Sashe 76
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
muhammad saida yaci ta baki, jini ya balle masa, bindiga d'ayan yasa ya buga a kan bappa, kara bappa ya sake yana dukawa hade da rike kansa da karfi yana salati, jin wani irin azaba mai tarin yawa na bazata. Don Allah kuyi hakuri, karku cutar dashi don Allah, muhammad yana magana yana kuka. Kai ragon maza kaika san Allah ne?wani a cikinsu yace. Kuyi hakuri... Bamuda imani bare hakuri. Bappa dake duke har lokacin jikinsa sai rawa yake tsabar azaba, kamasa d'ayan yayi ya kwantar kaman rago yasa masa wuka a wuya. Ai muhammad na ganin haka yayi wani irin mikewa da karfi, ya bangaje mutumin da ya takasa, duk wani tsoro ya fitar masa a rai ganin tabbas abu biyune zai faru rayuwa koh mutuwa, rugawa yayi da gudu ya nufi bappa, kafun ma ya iso garesa tuni mutumin ya dirza wukar jini ya fantsama. Zuciyar muhammad ta riga ta kikashe yanzun, yaga mutuwar mahaifiyarsa, kaninsa, amma bai taba ganin mutuwar da ta mugu-mugun ratsasa ba irin wannan, sharbeben Adda dake rataye a jikin d'aya daga cikin yan Ta'adan ya zare da karfe, kafun giftawa da bismillah tuni muhammad ya shiga fad'a da mutanen nan, cikin bazata da rashin tsammani,Allah kad'ai yake kira, yakini kawai yasa a ransa koh yakashe koh a kashesa, suna da bindiga shikam wukane kawai, sosai suke..zuba alburusai yana kaucewa, cikin rashin sa'a wani yasake bullet, ya kuskure sa a hannun hagunsa, ihu yasa da karfi yayi kan mutumin, wukar hannunsa yasa ya fille masa kai,sosai jikin muhammad yake bari ganin yau da kansa ya kashe mutum shi muhammad, mutum hudu ya kwantar, daman su hudun suka bisu. Mikewa yayi ya sabe gawan bappa, sai kuma ya rasa ina zai nufa dashi, tunda fa ya fitoh baiga su inna ba, wani shawara ne ya fado masa, aje bappa yayi ya sabi bindiga da wuka ya koma cikin rugan su gidado. Tun daga nesa ya hango fulani da aka tara waje d'aya, cikinsu harda su gidado da wasu kattai suka danne sa, sai lantana dake kwance bata motse, sai jinjira a gefe tana cillara kara cikin jini koh cibi ba'a yanke mata ba, Alamu dai daga haihuwarta ta riski wannan masifa. Bin jikin ciyayi muhammad yayi ya saita mutanen da suka danne gidado, su biyar gabaki d'aya ya sakar musu bullet one by one, ai take yan ta'adan nan suka fusata suna sake ruwan harsashi ta saitin muhammad, da sauri ya kwanta a kasa. Wanna daman gidado ya samu da wasu matasan fulani suka d'auke wukake da adda aka fara aran gama. Inna dake gefe da sauri ta rarrafa zuwa wajen jaririyar, wuka ta karba a hannun wani ta yanke mata cibi, nadeta tayi a d'an kwallinta ta kama hannun indo, tare da wasu matan suka ruga a guje, sukayi daji kowa yayi takai takai, aka bar gawan lantana a wajen, don ta rai ake. Muhammad yau an zama zaratan maza sosai ake gomxa fad'a, duk wani tsoro nasa yau ya kau, yakini d'aya a ransa zaiyi rai koh ah ah, ganin yanda wasu dakarun barayin nan suka fara shigowa rugan, suna karuwa har sun fara ninkesu, gashi mata da yara da suka rage a raye sun dade da gudu, yasa muhammad d'aga murya da karfi, kowa yayi ta kansa karuwa suke aje-aje zasufi karfin mu. Ai yana maganar nan da gudu ya kama hannun gidado da wani saurayi zaiyi sa'an sa suka