Sashe 11
Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Farace sosai?" Yaron ya tambayeshi ya gyaɗa masa kai alamar itace, yaron ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran dake wasa kira yace
"Ka rakashi gidan Malam bakanike"
"Bansan gidan ba" yaron ya faɗa yana zabura ze koma gun wasansa wanda ya kirashin ya talle masa ƙeya yace
"Gidan su Jafarun ne zakace baka sani ba banza gidansu yar Fara fa"
"To ai haka zaka ce mun ba yanzu Anty yar Faran ta wuce ba da Antynsu me Mota sun taho da kaya da yawa mu muka kai mata gidan ma ta bamu Cakulat" yaron ya sake faɗa kafin yayi gaba yana tsalle, Ahmad ya zaro dari biyar a aljihunsa ya bawa babban yaron kafin yabi bayan wancan. Da yar tafiya daga Titi zuwa gidansu a can cikin Lokon suke har sun kusa shiga Alfindiki ma daɗin da sukaji lokon gaba ɗaya lailaye yake da Interlock ga Fitulun Solar da alamu basu da matsalar haske har tsakar gida sun huta da kunna fiti. A ƙofar wani gida yaron ya tsaya.
Daga yanayin ginin zaka fahimci gidan masu ƙaramin ƙarfi ne, ya sallami Yaron da alawoyin dake cikin Aljihunsa sannan ya juya ya tafi daman gurin kawai yake so ya gani. Babu ƙyama ya saka Ruwa daya zubawa Omo da freshner ya goge kujerar tsaf, ya maimaita gogewar har sau uku kafin ya saka clean ruwa ya goge sannan ya sake fesa Freshner akai sa'annan ya ya tayar da mota ya bar gurin.
Yana tuƙi yana tunanota, yanda take haɗa fuska tana motsa ƙaramin bakinta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Ya tuna idanuwanta sanda ta rasa mafita ya bata Hijabi, muryarta a karaye da tace masa ta gode har zuwa tafiyarta a sanyaye kamar wadda batada laka. Zuciyarsa ta ringa ayyano masa gidan data fito, yanayi na suffa da tsarin halitta daga ita har Yayarta be taɓa hango daga irin wannan unguwar suka fito bama balle wannan gidan, seya tuna da wani abokinsa Munir da ya taɓa ce musu Mata da suka amsa sunan Mata na cikin Lungu.
"Kunga unguwannin nan da muke gani as no go, wlh mata nacan, kaga yarinya kamar ita tayi kanta gashi sun ƙoshi da tarbiyya kawai dai basu kai wayewar da muke kwaɗayi ba amma ni dai idan na tashi aure Lungu zanje na samo mata wadda zan ringa Faɗawa magana taji da ɗan kuɗina ƙalilan Alaji a hankali na wayar da ita yanda nake so" inji Munir ɗin to yau ya gasgata zancensa domin Fatima dai kodaga Villa ta fito ta isa Mace kuma za'a nunata a ko ina ba tare da anji kunya ba, shikam yaga Mata dukda tace be mata ba, ze tabbatar da se yayi matan dan baze bari ta wuceshi ba, ita ɗin tayi daidai da tsari da ra'ayinsa.
Yama manta da zeje gidan Nazira seda ya ganshi a ƙofar gidansu tukunna ya tuna, kwakwalwa duk tunanin Fatima har ya fara loosing focus. Gidan ya shige akan se da dare idan ya fita seya kai mata kawai. Haka ya ƙarasa yinin ranar har gizo take masa muryarta na masa amsa kuwwa. Ahmad be taɓayin budurwa da yaji ta shiga zuciyarsa farat ɗaya a ganin farko ya sakawa ransa ya samu mata ba se akan Fatiman. Mutum ne shi da idan abu ya shiga ransa tofa se Allah, Fatiman kuma abin nata yazo masa da gaske, daga haɗuwa yini ɗaya harya fara tsara rayuwar da zasuyi tare, har tunani yakeyi idan da gaske tace beyi mata ba wani kalar garari rayuwarsa zata shiga dan ya rigada ya kwallafa rai a kanta, shi kuma duk abinda ya saka rai da samu baya taɓa saduda har seya mallaki wannan abun. Yaya zeyi idan ya gaza cin galabar zuciyar Fatima ta Aminta dashi.
