← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 104

Sashe 75

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hijab ta saka ta d'auko babban dardumar ta, ta kara shimfid'awa a gefe, ganin taburmar bazai d'auke suba, dardumar ma bai gama d'aukar suba wasu a bakin dakali suka zazzauna. Zama sumayya tayi akan kujera tsugunu bayan ta d'auko sa a kitchen" ina kwanan ku"? Lafiya sumayya, ya maigidan naki? "Lafiya" kawai sumayya ta amsa kamar irin bata ganesu innan ba. Yar nan kice kika dawo haka gaskiya aure ya karbeki sosai wallahi, Hajjo matar babuji tace "Umm ikon Allah kenan ai hajiya, sai ya baka abinda wasu basu so ba"amsar da sumayya ta bata kenan tana cigaba dacin kosanta kamar irin taga sabbin fuskar nan. Jikin dada yayi sanyi, ganin halin koh in kula da sumayya ta nuna musu, da ace dane koh makaranta sumayya ta dawo inta ganta saita mata oyoyo ta rungume ta, suna wasa da tsokanar juna irin na jika da kaka, amma yau kallon banza sumayya ta mata, kawalli yaufa wuni muka zo miki, gabaki d'ayan mun nan munyi kewar ki yar mu. "eh dole kuzo mini jaje ai, tunda kunsace mijin hankalin ku ya kwanta, abinda ake so a gani dai insha Allah baza'a gansa ba, koh xaku mutu haka zaku ganni ku barni, don Mu Allah muka rike" tana magana tana shan kunun ta kamar ba ita ke magana va Miemie ce ta mike, habba sumayya wannan wani irin banzar magana ne, ya zaki bude baki kina fad'awa hajjo da dada irin wannan magana? "Keee mimi, ban kasa dake ba karki kuskura ki kwasa, dasu nake babu ruwan ki a maganar nan, kona karta miki layin rashin mutunci" Eyeeee lallai sumayya, yaushe kika koma mara kunya haka? "Kubra kenan rashin kunya ai dole na koya, koh kin manta gidan da nake ciki ne"?sumayya ta bata Amsa Habba sumayya wannan ba halinki bane, don Allah kiyi hakuri mu da kika gan munnan bamuzo don kara bata miki rai bane, munzo gyara abinda muka bata ne, aunty husna surkuwar uncle Abubukar tace. "Keee Husna karki kuskura kisa baki a maganar nan, ina ganin mutuncin ki, sannan kina maganar ku gyara abinda kuka bata, wani abin kuka bata da har xaku gyara?aini koh sanin ku banyi ba" Mamakine ya cikasu sumayya ta zama yar tasha, sun shiga uku, yarinyar da koh zagin yara bata iyya ba yau harda zagen manya haka. Sumayya dafa iyayen ki maza muka zo gidan nan suna waje. Kallon mammu sumayya tayi, jin abinda tace"meya kawo ku gida na kuma gayya guda haka"? Munzo ne akan auren ki da yaron nan MAKAHO, tundadaman baso kike ba mumuka miki dole, sam yanzun bamu lamunce ba takardan ki xai baki baziki zauna da misk................. ************* Muhammad dai yau shida indo , zasu cikin camaroon tallan nono, ta uzzura masa yau saiya rakata, dayake shima yana son zuwa cikin birni yasa sa binta, yau gidado ne kawai yaje kiwo, bappa da matar gidado wance cikin ta ya tsofa haihuwa yau koh gobe. Cikin Cameroon suka shiga, indo na tallan nono shikam sai kallon gari yake abinsa, basu dawo da wuri ba sai yamma lilis suka dawo. Bappa ne xaune a bakin masallaci yayi tagumi, su Al'ameen suka same sa, gaidashi sukayi suka wuce cikin gida. Da dare bayan isha'i Bappane da iyalansa zaune a tsakar gida harda Muhammad, hira ake sosai, tunda muhammad yazo gidan baitaba ganin sun