← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 104

Sashe 71

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

laaa ka tashi?yace da sauri yana karaso wa kusa da Al'ameeen. Al'ameen kam ya cika da mamaki wai inane nan? gashinan a cikin wani daki kamar akurkin kaza, haka yake kallon d'akin, sai dai jin fulatanci a bakin su yasa sa gane fulanine su, duk da gidan Adara fulani ne sai dai sam basa magana da harshen su, da hausa suke magana sai dai koh yaya ne indai mutum ya zauna a jalingo, zaiji fullaci koh bai iyya maida martani ba bare shida yake zaune a unguwan fulani, shima cikin fullaci yake tambayar su nan inane yake. Murmushi yaga saurayi yayi, sai kuma ya juya ya kalli yarinyar, indo wai har yanzun baki tafi tallah ba?kinsan in inna tazo ta samu baki wuce ba ranki zai baci koh,fita ki d'auki nonon ki kitafi. Ba musu ta mike duk da ranta baiso ba, ta fita a d'akin, juyawa gidado yayi yana kallon Al'ameen, sunnu ya jikin naka?duk da fulatanci yake magana. Sosai Al'ameen yake mamakin wannan Al'amarin, wai garin yayane ma yazo inda yake nan, yanaji gidado nata masa magana amma kala baice ba. Ganin yaki magana yasa gidado tashi yabar dakin,cikin gida ya shiga yaje ya sanar da bappan sa bakon ya farka, amma baya magana don shi ya d'auka koh wata matsala ce, ya hana muhammad magana. Al'ameen na zaune kamar gunki yana tunani abubuwan da suka faru dashi, a yan kwana kin nan, sai kuma tunanin sumayya ya fado masa, koh yanzun a wani hali take?lumshe idanunsa yayi yana kiyastata amma yagagara hasko kaman nin ta, yaso ace itace mutum na farko da zai fara gani, bayan dawowar idanun sa. Gidado da bappa da suka dade da shigowa, sai magana suke amma Al'ameen baisan ma sunayi ba, dafasa gidado yayi, da sauri ya zabura sai kuma ya d'aga ido yana kallon dattijon dake kusa dashi, ya zuba masa ido, sunkuyar da kansa yayi Amma baiyi magana ba. Akwai inda yake maka ciwo ne? A hankali y dago kai ya kalli mutumin, sai kuma ya basa amsa cikin fulatanci kamar yanda yamasa magana, babu abinda yake mini ciwo. tashi ka fitoh kayi Alwala ka biya sallan da ake binka, gidado zai kawo maka kaya ka saka da abinci kaci. Toh kawai Al'ameen yace, yana mikewa tsaye da taimakon gidado ya fitoh a d'akin, kasance war dakin a hanyar kofar gidane , yasa yana fita yaga inna zaune tana gyaran zogale a tsakar gida, ina kwana? Mtswww kawai inna Talatu tayi, tacigaba da abinda take ba tare da tabi takan gaisuwar saba. Sanin halinta yasa gidado d'aukowa Al'ameen buta ya mika masa,shima Al'ameen dayake ya saba ganin abinda yafi na inna yasa bai wani damu ba, don duk Abinda zata masa lafilane in an had'a da rashin mutuncin gidan Adara. gidado dakinsa ya shiga, kaya ya d'auko kala uku na fulani, sai nono da matar sa ta dama,ya had'a da dambu ya kaima Al'ameen a d'aki. Bayan muhammad ya idar da sallah, wanka yayi bayan gidado ya iba masa ruwa a rijiya, ya chanja kaya, abincin ya bude kasa cin dambu yayi, nono kawai yasha, kad'an duk yabi ya shiga damuwa halinda sumayya da kanwar sa zasu shiga a rashin sa. Sai bayan muhammad ya gama kimtsawa, kafun ya mike a hankali ya fitoh a d'akin bappa ne da gidado zaune a