Seda yayi sallar Isha'i ya tafi gidan Nazira, ya tarar da Matan Naziru Uwargidan Anty Mardiyya da Amaryar da yayi kwanannan Yusra wato Yuseebaby Shahararriyar yar rawar Nanayece a Sabuwar Manhajar Tiktok, su suka fara yankewa bin waƙa ana rawa a tiktok ɗin cibi. Allah kaɗai yasan inda Nazirun ya yayibota kuma da yake me uwa a bakin murhune duk sukar da abokanan Alhaji suka ringa kawo masa akan Yarinyar wadda kowa ya bada shaidar bata jin magana cewa yayi tunda me Auranta yaji ya gani ai shikenan, Karuwa ma idan ta tuba ana auranta balle ita da babu wanda ze kawo shaidar cewa tana Alfasha, Yarinyar da har video take iyayi da undies ta ɗora a Tiktok amma Alhajin ya murje ido yace babu komai ya aureta, koda yake umarnin Hajiya domin ita yarinyar tayi mata, yanda tayi suna tayi shura tana da followers bila Adadin a duniya baki ɗaya ba iyakar Nigeria ba ga uwarta tana da kuɗi suna da ƙaton gida wanda akace ire iren Alhazan da take hulɗa dasu ne wani ya gina musu gidan, hatta Kawunta daya bawa Nazirun Auranta se bayan anyi Baba Alƙali ya binciko cewar ƙaryane ashe ba ɗan uwanta bane tsohon saurayinta ne.
Mahaifinta kuma yana raye sukace ya rasu, mutumin Sokoto ne, gajiya yayi da halin uwarta ya saketa tun Yusran na yar yarinya ta taho da ita Kano ta tashi a sakalce yanda dai take yanzu, to Me aure da iyayensa sunce sunji sun gani duk wani me abin faÉ—a dole ya kama bakinsa.
Sanda Ahmad ɗin ya shiga falon Nazirar ma tarar da ita yayi ta jera Yayan Nazirar Su uku yammata babbar ta riƙe yar Babyn ta kunna waƙa tana musu Video suna rawa Nazirar da Mardiyya da wata da be sani ba suna zaune suna hira daga gefe, ransa ya baci, tun batafi wata da shiga gidansu ba ta fara koyawa Yaran gidan wannan iskancin raye rayen ana video, seda ya kwace wayar Maimuna data Sarah, ita Aslamiyya tumda ya mata gargaɗi ta dena. Wayar Sarah ko awa batayi a hannunsa ba Hajiya tazo ta fara Tijara Momy tace ya basu wayarsu. Maimuna ma taurin kai tayi masa taci gaba dayi wai a Draft take saving randa ya ɗauki wayarta ya gani shikenan ya kasheta ya ajiye seda tayi wata uku taji jiki kafin ya bata to basu Kaɗai ba Babbar Yar Alhaji Zakariyya ma tana nan ance ta fara zama sananniya a Tiktok ɗin dukda dai ubanta yace wai tallan kaya takeyiwa Mamanta dake tana siyar da Dogayen riguna da sauran kayan kwalliyar Mata, amma fa rawa take tiƙa abinta kuma duk wani trend daya fito sune akan gaba gurin yi abin dai se a hankali.
Bayan sun gaisa ya Naziran yace mata
"Amma Anty kina kallo take ɗaukan video yaranki harda Baby zata saka a Tikto, baki san duk a nan yara suke kwaso baki kowa idan ya gani da me faɗar Alkhairi dame bakin sharri wani ma yabawa zeyi amma idan bakinsa bame kyau bane se kiga wani abu ya faru, ya kamata dai ku ringa kiyayewa, ko su wanda suka kawo Tiktok ɗin wayanda suka san abinda sukeyi a cikinsu basa exposing yaransu ƙanana ko zasu musu video basa nuna fuskarsu amma kalli yanzu dan Allah Nur ai ta wuce shekarun da zata ringa daukar hoto babu kallabi bare har a ɗorata a Tiktok".
