Sashe 24
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Minti Arba'in Lecturer yayi ya sallame su saboda duk kusan sunyi covering komai sati biyu ya rage musu su fara Exam. Surayya Mas'ud ta jata Ribadu Hall dan taga Babynta, ta haihu sati uku kenan yau ta fara shigowa Lecture ta bar yaron gurin sister ta acan suka shantake har akayi Magriba kafin suka fito tare Mijinta yazo daukarta ita kuma ta shiga Amina. Tun daga staircase ake jiyo kayaniyarsu Sururat da Badar haka suke kullum basa gajiya da magana kamar Aku ta shiga da sallama ashe video kayan Lefen Anty Yusra Yayar Badar suke kallo, dalilin zuwanta Kaduna kenan ta cire Hijabita ta ninke itama ta shiga kallon, Anty Yusra tasha kaya, ko da yake abu ne irin nasu na kwarya tabi Kwarya, Babansu Badar Ex Senator, zaben da ya gabata ya sauka Baban Angon ya karɓa.
Suna kallon suna cin abunda Badar tazo musu dashi da suka gama ta koma kan gadonta ta kira Baffanta. Cikin shaƙuwar dake tsakaninsu suka gaisa, yace mata
"Mamana ya makatanta ya karatun? Babu dai wata matsa ko?" Safe da yamma idan sukayi waya seya tambayeta haka, Yanda Baffanta yake sonta yasa take jin zata iya sadaukar da komai sabida shi.
"Komai Lafiya Baffa, baka koma gida bane har yanzu naji ƙarar babura?"
"Ban koma ba yanzu dai nake shirin tafiyar, kinga Yayanki ya turo miki kuɗi ko? Kiyi haquri da abinda ya samu abinda nake ta jira a biya ni ne har yanzu shiru lamarin ƙasar se Addu'a kuɗi sunyi wuya a hannun mutane ga Yayan naki shima komawarsa Makaranta ya tashi shiyasa nace ya raba wannan ya tura miki idan yaso in Allah ya yarda wasu suka samu se a sake aiko muku"
"Babu komai Baffa sefa da nace maka ma ka barshi ina da komai kudin ma akwai canji a hannuna zasu isheni har zuwa sati hudun amma kaƙi yarda da ka barwa Yah Jafar ɗin duka yafini buƙata" ta faɗa cikin muryar shagwaɓa. Baffa yayi murmushi yace
"Ba wani nan na sani ko baki da komai ba zaki faɗa ba ni kuma haƙƙi nane dole nayi miki fatana dai kiyi karatu dukda bani da haufi akanki amma ina sake jan kunnenki da ki tsare kanki ki kuma tsaya iya inda Allah ya ajiyeki karki ringa hangen wasu da suka fiki ko kiyi sha'awar abinda suke dashi rayuwa mataki ce wata rana idan da rabo se kiga kin kamo su".
Ta haddace wannan kalamanna Baffa, shekara uku ke nan tunda taa shiga Jami'a kullum sukayi waya se yayi mata takararsu. A sanyaye tace
"In sha Allahu Baffa ina kiyayewa kuma zanci gaba da kiyayewa"
"Yauwa Mamana Allah yayi miki Albarka, ina Badariyya yau ban jiyo karaÉ—inta ba" Baffan ya sake fada nayi murmushi nace
"Gata nan Baffa bata dade da dawowa daga Kaduna bama an kawo Lefen Yayarta jiya É—azu ta dawo ta kawo mana kayan dadi"
"Aiko naji zancen gurin Ummanku tace nan da wata biyu ne auranko? To Allah ya sanya Alkhairi yasa zamu ga lokaci in sha Allahu idan na samu dama nima zanje musu ɗaurin aure saboda kirkin mutanen da yanda suka riƙeki ba wanda zaka yanke zumunchi dasu bane kice ina gaisheta ina mata ya hanya"
Kafin ma Afeeya tayi maganar Badar ta wafci wayar dan tunda ta kira sunanta ta miƙe. Ta gaisheshi ta ringa washe baki tana cewa Amin kafin ta miƙa mata wayar har sannan bakinta a buɗe, sukayi sallama yace ta gaida sauran yan
É—akinsu.
