Sashe 61
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sa ruwa ba saboda ba'a tabbatar anga wata ba vegetables ma bata yanka ba tadai sasu a firij ne Bayan Ansha ruwa sumayya sallamar mutane tayi wa'inda bata musu ba ta basu hakuri wasu kuma sukace gobe koh jibi zasuzo Amusu Yau kam saida muhammad ya saya mata matsala 8 tasha tsabar yanda bayanta ke ciwo amma fa gaskiya ta samu kudi bana wasa ba a sallan nan khadija karan kanta kudi ta samu sosai Har dare ba'a sanar anga wata ba haka su sumayya suka kwanta da niyar inba'a gani ba zasu tashi da azumi Aiko hakance ta faru don da asuba ji sukai ana atashi ayi sahur jama'a gobe ba sallah bane Ai yau kam sanin da sumayya tayi ba karamin mutane ne zasu zo ba yasa tana sallan asuba ta tattara boron lallen ta tayi gidan goggo Al'ameen ta bari a d'aki yana bacci tace masa zata saloon gyaran gashi sai tayi lalle tama khadija Gidan goggo taje tayiwa khadija lalle ja da baki itama tayiwa kanta sai dai bata ma hannun dama ba manna masa gam tayi khadija tasa mata lalle akai Lallen su na kamawa ita da khadija saloon suka wuce aka gyara ma khadija gashi don ita kam bata wanke kanta a sefe, kitso khadija ta watsa mata a saloon sai kusan la'asar sumayya suka dawo, kai taga ikon Allah jama'a ne tirem a kofar ta Al'ameen ya rufe kofar d'aki ya fita sukam suna zazzaune a baranda haka ba yanda ta iyya ta hau musu lalle Dayake ana da tabbacin gobe sallah ne yasa khadija had'a musu miyan sallah ta d'aura zobo tana gama had'awa ta juye a robobi tasa a firij muhammad ma ya turo kayan marmari da sumayya tace zata markad'a a blander tayi juice dashi Sai dare sosai mutane suka watse ita da khadija suka kai nikan shinkafa bayan sun dawo suka kwaba, yaukam khadija a gidan ta kwana da sumayya a waje yayanta na d'aki *RANAN SALLAH* yau take sallah ranar farin ciki ga dukan wani musulmi kowa ka gani fuskar sa d'auke da farin ciki hakan take a wajen su sumayya tun asuba khadija ta fara tuyan masa sumayya ma wuta ta hura ta d'aura shinkafa don yau dai ba'a gas koh hot plate za'ayi girki ba Vegetables inta ta kama yayan kawa su green beans green pepper yellow pepper piece cabbage carrot harda k'wai ta d'aura a wuta ga babban kwalban BAMA a zaune agefe karfe 7:30 sumayya sun gama girkin sallah, manyan kulolin ta masu shegen kyau, bata taba bude suba sai a ranan mai guda biyar ne ta zuba shinkafa masa coslow miyan ganye da miyan stew sai manyan manyan kofunan zamani ta juye zobo a ciki d'aya kuma mango juice duk sunyi sanyi har suna raba ta sake maidasu firij, wannan na gidansu Ammar kenan, sauran juyewa tayi a babban kula haka ma miyar duk d'aki ta shigar dasu sanin halin mutanen gidan Wanka tayi ita da khadija suka saka kayansu mai kyau da hijab Al'ameen ma gezena insa sabo ya saka koh sanda sumayya ta hanasa rikewa ita ta kama hannunsa khadija ta rike musu sallaya rufe kofa sukayi lokacin karfe 8:30 sauri suke karsu rasa sallah Suna fita a gidan sun tsaya a bakin titi amma ba keke koh wani keke suka tare a ciki haka suka fara takawa, kamar hadin baki saiga Ammar ya shawo kwana da motar sa packing yayi a gabasu hade da budewa ya fitoh sanye yake da wani d'anyen yadin shaddane mai kyau sai hula da takalmi agogonsa sai d'aukar ido yake. Ashe gwara danayi sauri tun d'azun ina ta tunanin bazan same kuba taima ? Laii Ammar kaine sannu ina kwana? Lafiya muahmmad barka da sallah. Ai ba'ayi sallar ba tukum, muhammad ya basa amsa "Ina kwana"?sumayya tace tana had'a fuska ganin yauma kamar