Mardiyya tace "uhm" domin abune dayafi ƙarfinta tayi magana su koma gida ta haɗa mata tuggu gurin Mijinsu se ɗayar matar ce tace
"Nima dai na faɗa, Malamai ma nata wa'azi akan wannan shagalar data zo mana wlh, gaba ɗaya yara sun lalace, tun suna ƙanana an cire musu kunya ana sakasu suyi ta raye raye ana ɗorasu a duniya haka zasu tashi basajin nauyi ko kunyar yin rawa a ko ina ko a gaban wa kuma ta bakinka dame baki mai kyau da mara kyau kowa ya tanka Allah dai ya kiyaye. Kaganni ni ko saka hoton jinjiri a status na kiyaya wlh, nan wata ƙawata ta haihu, bakuga yaron ba Tabarakallah Masha Allah kyakykyawa kamar ɗan larabawa.
Ta ringa turashi group group na makaranta, na kasuwanci, na Novel ne groups ɗinta na WhatsApp babu inda bata tura hoton Yaron nan ba kowa kaya kaya anata yabawa wasu na cewa basu taɓa ganin Jinjiri me kyansa ba, in taƙaita muku wlh Yaron nan kamar wasa ya fara rashin lafiya, Asibiti har Saudiyya suka kaishi anyi gwaje gwaje ance komai lafoya ba'asan abinda yake damunsa ba yaron nan be samu lafiya ba har seda ta Allah ta kasance shekarar sa Ɗaya ya mutu kuma bata daddara ba yana Jinyar tana sake tura hotonsa wai a tayasu da Addu'a Allah ya bashi lafiya, shin idan ka haihu ba zaka iya faɗa haka kawai ba dolene se ka tura hoton Yaro ko Yarinya a group?
Kasan iya inda ze tsaya mutane da Aljanu masu ido biyu da masu huɗu duk suyi ta kalle maka Yaya to yi ta kanki dai ki karɓe jinjinniyarki idan ma su manyan ba zaki hanasu ba ita dai bata san komai ba kar a fara ɗura mata sheɗanci a kwakwalwa".
Yusra fa ta shaƙa tayi fam musamman da Nazira tace ta goge Video dan idan Babansu ma ya gani tasan se yayi faɗa ai ta zata a WhatsApp status zata ɗora shiyasa ma batayi magana ba. Ta ringa hararar Ahmad domin shiya zo da wannan sanaben, shidai ko kallonta beyi ba dan ko gaisawa basuyi ba ya gama abinda ya kaishi gidan ya tafi.
Yana cin abinci a falon Momy yana bata labarin zuwansa gidan Nazirar Jay ya kirashi, a speaker yasa wayar yana ci suna magana har zasu kashe Jay É—in yace
"Yah Ahmad waye ka gani É—azu that you hanged my call?"
Ahmad ya saki wani murmushi, shauƙi ya kwasheshi harya manta a inda yake. Wani baya yayi ya tallafe ƙeyarsa da hannu biyu yace masa
"Addu'arka ce ta karɓu, muna wayar nan naga wata tsaleliyar budurwa ta sace mun zuciya, I'm telling you my brother na samu matar Aure"
Ihu Jay ya fasa, a kwance yake akan tamfatsetsen gadonsa cikin apartment ɗinsa a birnin London amma haka ya tashi yana ihu yana tsalle kamar wani ƙaramin yaro. Ahmad kuwa besan katoɓarar da yayi ba seda ya ɗaga kai suka haɗa ido da Momy, a sittin ya fice daga falon seda suka kwana biyu suna wasan ɓuya dakyar tayi Bikonsa amma dukda haka sun zama kamar surukai baya iya haɗa ido da ita.