Sashe 99
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
sane dashi. A lokacin An jima da sakar mini yata kamila wance ta koma makaranta tana ci gaba da karatunta da bata samu tayi ba, kusam ta dawo rayuwar muahmamd wanda bansan da labarin ba saida taje gidan Adara aka mata duka, a lokacin raina ya baci kuma na jama kamila kunne akan ta rabu da rayuwar yaron nan in tanason kanta da lafiya, amma bata daddara ba ita da kawarta suka je mutum biyu wajen boka.............................................har sanadin haka ta samu wannan matsala na kadangaru wanda na tabbata Alhakine yake bibiyata. Munyi neman duniya wa bokan nan don mu biyasa koh mu basa hakuri ya rabu da ita, Amma ina bamu gansa ba duk malaman da muka kira shuru ba sauki, a lokacin na shiga tashin hankali ita kuma safina a lokacin take jin dadin ta, naje wajen ta akan ta taimaka mini akan zancen kamila koh da kudine don kaf abinda muka tara ya kare a wajen jinya amma haka safina ta murza ido bata tuna irin hallaci dana mata ba ta hanani koh biyar, ni kuma abin yayi matukar bata mini rai hakan ne yasa na d'auki kayan dakina na sayar na biya yan dabanda suke mini aiki tsawon shekaru, akan su kashe mini muhamamd yanda aikin safina zai lalace sannan nima na huce takaicina akansa, tunda ata dalilinsa rayuwar yata ya shiga garari, don haka kowa ma ya rasa. Aiko yan ta'andan nan sun bani tabbacin batar muhamamd wanda zancen yaje har kunnen safina, kuma ta zargi nice wanda har gida tazo mukayi fad'a kasha kasha, ta tafi ban sake bi takanta ba, sai kawai labarin rashin lafiyar safina ya riskeni, da kuma dawowar muhammad gida. Shine nazo neman yafiyar ku don Allah ku yafe mini sharrin shaid'an ne? Ai kece shaid'aniyar in kam, munafuka wallahi bazan taba yafe miki ba har abada kin cuceni kin rabani da matata kin muzguna ma rayuwar yata, Allah ya isa tsakanina daku kuma bala'i yanzun kika fara gani. Jin abinda abie yace yasa dada mikewa tsaye da hannu tayi pointing in mutanen gembu, maza maza su tashi su tafi gidan shugaba su tattari safina a yau innan su maidata wajen dangin uwarta babu ita babu safina har Abada, ita tana ta bauta mata ashe shaid'aniya ce. Baban kamila mikewa yayi yanzun nafisa har kisan kai kike? toh kiji daga yau bani bake kuma bara kiji na sakeki saki biyu daman babu igiya d'aya a tsakanin mu, ki tattara yarki ku kara gaba koh gidana karki koma don bakizo da kome ba, bazan iyya zama daku ba, kuka nafisa tasa da sauri ta rike kafar baban kamila tana neman yafiyar sa tunkudeta yayi ya kama gabansa. Duk yanda yusuf yaso w ajen yayi shuru abu ya gagara ganin yan gidan Adara sun rufarwa nafina da duka, waya Ammar yayi wa ofishin yan sanda cikin kankanin lokaci sukazo daker aka kwace nafisa anso tafiya da ita, Amma yusuf ya hana yace a barta kodon Albarkacin kamila dake d'auke da wannan matsala taje duniyace, haka ta mike daker tana koran kamila suka bar unguwan gwanin tausayi. Hafsa a ranan kuka tasha bana wasa ba kuma itama ta basu labarin, bayan rabuwarsu akan cikin bai zube ba, jinine ya zuba kuma mahaifinta yace sai an zubar da cikin Abdul salam, baza'a haifa masa a gida ba ganin yanda ransa ya baci yasa kanwar mamarta d'aukar ta ashan ta haifi kalamu bayan haihuwar sa ne matar cousin nata kabeer ta rasu, bayan shekara d'aya da mutuwarta sai ya nemi ya auri hafsa kuma ba musu findon ta amince dayake kowa yasan halin ta macece mai nutsuwa, kuma bayan auren su ta rike yaran kabeer hannu bibbiyu, wannan dalili yasa sa rike d'anta itama kamar nasa hatta su babayo basa nuna wa kalamu ba yan uwansu bane harya girma, bayan kalamu ta haifi yara uku shamsiyya(tayi aure a maiduguri) falmata da musa (auta) duk yaran hafsa ne da suka haifa da kabeer. Sosai abie ya nuna nadamar sa kuma ya nemi yafiyarta tare da sanar da ita insha Allah gobe gobe xasu je maiduguri har wajen mahaifinta ya nemi yafiyarsa wannan umurnin yusuf ne kuma hardashi zasu. Washe gari haka aka tattaru duka aka wuce maiduguri duk yanda akayi sumayya ta zauna saboda yanayinta amma ina tace da ita za'aje taga kakan ninta da kanwarta shamsiyya, ba yanda aka iyya haka aka tattaru harda Ammar suka wuce maiduguri. Da isarsu suka sauka a gidan sarki yayinda Ammar ya nemi Alfarmar su muhammad su bisa gidan Uncle nasa su kwana, bazasuji dadi ba in sukasan yazo Maiduguri ya kwana a wani wajen, ba musu ramadan da muhamamd suka bisa jin yace musu babu kowa a gidan daga uncle nasa sai matarsa da yarsu babba. Unguwane mai kyau suka shiga cikin wani gida madaidaici mai kyau,sunyita sallama Amma shuru ba'a amsa ba, hakan yasa Ammar nufar kofar falon ganin kamar a bude, aiko yana turawa yaga kofar ta bude, bismillah yama su muhammad ba musu suka shiga da sallama, amma shuru. Macece zata kai shekara 44 zaune akan sallaya a falo ta fuskanci gabar rabin fuskar ta kawai suke iyya hanga zaune take tayi tagumi kana ganinta kasan tayi zurfi a tunani. Girgiza kai Ammar yyi saboda wannan abin ba sabo bane agunsa, abune da ya saba da ganinta a haka, da sauri ya nufi wajen da take ya tabata Aunty!!!!! Da sauri ta dawo hayyacinta, ta dubesa a dakile tace Ammar yaushe kazo? Yanzun nazo kina sana'ar taki ina zakisan na shigo? Shuru ta masa alamu dai batada yawan magana, koh ince damuwa ya maidata haka. Ganin ta masa shuru yasa sa tambayar ta, aunty ina mom? Basanan Ammar kai kad'aine? Ah ah Aunti babba nida abokai nane, yace yana nuna mata su Ramadan dake tsaye, yayinda shi kuma muhammad ya zuba ma fuskar matar ido yana kallonta, kallo irin na tsana, koh shekara dubune bazai manta da wannan fuskar ba. Ai tana kallonsa jikinta ya soma rawa da sauri ta mike tsaye sanye da hijab, tana nunasa da hannu sai kuma ta yanke jiki zata fad.............. Ruqeenjalal *MATAR MAKAHO*