kullum idonsa akanta Lafiya sumayya muntashi lafiya? "Lafiya mungode Allah" Khadija kam kuri tayi tana kallon sa toh a ina tasan bawan allah nan ne kam ta kasa tunawa, a hankali ta ma sumayya magana, aunty nikam a ina kukasan wannan ne? "Habba khadija kin manta mutumin da yazo asibiti lokacin da za'a mini tiyata ya baki kudi ki ban" Oh na tuna na tuna Aunty , ina kwana?tana gaida Ammar kin amsawa yayi hannun muhammad ya kama muje koh ku shiga mota muyi sauri karmu rasa sallah Ba musu dukansu motar suka shiga yaja suka kama hanyan masallaci Allahu Akbar anyi sallah lafiya jama'a kamar kasa suna ta fitoh wa a edi kowa ka gani fuskar sa a washe sai gaisawa ake da juna abin gwanin sha'awa kowa na sanye da sabin kaya sai dai na wani yafi na wani tsada Bayan su Ammar sun fitoh a cikin cunkoson jama'ar dake masallacin, yaso kaisu muhammad gidan su amma sukace ya maidasu gida zasu d'auko abincin da zasu kai gidan nasu Ba musu ya mai dasu gida abincin muhammad ya d'auko musu a kula ya fitoh waje dasu juice taburma ya shinfid'a musu ba kyama Ammar ya zauna sukaci abincin da muhammad sai santi hake don gaskiya abinci ne na kece raini Ta bangaren sumayya abinci ta sassaka a kwanuka ta baiwa khadija ta rabawa mutanen gidan ADARA kowa da plate nasa ta zubawa goggo ma ta kai mata tana dawowa sukaci abinci tukum kafun suka sake wanka lokacin azahar yayi sallah sukayi sumayya ta watsawa khadija make-up sosai khadija tayi kyau tana sanye da dogon riga na zani holland mai shegen kyau sai gyele da jaka tare da takalmi hada agogo da su sarka masu azaban tsada sosai sumayya ta kashewa khadija kudi a sallan nan Ita kam les tasaka sai mayafin ta babba powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki don A matsayin ta na matar aure hakan baidace ba tayi kwalliya ta fita tana d'aukar hankalin maza Al'ameen ne ya shigo duba su sumayya sun gama shiryawa ne Ammar ya dawo yana jiransu "Don Allah yayan khadija ka sake wanka mana ka chanja kayan jikin kan nan"? Meya samu na jikin nawa? "Ba kome amma dai ya kamata ka chanja tunda gidan masu kudi zamu gwara mu kece raini" Kai sumayya kin cika shirme amma dai bara na watsa ruwan shap shap yayi wanka ya fitoh sabon gezena da sumayya ta d'inka masa shiya saka mai tsadane sosai sai takalmi da agogo yau harda glass sumayya ta d'auko tasa masa lias na hannu riga duk ta makala masa, hannunsa ta kama suka fitoh bayan khadija ta rufe kofar Kulolin suka d'auko guda biyar sai jup na juice da zobo duk suka jera a boot na motan Ammar Tunda sumayya ta fitoh idon Ammar ya sauka akanta gabaki d'aya ya tatara hankalin sa Gareta sai kallon ta yake kamar idanunsa zasu zazzago Sumayya kam tun fitowar ta ta lura da kallon da Ammar ke mata kamar maye duk d'aga ido da zatayi sai sun had'a ido ganin yanda duk yabi ya zuba mata na mujiya yasata juyawa da sauri cikin haushi tayi cikin gida Khadija dake kokarin shiga motar ganin sumayya tayi cikin gida yasa ta kwala mata kira, aunty sumayya kin manta wani abune? Sumayya koh juyowa batayi ba tayi shegewar ta ciki da sauri Al'ameen ya fita a motar jin khadija tace masa sumayya ta koma cikin gida yabi bayanta.......... 08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* *1 Gumbar kankana da ayu* 2 *Gumbar ayu zallah* 3 *Gumbar Madara da kwakwa* 4 *Kaza mekwai* 5 *Zabo me zuma* 6 *Kaza me allurai sahihiyar mallaka ba boka ba malam* 7 *Kwallin idonka inadona* 8 *Tauwadar mata* 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245 *MATAR MAKAHO*