zauna haka ana hira ba, harda inna da matar gidado lantana, Bappa bakajin dadi ne? Gidado lafiya ta klau, bansan meke faruwa ba tunda na tashi yau nakejin babu dadi a jikina. Toh Allah ya kyauta bappa, inna tace tana kallon sa don tun safe itama ta lura akwai abinda ke damun sa. Ameen Talatu. Amma bappa wani irin abune yake damunka haka? Gidado mubar zancen nan kawai bashi da Amfani. Kamo wani tadin akayi, sai hira ake muhammad nad'an saka baki kad'an kad'an in aka sakosa a zancen. Sosai yau gidan bappa aka sha hira sai chan dare, muhammad ya musu sallama, kwanciya yayi bayan yayi Alwala yayi addu'ar bacci, haka kawai yake jin kirjinsa na bugawa, kwanciya yayi, yayi likimo a gado,har bacci ya d'auke sa. Ta bangaren su bappa, sallama sukayi da juna bayan wucewar muhammad don shiya fara tashi, kowa yaje ya kwanta, Amma dai jikin su a sanyaye, yau dai indo taki kwana ita kadai a dakin ta, tace da innar ta zata kwana, dole tasa inna komawa d'akin indo tabar bappa a dakin sa. Da misalin karfe 1:14am agogon cameroon, Al'ameeen ya farka da salati jin ihu tako ta ina da salati, gari ya kaceme da hayaniya, karan yara da matane kota ina, ga ruwan bindigogi dake tashi, da sauri ya dirka daga kan gadon jin inna na salati da karfi tana wuta wuta jama'a cikin yaren fulatanci ................. Fan's naga messenge inku ta PC nagode Allah yabar kauna wa'inda bamma reply ba sumin Afuwa abinne da yawa *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibr ahim* Page7 Fita yayi a d'akin da gudu yayi waje, jikinsa rawa ya soma ganin An cinnawa gidan bappa wuta, ga sauran gidaje duk wuta ke tashi da karan mutane da guje guje. Gidado ne ya fitoh d'aki rike da matar sa, da tashin hankali yasa ta nakuda, ya kalli bappa dake xaune shuru, babu alamun tashin hankali a fuskar sa hakama babu alamun kwanciyar hankali. Inna ce ta mike da sauri ta isa garesa, hannun lantana ta kama wance ke kokarin faduwa,gaskiya haihuwace gadan gadan fa bappan gidado musan abinyi. Hanyar wajen gidado ya nufa hannunsa d'auke da wuka sharbebiya. Kai gidado ina zaka?koh bakajin abinda ke gudana a waje ne?muhammad yace cikin tsananin tashin hankali. Kaga ku zauna a ciki bara na fita, mu munfi karfin ana kashemu, muna buya sai dai a fito a gwabza, yana magana yana kokarin barin gidan. Kaiiii gidado, fitar da zakayi ba shine mafita ba, kanada tabbacin inka fita zaka dawo ka samemu a raye?wuta fa aka kunna wa gidan nan, mafita zamu nemawa kan mu, na fita a garin gabaki d'aya. Allah ya sauwaka, mugudu mubar mahaifan mu, da Arzikin mu. Gidado kabi abinda yaron nan ya fad'a, don yafika gaskiya nakuda matar ka take, kamata yayi ka fitar da ita, ga indo can sumar ta biyu,inna tace tana nuna indo dake zaune a gefe kamar ruwa ya cita. Shuru gidado yayi ya tsaya sosai jikinsa ke rawa , kowa yasan yanda ran fulani yake baci in an tabo musu dukiya ba sauki, gaskiya inna saidai kuzo kutafi da ita kaima muhammad ka bisu, mukam zamu kare shanukan mu, yayi maganar yana tsinka zanar bayan gidansu wanda wuta bai iso gunba. Soyayyar da ka iyya jure shadi akanta, da soyayyar tsakanin uwa da d'a, bazaka iyya sadaukar da arzkinka ba, gidado ku rayu tare? Mikewa inne tayi, gidado ya ciccibi matarsa da