gindin bishiya, sai inna dake zaune a gefen su rike da fifita, karasowa yayi kusa dasu bappa a hankali, ya zauna a gefen su,duk da bansan tayaya nazo nan ba, amma dai nasan taimako na kukayi, nagode Allah ya saka da Alkhar, yace musu. Ameeen,bappa da gidado har suna had'a baki suka amsa masa, sai kuma bappa ya kara tambayar sa, yaro garin yaya babba dakai har ruwa ya jaka?koh wani abinne ya faru dakai? Shiga ruwan nayi zan sha, shine yajani, ya bashi Amsa. Kai bako ne hala koh?don ruwan mu bayason bako. Eh ni ban taba zuwa kauyen nan ba, baba A ina kake? Jalingo. Jalingo kuma?inane haka, nidai bantaba jin sunan wannan gari ba, gidado yace da mamaki. Bappa ma kara tambayar sa yayi inane jalingo kuma? Muhammad kam sai yanzun ya tuma ashe bafa a kasar NIGERIA yake ba, yanzun toh Amma a ina yake haka, gadai mutane kamar na kasan sa fulanine musujin yare, wani kasane wannan, dan uwa?yayi maganar yana kallon gidado. Gidado ya juya ya kalli bappa, shima bappan gidadon ya kalla suka had'a ido, sannan suka sake maida kallonsa kan muhammad, Cameroun. A hankali yace musu ba'a kasar nan nake ba. Kamar ya ba'a kasar nan kake ba? Eh baba ba'a nan nake ba, a nigeria nake. Nigeria, a ta ina kasar take? gidado ya tambaya da mamaki, don shikam baisan wata kasa nigeria ba, murmuahi bappa yayi yana kallon gidado, nigeria ai na sha zuwa, lokacin da muke cikin ganiyar kuruciya, har kasar muke zuwa kiwo tun daga Cameroun, har nigeria. Wai bappa kasan kasar ne?inji gidado Sosai ma nasan jahohin kasar, kai yaro a wani jaha kake?ya tambaye muhammad. Taraba, ya basa Amsa yana kallon inna dake ta zabga masa harara tun daga inda take. Allah sarki ai naje jaharma dashi, da gombe harda Adamawa, amma tunda kace a taraba kake kenan ta Gimbu ka shigo kasar cameroun? Nima ban sani ba baba kawoni akayi. Kamar ya yaro aka kawo ka, ban gane ba? Shuru muahmmad yayi yama rasa ta ina zai fara. Dafasa bappa yayi, kaga yaro ka fad'amin gaskiya, mu bazamu cutar dakai ba sannan haka muke fata agunka. A hankali muhammad ya gyara zaman sa, ya fara bawa bappa da gidado labarin sa, har Auren sa da sumayya, da batar mahaifin su , har zuwa sanadin zuwarsa kasar nan, ya kara dacewa, sannan baba ina so na koma kasata koh don ganin halinda na tafi nabar mai d'akina a ciki. A hankali bappa ya d'aga ido yakalli muhammad da kyau, ya sunan ka? Muhammad Amma anfi sanina da Al'ameen. Ashe sunan baba nane dakai, Zan fad'a maka gaskiya, akwai asiri a jikin ka har yanzun, sanan bakai aka ma asirin ba, an ma wasu asirin ne a jikin ka, anyi amfani da tauraren ka anyi asiri da kai, dole kana bukatar ka zauna ka nutsu, komawar ka gida yanzun matsala ne duba da abinda mutanen da suka kawo ka sukace, zaka bata musu aiki sanan kwangilar kisan kai aka basu, watoh kaga yanzun an daina Amfani da boka, da zahiri ake son ganin bayanka, ka zauna anan zan maka jinya da izinin Allah duk asirin dake jikin ka zai karye, wa'inda akama asirin ma zasu dawo hayyacin su, sannan zan taimaka maka da maganin kariya babu wani asiri da zai sake cinka bi'izinillah,kaima ka dage da Addu'oin neman tsari a wajen Allah, don yawan ibadan ka shiyasa har yanzun basu