"Muguwa da zaki mun buƙulun gwalagwalan addu'oin Baffa" ta faɗa bayan data kashe wayar.
Zata bata amsa Anty Sauda ta kirata dan haka ta dakata ta É—aga da sallama kafin ta shiga tsokanarta tana cewa
"Amarya uwargidan Alhaji Ali, kin tare gaba kin tare baya"
"Faɗi ki ƙara dagani babu wata" ta baya amsa ta tabbata tana can tana fari da ido irin yanda take duk sanda tayi mata kirarin. Dariya sukayi kafin na gaisheta ta amsa tana tambayata makaranta.
"Ina Mutumina Mahfuz? Banji Gwarancinsa ba yau?"
"Suna gida, nazo Marmara ne, bikin Ƙanwar Baban Aziza za'ayi wannan satin dan wulaƙanci basu kawo mun Anko ba se ɗazu shine na kawowa Umma kuma ranar Laraba za'a saka"
"Tofa, seta zarga miki ko Bubu ce ai ina Umman har yanzu ba'a gyara wayarta ta bane?"
"Me gyaran yace ya gama kuma Jafar ya koma makaranta ɗazu be karɓo mata ba, ina Badar?" Anty Sauda ta faɗa seta bawa Umma wayar tayi sallama da Hausarta da yau bata saisaita ba, Buzanci ya cinye harshen nata sama da shekaru Talatin da Baffan ya aurota ya kawota Nigeria amma Hausa ta gagara kama harshenta dakyau. Bayan sun gaisa da Umma itama ta sake mata jan kunne akan ta kula da kanta kafin tace na gaida Badar da sauran Roommates ta maidawa da Anty Sauda wayar.
"Naji Umma tace kince se kunyi hutu zaki dawo, bikin Zuhran Umma Halima fa saura sati biyu, ba zaki zo ba?" cewar Anty Sauda. Afeeyah ta gyara kwanciya ta ce
"Saura sati biyu mu fara Exam kinga satin bikin kenan zan mata addu'a daga nan Allah sanya Alkhairi"
"Kedai dan bakwa shiri ne kawai amma nasan da Zainab ce ko jarabawar kike sekin zo ai"
"Zainab kikace ai, Yah Zuhra kuwa ko ina Kano be zama lallai naje bikinta ba wlh"
"Allah ya shiryeki da ruƙo Afeeya ke abu baya taɓa wucewa a gurinki ne wai?" Cewar Anty Sauda. Afeeya ta tunzura baki kamar tana gabanta tace
"Ai wlh duk wanda ya ci mutunchin iyayena ko bayan shekara dubu bazan yafe masa ba balle mu'amalar arziƙi ta haɗani dashi" ta faɗa cikin jin zafin abinda Itama Zuhran tayi mata, faɗe ya haɗo su ta zageta tace mata dangin Sadaka Yallah, kuma ai ba ita ta zaga ba da Ummansu take tunda itace Buzuwa daman kuma kullum idan tsiyar Babarta Umma Halima ta tashi da haka take zagin Umman tasu dan basa shiri, tunda aka aurota bata sonta a yanda sukaji wai da Aminiyarta Baffa yake so tunda ya tafi fatauci Nijar can ya hadu da Ummansu a hannun Mahaifinta ya zauna shikenan daya dawo yace ya fasa auran Ƙawar Umma Halima wannan ya
Ƙulla gaba tsakaninta da Ummansu har yau kuma dukda abin yayi sauƙi saboda girma da shekaru amma bata fasa rashin idan rashin mutunchinta ya motsa seta mata gorin cewar tunda aka aurota maimakon Baffa yayi gaba tsiyacewa yake wai yanda take fara tazo musu da farar Ƙafa.