nausa daji da gudu, haka ma sauran mazan ana harbinsu suna gudu wasu na faduwa matantu, barayin suka mara musu baya, yayinda su kuma suka raba kawunan su, kashi-kashi. Muhammad gudu suke a daji koh gabansu basa gani, gudune irin na bakin Rai bakin fama, nausawa daji suke yan ta'andan nan na binsu, a hakan suka ringa gudu, (wani abu sai tashin Hankali kayi abinda koh da kudi aka had'aka bazaka iyya ba, sai kaga masifa)sosai sukayi nisan kiwo, gudu suke mutanen na binsu suna sake bullet, Allah ya tsare su, har suka isa wani baban ruwa fad'awa sukayi ciki, yaufa muhammad da kansa ya tsallake ruwa, suna tsallaka kogin har lokacin mutanen na binsu, sosai suka kara azama basu jima da gudu bayan tsallake kogi na biyu, suka hango wani kauyen, ganin Hakan ne yasa mutanen juyawa suka barsu. Faduwa muhammad yayi dasu gidado a kasa, ganin sun shigo cikin mutane, A raye basu mutu ba, karasawa sukayi cikin gari. Sun ma rasa ta ina zasu fara, fahimtar da sukayi garin kamar babu alamun musulunci, ganin yanda mutanen garin suke, buya Al'ameen sukayi basu bari hankalin yan kauyen ya dawo kansu ba, a hankali suke bin cikin gonaki har suka tsallake kauyen lokacin dare yayi sosai, don akiyasce zaikai 10:00 na dare, gindin wata bishiya suka samu suka zauna, kowa na maida numfashi koh bacci basuji yau, muhammad kam jingina yayi da jikin bishiyar ya lumshe idanunsa yana tunanin rayuwa, tunda ya tashi yake ganin jarabawa iri iri, Amma baitaba zata zaiga irin nayau ba, ace tun 2 na dare yana cikin tashin hankali har dare war haka, ada yayi tunanin zuwan sumayya da farin cikin da ya samu, baitaba tunanin akwai sauran wani damuwa ba, ya zauna da sumayya da zuciya d'aya, duk da an sanar dashi ita ba mutuniyar arziki bace, auren jingina za'a basa, hakan yaji A Ransa zai iyya zama da ita cikin aminci, baitaba sawa ransa, don sumayya tayi ciki zai gujeta ba. A Ranar daya samu tabbacin farin cikin sa, sumayyar sa budurwa ce, yaji dukkan wani damuwa kunci ya yaye, a lokacin rayuwa yake tuna musu mai dadi nan gaba,don ya tabbatar auren sa da sumayya akwai dalili, bai d'auka zaiga irin masifar yau ba, shine yayi kisa?kisan ma mutum d'aya ba, ba biyu ba, atake yaji aransa tabbas yanason zama SOJA don ya bawa kasarsa gudumawa, da maganin ire iren mutanen nan, indai da rai da lafiya koh kurtune inya koma gida zai nema, tunda ba ilimi mai zurfine dashi ba, insha Allah sumayyar sa sai tabar Amsa sunan MATAR MAKAHO zuwa MATAR SOJA........ ******************* Bazaki cigaba da zama da miskini ba yanzun sumayya, mahaifin kima yace gobe in Allah ya kaimu zaku wuce garin su mahaifiyar ki. "Kin gama, koh baki gama ba"? Na gama sumayya. "Toh bara kiji, ni a haka naga mijina kuma nake son zama dashi a miskinin, banga wanda ya'inda suka isa su rabani dashi ba, wallahi sai mutuwa karyar mutum" Sumayya Rashin kunyar da kika koya harya kai haka, bansani ba shige toh muje, su Abie na waje saikije ki kare musu tanadi bamu ba, aikoh me muka miki bamu shanshanci wannan iskancin ba. "Inje ina? mijina bayanan kuma baibani izinin fita waje inga kowa ba" sumayya tayi maganar tana tura kosanta a baki bibbiyu ma, take turawa irin na huce haushin nan. Innalilahi