← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 104

Sashe 27

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kallonsa harya ido wajen kujiran Yana kokarin zama mini akan kafafu da sauri na mike zaune na nade kafafun nawa"yanzun zama mini zakaye akan kafafu daban d'aga ba ka karyamin kasusuwa Koh me"? Au kafarki nagun ne?ya tamaya "Kaji nace maka Ina kwance sannan kazo zaka zauna akujiran" Sanann yanzun kana tambaya ta Ina kwance ne" Sorry yace Yana zama a inda ta d'aga kafartata, Sumayya!! Na'am Sumayya Ina Mai baki hakuri nasan tabbas band'auke Miki nauyin da ya rataya akaina a matsayina na mijinki b Ina Mai neman afuwanki wallahih Sumayya bani dashine shiyasa yau kwana biyu ban baki kome ba "Ba kome ai nasan baka dashin ne sannan ni don na samu na sai Mana abinda zamuci ai ba kome wata Rana Allah zai baka kaima sauka sai mana"nace Ina kallonsa Nagode Sumayya Allah ya saka mini da alkhari "Ameeeeeen Daman jiranka nake kazo muje mu duba jikin khadija kasan yau ban samu zama ba tun safe" Amma bakin gaji ba ki bari gobe Mana sai muje "ah ah muje dai, gobe ma akwai masu zuwa kwalliyar bud'an Kai dana dinner har dare Ina busy" Ok toh yace Yana mikewa Hijjab nawa har kasa na d'auka nasa da karamin purse D'aukar sandar sa yayi ya tsaya Yana jiranta a kofar d'akin "Yau fa bazaka tafi da sandar nan ba atoh" Akan me? "Akan zaka fita Dani" Ke asuwa? "Asu masu ido" nace Ina kamo hannunsa ba musu ya aje sandar Tsaya na rufe kofar, yace Sake Masa hannun nayi ya rufe mana kofar,Yana rufewa sake kama Masa hannun nayi Muka fita a shashen mu Tsakar gidan kaman ba dare ba duk jama'ar gidan na zazaune wasu a taburma wasu a kujira,nidai ganinsu baisa na sake hannunsa ba Ke fasuma Wai me kika ganine a tare da miskini kike zaune dashi kamar auren tsafi,d'aya daga cikin Yan gidan Tama Sumayya gogar zana Ai toh auren tsafinne Mana inba haka ba mutun da arziki ya zabi Talauci,fasuma ta bata amsa.. Nikam ban tanka musu ba Donna fahimci Yan gidan nan sai shiriyar Allah don mutum Kam sai wani ikon Allah,tunda mutuwar inno Bai saka sun tsakaita da dambe da cacar baki ba ai hukuma ma bazata iyya dasu ba, kamar yanda Al'ameen yace Waje muka fita,Ina rike da hannunsa muna tafiya,duk.inda muka wuce sai an bimu da kallo bare ga mazan unguwan da Basu sanni ba suna Daijin kwatance a bakin matansu,duk.madalisan da Muka wuce bin mu ake da kallo ga hasken sola ya haska Koh Ina, a hakan har muka shigo layin su Goggo Amina, na saima Khadija kankana da lemo, da sallama a bakina na shiga gidan,don shi yace bazai shiga ba sai ammasa iso "Assalamu alaikum" Waalaikumu salam barka dai Sumayya sannu da zuwa Goggo Amina ta fad'a tana shimfid'a mini taburma "Yauwa Goggo Ina wunin ku" "Lafiya Alhamdulillah Sumayya kece da Daren nan" Eh Goggo tare muka taho na fad'a Ina sunkuyar da Kai,(Wai kunya Shine ya tsaya a waje ai aikin muhammad kenan kamar gidan bakonsa ne,kice ya shigo "Toh Goggo" nace na koma kofar gida "Ka shigo"nace Ina juyawa Toh kin hanani rike sanda sanna kin tafi kin barni "Yanzun bazaka iyya shiga da kanka ba"? Eh bazan iyya ba Uhmm kawai nace na Kama hannunsa da yake dare ne koma ba NEPA sai da muka kusa isa kusa da Goggo na sake Masa hnnu, Zama nayi a taburman shi Kuma ya zauna a kujira, Goggon Ina wuni? Lafiya Muhammad hala kunzo duba khadija ne? "Eh wallahih Goggo shuru yau najita bata zoba shine muka taho mu duba Koh kan nata ne har yanzun"? Wallahih Sumayya ta fad'amin abinda ya faru,zaman gidan mu sai hakuri kuma.ku Kara hakuri kinji kome zai wuce "Ba kome gaggo" Aiko khadija kam.na kwance a d'aki yau Koh fita batayi ba Kai na ciwo ga zazzabi duka,Daman khadija akwai raki ku shiga ku duba ta,inji Goggo Mikewa mukayi, muka shiga d'akin Khadija ce a kwance tana bacci, Fita mukaye don bamu tashe taba "Toh Goggo zamu tafi ga wannan ba yawa Allah ya Bata lfy wannan Kuma 5k ne yayanta ya bani Wai na baki koh gobe saita je asibiti"nace Ina aje laidan da na shigo dashi,hade da mikawa Goggo kudin Wai Al'ameen d'awainiyane har haka daka bare Koh chemist taje goben sun Kara Mata wasu magani Koh na 200 ma Al'ameen Kam mamakine ya kamasa yaushi ya samu kudi har 5k da zai bawa khadija,Amma Sumayya tace in jisa, "Goggo taje asibitin dai zaifi tunda jiya chemist in ta fara zuwa ba'a dace ba"na fada Ina taka kafar yayan Khadija Jin yayi shuru baice kome ba Am am gaskiya ne Goggo ki karbi kudin inyaso taje asibitin Amma kudin yayi yawa ai muhammad Ba wani yawa Goggo In change ya rage ku rike zai D'an rage muku wasu Abubuwan Kai Amma mungode muhammad, Sumayya Allah ya saka "Ameeeeeen" har muna hada baki dashi Fita mukaye daga gidan Goggo Amina kafun na rike Masa hannu Jin tayi hanyar titi ba hanyar gida ba yasa yace Mata Sumayya Ina zamuje koma bafa nan bane hanyar? Sai da Kai zanyi nace Ina tare keke napep............ *Gaisuwa na musamman da fatan Alkhari ga special FAN'S na MATAR MAKAHO Naga sakonku, Allah yabar kauna,Ina godiya* *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* *Contact them vie* 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO*
Chapter 27 · 0% Book details