← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 104

Sashe 13

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

upstairs shima dakuna goma Sha biyar ne Hawa na uku ma haka,Amma duk yawan d'akunan gidan munan falon mu dayane shine falon kasa, Wanda Koh a Hawa na uku kake kana hango falon, d'akunan kasa na samarine sai kakarmu dake zaune dasu a kasan Wai tana saka musu ido injita, dakunan Hawa na biyu na iyaye ne Hawa na uku shine na Yan Mata da d'akunan yaran gidan da sukayi aure maza,suna zaune da iyalansu ,.. duk yanda Zan fasalta muku gidan mu saifa na rage wani abin, Kaf gidan mu da colour D'aya aka kawatashi da white colour sai surkin baki Kama daga kujiru labule Abubuwan da aka kawata gidan kome farine daga sama har kasa abin sai Wanda ya gani, Jama'ar gidan mu duk Muka samu a falo da yake yau weekend ne ba aiki ba makaranta kowa na zaune wasu na kallo wasu na Danna waya wasu na Danna laptop yara na wasa wasu abinci suke ci ganin mu yasa dukansu barin abinda suke suka zuba Mana ido Kamar yau suka fara ganina,tunda Khadija ce Basu sani ba, Idanuna ne ya sauka a Kan kakata dake zaune tanacin kefe sai uncle's nawa dake zazaune wasu na cin abinci wasu na Hira wasu na duba takardu, wani abune ya tsayamin a makoshi Mai kamada Takaici sun aurar Dani Basu damu da rayuwar da nake ashan ba gasuna suna zaunen su Kamar Basu San wata Sumayya da aka bawa MAKAHO ba Basu neme sanin ya rayuwa ta kare ba waima me dalilin auran Dani ne tunda gasu Aunty miemie sun girme ni nesa ba kusa ba Amma saini kadai aka aurar auren ma da MAKAHO ba lafiyaye ba,Koh don anga mahaifiyata Bata gidan ne Kai Koh mahaifiyata Bata gidan ai ubana nanan Koh da kowa zai nuna Mini kiyayya dada zata sassauta tunda ita ta haifi babana amma Ina abin ba sauki, "Ina kwana dada,"nace Ina zama a cikin Daya daga cikin kujirun falon, Toh matan miskinai ne agidan namu yau Koh idonane,? Ah ah Kaka ba idon ki bane kinsan azumi ya karatoh anzo amsan zakkah ne, Hhhhhh Kai miemie baki da dama Amarya ce fa tazo ganin gida mutun da gidansu kece yazo karban zakkah,kubra ke fada tana dad'a tunsirewa da dariya Waiku yaran nan wasu irin Yan iska ne me yasa baku da mutunci shegu kawai ai gwara ita tayi aure Koh? Keee koh miskini kin samu yazo wajen kine da sunan aure, a cikin ku waye ta samu miskinin na zuwa wajenta,Yaya Abdu ya fada ransa a bace, Ai itama ba zuwa yayi ba lika Masa akayi,miemie ta basa amsa,.. Rufe mini baki karna ci ubanki Yar iska Abdul yace Yana mikewa, Ai duk laifin dadane Sam bansan me yasaba, Dada (kakar mu) itace babba Amma ita ke sasafo Mana bala'i yaya kabiru yace Yana maijin takicin ahlin gidansu, Abubakar kanajin abinda shegen yaron Kan nan kabiru yake shimin mutunci kayi shuru kana kallonsa,,, Kiye hakuri Dada Kai kabiru zanci kaniyarka fa inka sake shiga abinda ba ruwanka uwarka aka zaga Koh me da zaka saka bakinka a ciki, Mikewa Kabir da Abdul sukayi sukabar falon, Ganin yanda aka Mai Dani Kamar kashi ba Wanda yabi ta kaina kowa na Harkan gabansa Ganin Banga Abie na a cikin falon ba yasa na mike nayi hanyar upstairs na nufi d'akin sa nabar Khadija a falo wance ke rakube Kamar ace kitttt ta ruga, Bude kofar d'akin nayi nasa kaina na shiga Abie nane zaune a kasan tiles Yana duke da Kai sai momy (yadikko na) zaune a bakin gado daga Gani dai magana suke.................. *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book Page 1 Bayan fitar Ammar Khadija ta kirga kudin dubu goma ne,Mika min tayi, Aunty ga kudin "Ajjye Khadija in yayanki yazo ki basa tunda shike fama da zirga zirgan asibiti" toh Aunty ta bani Amsa tana aje kudin a cikin ak'watin Kayana, Al'ameen na fita daga asibiti da kafa ya koma har gida Dayake akwai sanda in Kuma yazo titi sai ya Kama yara su tsallakar dashi Yana Isa unguwan su(sintali) wajen shagunan bakin titi ta inda yake sai da mangoro a bakin su, Shagon malam shu'aibu ya fara zuwa don shine yafi masu shagunan abin arziki sosai alayin da sallama a bakinsa ya shiga shagon, Assalamu alaikum malam shu'aibu Waalaikumu salam Mai mangoro ne? Eh nine malam shu'aibu barka da jama'a Barka dai lafiya Kam Naga yau tun safe danazo bude shago Naga hulbairon ka a rufe dazun na aiki yaron gidana ya karbo mini yako yake fadamin baka nan? Eh wallahih malam shu'aibu iyalina ne ba lfy jiya na kaita asibiti, Allah sarki ya jikin nata? Da sauki Daman nace