wa'inna'ilaihi raji'un na shiga uku ni sumayya,na lalace da'aka had'a baki dani aka aurar wa yan iskan Adarawan nan, yarinyar yarona ni sumayya na bonu, wi.. wi. wi dada ke kuka tana maganar nan gwanin tausayi Mimi ce ta mike tayi waje, wajen su Abie dake zaune a cikin manyan mototi a waje na Alfarma, gabaki daya yan unguwan sun maida hankalinsu kan mototin, atunanin su koh wani masifar yan gidan suka jajibo. Miemie na isa kuka ta fashe dashe a bakin motar da abie ke ciki. Da sauri dukansu suka fitoh a motar , magidanta ne sun d'an manyanta, su biyar harda abie sai samari hudu da masu aure biyu, abie da sauri ya fara tambayar mimi abinda yake faruwa, ina sumayyar?gabaki d'aya inka gansa sai ya baka tausayi. Tas mimi ta zayyana musu kwandon masifar da sumayya ta juye musu, kuma tace bazata fitoh ba mijinta bainan. Ita sumayyar ce ta fad'a miki haka?babuji yace yana rike baki. Eh babuji.... Ke kije cikin gidan kice ana sallama damai gidan, babuji yace wa mimi. Juyawa tayi ta shiga gidan, daidai lokacin Ammar ma yayi packing in motarsa, suka fitoh shida khadija a ciki, rage mata hanya yayi a bakin kasuwa. Karasowa yayi da sauri kusa da dasu, cikin sallama ganin su mutane ne ba raini, gaisawa sukayi, khadija ma ta gaidasu, tana mamakin meya kawos, don bata mantasu ba, sune iyayen sumayya, cikin gida ta shiga ta barsu a waje harda Ammar. Bayan d'aya daga cikin mazajen gidan adara ya fitoh, gaisawa sukayi dasu babuji, sannan suka nemi izinin shiga cikin gidan zasuyi magana da yarsu in ba damuwa. da mamaki mijin inno ke kallon su izini shi ai harma ya manta ana neman izini, kafun a shiga gidan wasu, suda gidansu ina yaga izinin shiga, amma dai ya maze yace su shigo. Ammar fa zare ido yake, wai meke faruwa ne haka, yasa sa binsu a baya suka shiga ciki. Sumayya na tsaka da cimar ta, taga shigowar Familin su maza, kwarjinin da suka mata yasata mikewa tsaye, haka kawai taji gwuwarta yayi sanyi, had'a ido da tayi da abienta dake binta da kallo, baitaba tsammanin xaiganta haka ba, daren jiya koh bacci baiyi ba, yana zullumin halinda xaizo ya risketa yau. Sannu sumayya tunda baxaki fita ba, mu munshigo munsame ki, uncle gaddafi yace. Tsunkuyar da kai, kawai sumayya tayi batace kala ba. Shige mu tafi, in mijin naki ya dawo saiya zo muna da magana dashi, wannan auren bamu yarda dashi ba, daman kudi muka biya sulaiman akan auren. "Kamar ya uncle bangane baku yarda da auren ba? Kuma ba wanda ya baiwa muhammad kudi, asalima cemai akai ciki ne dani" Eh Momcy gida zamu koma gaskiya bazaki cigaba da xama a gidan nan ba,ai daman mu muka sakaki auren sa, yanzun kuma munce bazaki zauna dashi ba, uncle nata d'aya yace. Hajjo ce ta kalli sumayya, kuma kaf mu innan babu wanda ya miki kazafin zina in karya muke a kira sulaiman in, don mu sulaiman in ma bamu sansa ba jinsa kawai muke a waliyin mijin da muka baki. "Ai uncle bakin Alkalami ya bushe, a da kunada iko dani Amma banda yanzun, ban shirya xama karamar baxawara ba, ina son mijina. Sumayya!! abie ya kirata da dukkan yakininsa, yau koh momcy baice ba sunan Dadansa guda ya Ambata, sumayya yau nayi miki Alkawarin cika miki burinki, zan kaiki kiga mahaifiyarki kiga danginta, zan dawo miki da