Sashe 50
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Toh da tsoron ka zanji" Amma dai k'wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba "Nikam naji, k'wan maggi ga Albasa doyan kuma bai soyu ba, tie in kuma sugar baiji ba" Hannu yasa ya d'auke plate in gabanta da cup in tie in ya rike a hannunsa "Yaya haka kuma"? Ki miko mini kudi inje in sai miki abinci amma badai wannan zakici ba kowa ma ya hakura Almajiri zan kira na bawa, karasa maganar yayi yana shirin fita a d'akin Da sauri sumayya ta biyosa hade da kamo rigansa"dan Allah yayan khadija ka aje abincin mana waikai bakasan wasa bane?wasa fa nake maka" Wasa koh?toh ni da gaske nake kuma sakar min riga karki yaga "Habba don Allah yaga riga sai kace wata mai farashunan mayu" Toh waya sani "Yasan me"? Sakarmin riga hajiya "Ayya ka bani abincin mana wallahi wasa nake doya yayi d'adi haka tie ma k'wai innan inda kasan dafin Turai" Mika mata plate in yayi shima ya koma ya zauna abinci suka cigaba daci Bayan sun kammala ci yaukam ita ta d'auki kwanuka, bayan ta kaisu waje brush tayi shikam Aswakin sa ya d'auka ya goge bakinsa d'akin suka koma kayan bacci sumayya ta saka rigane da wando cotton mai laushi da socks na sanyi a kafarta, jin an fara yayyafi yasa Al'ameen fita waje ya tattare musu ruwa shima kayan baccin sa da sumayya ta sai masa ya yasa Sumayya gado tahau iyafis ta d'auka ta jona da wayan ta ta manna a kunne tana kallon film a ciki Shima bayan ya gama shiryawa d'akin ya rufe ya hau kan gadon, tattaba kan gadon yake har yaji ya tabota kwanciya yayi kusa da ita yasa hannu ya zame hular kanta Hannu tasa ta cire kunne d'ayan ta makala masa a kunne Kwanciya yayi akan filon da take gabaki d'aya ya nutsu yana sauraron abinda ke kunnensa, sai kuma yasa hannu ya taba sumayya hade da kiranta, sumayya! "Na'am" Uhmm Amma wannan indi'an film ne koh? "Eh..ya akayi ka gane"? Muryansu mana duk da Turanci suke magana amma dai sai kiji suna maganar sari koh bauta "Gaskiya ne kasan sunan film in"? Ah ah "this is fate, watoh kaddarar Rayuwa na Arewa 24" Oh film in karam koh? "Eh shine ma ke magana yanzun" Ai da sauri ya zare abin kunnesa tare da sa hannu ya zare na sumayya, kinsan Allah bazaki kalli film innan ba "Ikon Allah akam me bazan kalla ba"? Nidai kawai bazaki kalla bane. "Toh me kakeso na gani"? Wani film banda wannan "Uhmm nikam gaskiya shi nakeson kallo" tace hade da karban abinta ta mayar kunne Da sauri ya fizgo abin gabaki d'aya ya had'a da system in yana kokarin sauka akan gadon Da sauri sumayya ta cakumosa baya hade da kokarin karban system in Duk yanda taso kwatar abinta abin yaci tura duk inda tayi saiya zillar da hannunsa karshe ma hakura tayi takoma gefe tana maida numfashi Tashi yayi jin ta kwanta, zuwa yayi ya aje system in akan kujera, ya dawo ya kwanta abinsa Ganin ya aje yasa ta saurin mikewa zaune cikin azarbabi take kokarin sauka ta gefen kadon a hankali, tana sauka saboda matsen d'akin yasa dole saita biyo ta bangarensa kafun taje kan kujera, a hankali take tafiya Shikam tun tashinta zaune da saukarta duk a kunnensa shuru kawai yayi yana son ganin gudun ruwanta Tazo daidai dashi har zata gifta a bazata kawai taji ya fisgota baya ta fad'a kansa Kokarin tashi take, ya sake maidata, wai sumayya meyasa ne bakijin bari sam "Me nayi kuma"? Yanzun