bara nazo ka taimaka mini da kudi dubu hamsin za'a Mata aikine appendix ya kumbura a cikin ta don Allah ka taima kamin, Kutt lallai ma a karnin nan da kowa ke takai takai Ina Zan iyya daukan kudi har 50k na baka da sunan bashi, bayan anyi operation in Ina zaka samu kudina ka biyani, gaskiya bazan boye maka ba ni nan Koh biyar bazan iyya baka ba banaji ance Yar masu kudi aka aura maka ba me yasa danginta bazasu Mata jinya ba tunda sunsan baka dashi Daman suka baka ita Shikinan malam shu'aibu na gode, ya fada Yana fita ba tare da ya basa amsar tambayar Saba, D'ayan shagon Al'ameen ya shiga shagon gwanja bayan sun gaisa shima ya rokesa Koh zai samu bashin kudi Amma Kai dai wallahih D'an rainin wayo ne ya Ina Saida kayan Miya zakace na baka dubu hamsin duk kayan shagon nan aka sayar Ina zaiyi dubu hamsin, Haka yayita bin shagunan makwantansa Amma ba Wanda ya basa Koh sisi wasu kamma da bakar magana suke binsa dashi, A haka ya iso shagon Haladu shima yace baidashi,. Wajen bairon mangoron sa yaje ya bude ya tataba mangoron rabi duk sun lalace saboda yini da sukayi a rana Kuma a rufe, zabe masu kyau yayi Yana, D'auka yana sawa a k'wando ya shiga shagon Haladu dashi, Yana cewa, don Allah Haladu Koh zaka sayar mini da mangoro na zanje na zauna a asibiti na kwana biyu daidai Matata taji sauki Gaskiya bazan iyya sayar maka ba sai dai na saya kawai na sayar Nima na samu D'an riba, Ba damuwa Al'ameen yace Masa .....Nawane mangoron? D'ari takwas da hansim .....Zan baka dari biyar don Naga wasu sunyi laushi? Ba damuwa Allah ya saka musu albarka ......Ameen Kudin Haladu ya basa ya karba gida ya shiga ya bude kofar, da yake ya karbi key a hannun Khadija wanka yayi ya saka kayansa Jin ana Kiran la'asar yayi Alwala ya lalube takalmin Sumayya ya fita dashi a hannunsa, masallaci ya tafi yayi sallah ya wuce asibiti duk zuciyansa ba Dadi ya rasa wajen wa zai tinkara da zancen kudi,, yasan Koh mutuwa zaiyi Yan gidansu bazasu taimaka Masa ba bare Sumayya matar sa, ***Muna nan da Khadija har la'asar sallah mukayi dukan mu nurse tazo ta mayar mini da laidar ruwan a hannu na, Na kwanta baccine ya dauken nabar Khadija na zaune, Ya iso asibitin da sallama ya shigo dakin Khadija ta amsa masa. Sannu yaya ka dawo? Eh Khadija Toh yaya ka samu kudin? Wallahih Khadija sai addu'a naira 500 ne kadai na samu Amma yaya ya kamata ka sanar da Aunty gaskiya don wallahih Yaya Ina Jin tsoro kaga ance appendix in ya kumbura fa tunda Allah Bai baka ikon samu ba, ka fada Mata ita sai ta biya? Toh Khadija wallahih inajin kunya a matsayina na mijinta na kasa biya Mata kudin operation don samun lfyr ta, Habba Yaya karfa ka manta Allah yaga zuciyar ka baka dashine Kuma ba abin kunya bane tunda itama tasan baka dashi, Suna cikin Hira na farka a gigice Jin wani irin mahaukacin ciwon ciki ya tasarmin " Innalilahih wainnailaihir rajuun wayyo Allah na cikina" Subhanallah Sumayya cikin ne Al'ameen Daya Mike cikin tsananin tashin hankali yake lalubarta , Khadija ma da saurin ta ta iso ni,sannu Aunty take fada idon ta ya jika da hawaye *****Nikam.na kasa Bata amsa kuka kawai nake hankali tashe Khadija tashi kije ki Kira doctor eiiii sauri Toh yaya tace tana mikewa da saurin ta Al'ameen Kam hannun Sumayya ya Kama sai sannu yake Mata a hakan likita yazo ya sameta a halinnan Da sauri shida nurse suka rufu a kanta tare da K'ura Khadija da Al'ameen waje,allurai sukai Mata harda na bacci lokaci daya bacci ya dauke ta, Khadija da Al'ameen na tsaye a bakin kofa likita ya fitoh ya kira su zuwa office, Malam Al'ameen majinyaciyar ka tana cikin condition Mai muni ya kamata ka samo kudin aiki nan da awa uku ba wallahih kome zai iyya faruwa, Innalilahih wainnailaihir rajuun kawai suke fada, Suka mike zuka fita a office in Khadija Kam kuka ta fara abin Yama Al'ameen yawa ta Ina zai fara anya zai yafewa kansa kuwa in yar mutane ta mutu ata dalilin rashin kudin aikin da Bai samo ba, Yaya ya kamata Aunty tasan abinda ke faruwa muje ka fada mata ta Kama hannunsa sukayi dakin Suna shiga suka samu Sumayya na bacci .......... Yaya Ammar innan yazo baka nan ya bawa Aunty kudi Amma Taki karba tace na baka Allah sarki Ammar yazo ne? Eh yaya kana fita Yana shiga, yace ma Wai Daman Yaso kuyi sallama tafiya ne ya kamasa, na gaggawa, Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari Yan kiyaye sa aduk
Chapter 13 · 0% Book details