gama cin nasara akanka ba. Shuru muhammad yayi amma sam ransa baiso ba, baiso hakan ba, yaso ace ayau innan ya koma gare ta, yaje yaga halinda take ciki ya kalleta da idanun sa, yaga wani irin farin ciki zatayi yau idan taga yana kallo, amma babu hali, sannan maganar mutumin nan bai kwanta masa ba, don shi ba mutum bane mai bin maganganu irin wannan na magani magani, aa tsari tsarin nan sam basu ransa. Ka kwantar da hankalin ka babana, ni magani zan baka don nema maka lafiya, sannan mu sama ma wasu lafiya, domin samun lafiyar ka, warakan wasu ne, karkaji kokonto ni bana aiki da Aljanu koh wani shirka, magani nake bayarwa wanda Alllah ya hure mini sani akan ganyen itatuwa da sassaken su, tunda na ganka nasan Akwai sihiri a jikin ka, Amma inga sarkan da mahaifinka ya baka. Hannu yasa ya kunce sarkan ya mikawa bappa, kurawa sarkan ido yayi nad'an wani lokaci sai kuma ya mike ya dauko ruwa a kwarya ya saka sarkan, ya zuba magani kad'awa yayi sai kawai ruwan maganin ya zama fari tas, wannan sarka d'ayan biyu ne Amma bazance maka kome ba Akansa, bappa yace. Shuru Al'ameen yayi sai kuma ya gyada kai a hankali alamun ya amince,ya karbi sarkan ya makala, kamar kwana nawa ne zamuyi baba? Murmushi bappa yayi sai kuma yace,ka kirani da bappa haka yarana ke kirana, sannan maganin ka bana kwana bane, na wata ne. Kamar wata nawa kenan bappa? Kamar wata uku, kuma kasan inka gama magani dole sai kunje cikin cameroun asai da shanu mu baka kudin mota. Shuru muhammad yayi kamar ya fashe da kuka, yanzun har wata uku yana zaune a wannan kauyen, ba tare da sumayya ba ai sai kewan ta ya kashe sa, tun lokacin sa baiyi ba, toh nagode bappa Allah ya saka,mikewa yayi a hankali ya nufi kofar da yake hango fili ta waje , alamu dai kofar gida kenan. ina zaka?Gidado daya mike yake tambayar sa don ya d'auka tafiya zaiyi Waje nake son fita, ya basa Amsa. Kanason zaga gari ne? Eh ina so, yace cikin ransa yana dariya wai wannan kauye ne gari. Toh jirani barana kunce shanu mu fita kiwo, saina nununa maka wajaje, yace yana tafiya tirkensu domin kunce shanun. Da sauri Al'ameen ya biyo sa wai zai tayasa kuncewa, ai yana saka hannu a kafar shanun da sauri yaja baya, ganin yanda shanun ta hafto kamar zata tunkudesa da kahon sa. Dariya gidado yayi, kai kaja baya fa shanun nan saimu, yana maganar yana kunce su . Matsawa muhammad yayi gefe yana kallon gidado yagama kunce su yana kad'asu yayi waje bayan ya karbi guzirin sa a wajen matar sa, muhammad na binsa a baya yana mamaki wai d'an yaron nan ne da mata. A haka suke tafiya gidado sai hira yake masa, duk inda suka wuce saiya ringa masa bayani, ga gonan wane, ga shanun su wane, ga kogin kaza a haka har suka nausa daji, wuni sukayi suna yawo sosai Al'ameen ya gaji bayan gidado ya kunce boronsa daya rataya, abinci ne a ciki sai goran ruwa, bayan sunci ne suka kamo hanyar gida basu suka iso ba sai goshin mangari ba, suna isa suka samu har an kira mangariba da sauri sauri gidado ya d'aure shanun suka tafi masallaci. Sosai jama'ar garin suke bin muhammad da kallo, ganinsa ras dashi kamar ba gawan jiya ba, gashi kyakkyawar bafulatani, suna idar da
Chapter 71 · 0% Book details