Sashe 66
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
lafiya, mijina har abada bazan taba barin kaba harsai ranan da na daina numfashi in Allah ya yarda. Toh bakice kina sona ba? "143" Meyake nufi? "Kayi tunani mai zurfi, wanka nakeso nayi nayi sallah, rana yayi ka kaimin ruwa bayan gida" Toh yace yana saken ta, boket na ruwan zafin ya d'auka, yana tafiya har lokacin idanunsa zafi suke masa, kuma bai bude suba. Bayan ya aje ruwan, dawowa yayi ya ibi na sanyi a wani boket in daba. Sumayya dake zaune har lokacin a dakali"ga baf a kitchen ka kaimin ban d'akin"tace masa Haihuwa kikayi ne wai gimbiya? "Mutuwa nayi" Insha Allah ba yanzun ba, yace yana d'aukar boket in, kaiwa yayi band'aki yana fitowa, sumayya dake kan dakali ya ciciba yayi bayan gida da ita, ajeta yayi. "Toh ka fita mana, waima menene naga ka rufe ido yaukam kaki budewa"? Idanun ciwo suke mini, yau kamar borkono a ciki. Uhmm kawai sumayya tace tana had'a ruwan wanka, duk yanda taso muhammad ya rabu da ita ki yayi shiya taimaka mata tayi wanka, ya d'auko mata wani towel in, ta d'aura ruwa ya cika a buta ya bata tayi Alwala. Shima wankan yayi ya fita a d'akin har lokacin idanunsa a tamke, yayi Alwala yashiga d'aki, zuwa lokacin sumayya tayi sallah tana zaune tana lazimi. Bayan ya idar da sallan, a hankali yasa hannu ya shafo sarkan wuyansa da mamaki ya kalli sumayya, gimbiya yanaga sarka a wuyana kuma, ke kika d'auko koh? Da mamaki sumayya ke kallonsa, yau kuma gimbiya ta zama kenan"eh nina saka maka, kace babanka ne ya baka sannan baka sakawa, akan me"? Sumayya naki saka sarkan nan ne, dom sau biyu ana kokarin fizgesa a wuyana,shiyasa na daina sawa. "Kamar ya ban gane ba"? Wallahi barayi mana, kaje kasuwa xaka saida abu anki saya, Amma barayi na kokarin sata. "Allah ya kyauta , wai bazaka bude idon bane" Ba musu yad'an fara kokarin, bude idon a hankali a hankali harya budesu duka. "Ya illahih"sumayya tace lokacin da idanunta ya sauka akan kwayar idon muhammad, yayi jajazur kamar jini zai digo, inka ga idon zaka d'auka koh buga masa shi akai jini ya taru. Sumayya menene naji kina salalami? "Ba kome, yayan khadija kaga idanunka kuwa"? Taya zan gani, bayan ba gani nake ba, me idon yayi? Wallahi kamar jini zai digo jajazur" Kuma Nima rad'adin da nakeji sosai fa. Allah ya kyauta, bara naji sauki sai muje asibiti, Amma dai yanzun, kaje chemist ka siyo mini magani rage rad'adi, kaima saika sayawa kanka naga, har wajen ya kumbura"? Gaskiya ne, kannawa ciwo yake wallahi, gashi ma yunwa nake ji, kema nasan kinaji bara na had'a duka nasai mana. Nikam bazanci kome ba, ka biya shago kawai ka d'auko mini lemo, bakina d'aci, ka tura a kira khadja tazo tad'an gyara mini kofar, nikuma bara nayi sauri na fitar da zanin gadon ya baci sosai" Toh ki zauna kawai tunda tafiyar taki batayi kyau ba, bara na jika zanin gadon inna dawo zan wanke? yace yana fita a d'akin bayan ya d'auki zanin gadon, waje muhammad ya fita bayan yakai zanin gadon band'aki, tsallake titi yayi, yaro ya samu ya aika gidan goggo, a kira masa khadija, shikam ya wuce chemist in jambusko. Yana isa chemist yasamu layi dole ya zauna har akazo kansa, maganguna ya saya harda wanda zai diga a ido, yabi shagon sa lokacin har shagari ya bude, d'aukowa sumayya lemon yayi, yasai abinci duka yana rike da laidodin a hannunsa har lokacin idanunsa rad'adi suke masa. Yazo tsallaka titi kamar daga sama yaji mota yayo kansa gadan gadan da gudu ya fara kokarin kauce wa, Amma ina saida suka cin masa, kamar zasu kadesa, amma suna zuwa kusa dashi suka ja birkiii Sosai ya tsorata sai kiran sunan Allah yake, wasu kattai hannun su d'auke da bindigogi, suka fitoh a motar duk sun rufe fuskokin su da mask........ *MATAR MAKAHO*