ina zaki? "Waje zan fita" Me zakiyi a wajen? "Fitsari mana koh an hana fitane in aka kulle kofa" Jin amsar da ta basa ya saka hannu ya mannata da jikinsa sosai kamar zai maidata ciki Karan shagwaba ta sake da karfi"wayyo" Ke menene haka saikin tara mini jama'ane "Toh ba kaine ka matseni ba" Toh ai ke ince bakiji koh kad'an kannan naki taurine dashi fa Eh naji kaina taurine dashi kuma ni ka sakeni fit......... Bai bari ta karasa ba kawai ya manna bakinsa da nata sosai yake kissing inta yana dad'a matsota garesa kamar zai maidata ciki A hankali tasa hannu ta kama kansa da karfi ta danke gashin kansa masu yawa sosai, hade da ajiyar zuciya Washhh ashhh kawai Al'ameen yace bayan ya zame bakinsa a nata, hannu yasa ya kamo hannunta data rike masa gashi ya d'aura a kirjinsa, da sauri ya maida bakinsa cikin nata Sosai yau sumayya da Al'ameen suka farantawa junansu duk da tafiya tayi nisa sumayya ta copsa Shi kuma Al'ameen tsoro. *RANAN MONDAY* Yaune fa hajiya khadin Goggo zata makaranta jiya koh baccin kirki bata iyya ba, da sassafe ta tashi tayi wanke wanke shara kafun 6:00 har tayi wanka dumamen da goggo ta duma shi taci, uniform nata tasa fari kal wando da hijab harda riga duka farare ne socks ta saka fari ta d'aura bakin d'an kwali(kallabi)ta zura hijab, sandal inta da Aunty ta tasai mata kala biyu d'aya ne d'aya sandal, in ta d'auka bakine shima don a dokar makarantar baki da fari suke so, tasa a kafarta sai agogo shima baki turare ta fisa fuskar nan washe kamar gonan Auduga takema goggo sallama hade da d'aukar school back nata shima baki mai kyau, ta fita a gidan Sumayya da Al'ameen ne a kitchen suna girkin karyawa kamar kullum yauma hakan take watoh ana aiki ana fad'a Assalamu Alaikum "Wa'alaikumus sallam, yan makaranta" Kai Aunty ina kwana? "Lafiya khadija harkin shirya gaskiya ne Allah yasa hakan ya d'aure banda littin" Ameen Aunty, ina kwana yaya? Lafiya khadija harkin shirya? Eh yaya na shirya D'aki sumayya ta shiga naira 200 ta d'auko sai drinks d'aya da goran faro d'aya ta fitoh "ungo khadija wannan kudi yayanki ne ya bada na baki koda zaki zo ya fita ashe da rabon zaku hadu ma kihau keke sauran d'arin saiki rike a hannunki ga wannan kuma kisa a school back naki kinji, banda kawayen banza banda abota da maza kinga makaranta ne da Christian sukafi yawa sosai kuma benchi d'aya ake had'a maza da mata don haka babu ruwan ki da yaran Christian abinda ya kaiki shi zakiyi kinji ki maida hankalin ki akan abinda ya kaiki Allah ya tsare mana ke" Hannu khadija tasa ta karbi kudin da drinks in hade dama sumayya godiya, yaya na tafi Al'ameen kam ya rasa ma me zaice da sumayya sumayya Alkhari ce garesa matar rufin asiri, toh khadija saikin dawo kindaiji abinda Auntin ki tace miki koh? Eh yaya.. Adawo lfy Bayan fitar khadija sumayya kam kitchen ta koma taci gaba da aikin ta Al'ameen na tayata Assalamu Alaikum "Wa'alaikumu salam" sumayya ta amsa tana fita a cikin kitchen in da sauri jin muryar wance ke sallamar Aiko itace da mamaki sumayya ta bita da kallo, Al'ameen ma da sauri ya fitoh a kitchen in jin muryar me sallamar "Lafiya" sumayya ta tambaye ta Eh lafiya daman n................ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sayanzunshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 IG @umsadincense *MATAR MAKAHO*