tiyo ya fashe ruwa yana zuba, da gudu indo ta rike hannun inna, muhammad ma binsu yayi a baya, har sun shiga bandaki kafun suka tuna da bappa yana bayansu, juyawa dukansu sukayi suna kallon sa har lokacin bai motsa ba. Inna ce ta dubesa, Bappan gidado yakana zaune kazo mu tafi baka ga halin da yarinyar nan take ciki bane? Kuje kawai Allah ya tsare hanya, ni bazan iyya gudu a rugan mu ba. Habba bappa yanzun kafison ka zauna azo a kashe ka, hakan bai dace ba koh a addinan ce, kana da damar kare kanka, ka bari a kashika, muhammad ya karasa maganar yana karasowa kusa da bappa. Don Allah bappa y'an dillo, indo tace tana kuka. Girgiza kai bappa yayi, kuyi hakuri bazan iyya zuwa ba. Muhammad ne ya dube gidado, kaga gidado ku tafi da inna, lantana da indo , ka fara fitar dasu, muna zuwa da bappa. Sanin taurin kai da kafiya irin na bappa, yasa gidado da inna suka fita ta zanan bayan gida, harda lantana data gama galabaita da indo. Zama muhammad yayi kusa da bappa sosai zuciyar sa ta tsinke, ganin yanda wuta yaci rabin gidan yanzun ma wani irin turiri da rad'adi yakeji a jikinsa ga hayaki, bappa don Allah badon niba kazo mu tafi a rugan nan, rayuwar ka tana da matukar Amfani wa Ahlinka, kasan wani irin hali zasu shiga in aka waye gari baka?akan iyya rasa dukiya, wata rana su dawo, Amma ba'a taba rasa uba wani ya maye gurbinsa har Abada, kama iyalinka adalci ka rayu dasu koh ba kome zasu walwala koh ba shanukai, akansu rayu bakai ba dukiya. Kuka bappa ya fashe dashi, babana bazaka gane bane yanda abin yake, akwai zafi azo a same ka har gidan ka a kwace maka dukiya, a kwace maka muhammali, asaka gudu kamar barawo ina sukeso muje, irin wa'innan mutane, sune sukayi sanadin iyaye na, shekara talatin baya, mu kullun cikin zulumi muke bamuda sakat? Kayi hakuri bappa, rayuwa tafi kome muhimmanci ita d'ayace, kayi hakuri mu fita anan, yana maganar yana kama hannun bappa ganin jikinsa yayi sanyi, kamasa yayi suka nufi bayan gidan, suka fita ta zanan gidan. Da ido bappa yake bin rugansu dashi, ganin gawawwakin fulani cikin jini manya da yara, kota ina hayaki ne. Tafiya suke kamar wasu barayi a hankali a hankali, suna bin ciyaye kamar a mafarki muhammad yaga yan ta'adan nan sanye da kakin sojoji ga bindigogi manya manya a hannunsu, kafun ma su buya tuni sun gansu, ai da gudu muhammad ya kama hannun bappa suka nausa daji, da gudun tsiya, suma suka rufa musu baya. Gudu muhammad yake da bappa suma suna binsu a baya, bappa ne yayi tuntube ya fadi tim, da sauri muhammad ya dakata kokarin tayar da bappa yake, Amma bappa ya kasa saboda ya buga kafarsa mai ciwo a dutse, ka tafi kawai yaron nan ni inaji lokacina yayi, Allah yamaka Albarka ya sadaka da ahlinka lafiya, sai wata rana.bappa yace. A karon farko muhammad ya sake kuka mai karfi, harga Allah a d'an zamansu da bappa jinsa yake kamar mahaifinsa, don Allah bappa karkace haka, bara na d'agaka, ciccibar bappa yayi, yana gudu kamar kiftawar walkiya yajisa a kasa dagashi har bappa, mummunan buguwa sukayi muhammad saida tsakiyar giransa ya tsage, saiga jini bappa ma gwuwarsa ta kwarzane sosai. Kafun ma ya mike tuni yan ta'adan nan sun kewaye su, d'aya daga cikin sune ya taka kafar
Chapter 75 · 0% Book details