Sallama sukayi tana cire wayar daga kunnenta kiran Ahmad ya sake shigowa. Tun tana wayar takejin alamar wani kiran, ta yatsina fuska kafin ta É—aga ita wlh ta manta ma shaf tace zata kirashi É—azu. Kamar ko yaushe cikin taushi yayi mata sallama ta amsa tareda gaisheshi sannan tayi shiru.
"Baki kirani kinji ya na sauka ba" ya faÉ—a a sanyaye, ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daÉ—i a ranta tace
"Kayi haquri, bacci nayi, ina tashi kuma kasan na gaya maka ina da class É—in yamma na dawo kuma ina ta zuci zucin na kiraka na manta wlh"
"Kullum dai uzuri Fatima, Allah ya nunamun lokacin da zanyi matsayi a zuciyarki da zaki dena mantawa da al'amurana. To ya makarantar? Ya lecturer? Badar ta dawo?"
Kunya ta kamata jin abinda yace kuma beyi fushi ba, tace
"Lafiya lau, Badar gata nan ta dawo tun da yamma".
"That's great, my regards to her, ki gaya mata idan dawo tare zamuzo da Bukar Babagana, friend É—ina da nake gaya miki surutunsu É—aya".
Ta guntse dariya tana kallon Badar kamar yanda ta tattara hankalinta akanta itama yanda kasan an bata ajiyarta in har auna waya da Ahmad ta ringa matsarta kenan seta tabbatar da batayi wani abun rashin kyautawa ba, ko bata faÉ—a masa maganar soyayya me daÉ—i ba dai to ba zata bari ta faÉ—i wadda zata bata masa rai ba.
"Zan gaya mata, kace na tanadi earpiece Aku biyu zasu haɗu ranar bazamuji kunne ba" ta faɗa tana fashewa da dariyar dan ta kasa ruƙuwa.
"Nidai babu ruwana bani na faÉ—a ba" cewar Ahmad shima yana dariya kafin ya sake cewa
"Baki tambayeni Jafar ba, jirginsu ya tashi babu jimawa yanzun nan ma na koma Hotel room"
"Ayya" ta faÉ—a a fili a zuciyarta kuwa tace
"Da shi kaɗaine a jirgin Addu'a zanji ya kife kowa ya huta da baƙin halinsa ai" Ahmad yace
"Ayya kawai zakice? Ba zaki masa fatan sauka lafiya ba jini nane fa Fatima".
Kafinna tashi amsa wayar tayi din din alamar shigowar wani kiran, na cire daga kunnenta ta duba sunan Bestie ne yake yawo se ta maida ita kunne tana cewa
"Amm, Umma tana kirana bari na amsa idan na gama zan kiraka"
"Muyi sallama kawai dan nasan da wuya ki kira, in kuma Allah ya dorani akanki yau kin kira i will be more than happy dan ina so nayi magana dake sosai, i really missed you Fatimaa" yaja sunan nata. Ƙirjinta ya buga, bata so ya ringa wani langwabewa yana mata magana hakan ze saka ta iya narkewa na fara sonsa dan ita ɗin son soyayyane da ita kamar wata India. Yanda take hasaso Mijin da zasu zuba madarar ƙauna ne Sam Ahmad bezo da cikakkiyar suffar ba.
Tana lissafin Namiji dogo me ƙirar ƙarfi a matsayin Sharukhan ɗinta, wanda ya iya tarairaya da kalaman soyayya masu saka jinin jiki ya tsaya, irin mazan nan da kallonsu kaɗai ze saka kaji zuciyarka ta motsa ko bashida sisi zata zauna dashi zata masa komai indai ze ringa kasheta da ƙauna yana dagata sama kamar yanda akeyi a India, ya ringa saɓarta kamar jaririya yana goyata
Mafarkinta kenan na Abokin rayuwa. Ahmad nada dukka suffofin datake so ta bangaren iya soyayya da tarairaya uwa uba akwai canji a hannunsa burin yammatan zamani Yaro da kuÉ—i sedai a gurinta ya rasa wani kaso me muhimmanci wanda take nema.