a Zaria Level two zan shiga ina karantar English Literature, bayan Baffa da Umma dasu Anty Sauda Ina da Best Friend Badar i think iyakar abinda kake buƙatar sani akaina kenan" ta ƙarasa tana yamutsa baki.
"Masha Allah ku uku kacal a gidanku kenan, ashe ke ɗin Autace shiyasa shagwaɓarki tayi yawa, shekarar ki nawa toh"
"20" ta bashi amsa a gajarce tana ci gaba da murza zoben hannunta. Sukayi jugum shi yana kallonta ita kuma tana faman juya Zobe, wayarsa dake Aljihuce ta katse musu shirun ya cirota ya duba, Jafar ne yake kiransa, ya nuna mata screen É—in wayar yana cewa
"Jafar ne yake kirana".
Tankar wadda take zaune akan ƙaya ta miƙe da sauri tace
"Ka amsa toh, bari naje ciki kafin ka gama". Kallonta yayi kaɗan ya kasa fassara yanayinta amma dai kamar she is not comfortable with him, ya mata uzurin haɗuwar farko ne dan haka ya miƙe shima yana laluba Aljihubsa yace
"Ai inaga zan wuce kawai idan naje gida se na kirashi wayarmu bata yankewa da wuri ga dare ma ya farayi karna zaunar dake a waje" Kuɗi ya zaro masu yawa daga Aljihun nasa ya miƙa mata yana cewa
"Kinsan farin shigan zuwa hira ne ni, bansan me akw tafiya dashi zance ba kiyi haƙuri ga wanan kisha Sweet kafin na sake zuwa"
"Nagode" ta faɗa ba tareda ta karbi kuɗin ba se wani kallo da ta musu ta ɗauke kai kamar taga wani abunda bata so. Wayarsa ya sake miƙa mata uace ta saka masa Number ta wancan ta goge, nan ma seda taji jum sannan ta karba, ta saka number ta mayar masa. Akan kujerar data tashi ya ajiye mata kuɗin ya juya yana cewa
"Zan kiraki idan na isa gida se kiyi saving number ta. Ki gaida Umma, se na sake dawowa" Ganin ta tsaya kamar wata sokuwa kawai tana kallonsa yasa yayi murmushi ya fice daga soron yanajin wayarsa nata ƙara yasan Jafar ne bala'in wutar ciki ne dashi yanzu idan ba ɗauka yayi ba ya ringa kira kenan ga Mita kamar Mace.