← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 104

Sashe 29

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

sai gobe "Toh khadija Allah ya Kara lafiya ga wannan ki D'an samu abinda kike bukata ki Saya dashi" nace Ina Mika Mata 10k Aunty ki barshi kawai d'awainiyar tayi yawa jiyama fa Goggo tace mini kun kawo Mana 5k naje asibiti danaje in ma,Ina saurayin da nace Miki yazo guna? "Eh na tuna har kikace bazaki fita ba"na Bata Amsa Ashe Dr ne Ina zuwa na gansa shine ya sayo mini magani kyauta, "Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari" Ameen Aunty "Wancan yayan kine ya baki wannan Kuma nawane,ki karba khadija kid'an Saya Abubuwan da baki dasu" Gaskiya Aunty nagode Allah ya saka da alkhari,tasa hannu ta karbi kudin "Ameen khadija" Yauwa aunty nace Koh Zaki aje mini tunda Naga azumi ya kusa Inna tashi zuwa kasuwa saina karba naje na sai kaya,samun na samu dinki da wure? "Ah ah khadija insha Allah, Allah zai Bud'a Mana har yayanki ya sai Miki kayan Sallah, wannan dai ki sai Abubuwan bukata irinsu kananan Kaya da mayuka Turare pad omo sabulu ke dai irin Abubuwan bukatar Yan Mata haka" Toh shikinan Aunty Daman bani da kananan Kaya sai na saya pant biyu Brz sai vest shima biyu Amma na gwanjo Zan Saya aunty sauran chanjen, Ina materials da ake yayi yanzun ana yankawa a dinka dogayen riguna dasu? "Eh khadija"na gane su Yauwa yadi d'aya dari uku su Zan Saya kala biyar na dinka "Gaskiya khadija kinye tunani Mai kyau kema saiki samu na chanjawa kwana biyu" Toh Aunty Zan tafi nagode Allah ya Karo customers "Ameen khadija yanzun ma wasu na zuwa da dare maganar dinner aike alkhari ce tunda sanadin ki nake samun kudin" Ah ah Aunty Allah ne ya tsaga da rabonki , shiyasa kike ci "Hakane Kam khadija" nace Ina shiga kitchen da sauri nake na d'aura Mana abincin da zamuci Bayan fitar khadija girki na Gama na juye Mana a kula,sai goshin mangari ba yayan Khadija ya dawo Sumayya sannu da gida? "Yauwa sannu yayan Khadija sai yanzun" Eh wallahih ya aiki? "Lafiya klau" nace Ina kallon sa ganin Kamar a cikin damuwa yake D'azun Bashir wani makwancin mu ke tambaya ta Wai MATAR sace taji labarin Wai kina lalle ke kikama Asma'u na aure shine Wai yake tambaya ta zata samu lalle gobe,make-up jibi da Rana? nace ya bari saina tambaye ki inyaso in mun hadu a masallaci anjima na fad'a Masa amsar ki. "Lallen me za'a ma MATAR tasa"? Suna ne haihuwa tayi jibi suna "Gaskiya nifa bazanje home service ba,in mutum nason lalle Koh kwalliya yazo ya same ni a gidana" Amfa Sumayya haihuwa ne ya za'a yi mace maijego tazo lalle gidanki? "Wallahih yayan Khadija ni raini ne banaso a rayuwa na kar mutun yaga kaje Masa lalle ya Raina ka" Kai Sumayya ba wani raini ai sana'a ce ta kaiki ba maula ba,ki daure kije ki Mata kinji? "Shikenan Allah ya kaimu goben Amma bansan gidansu ba da yamma ta tura yaro yazo ya kaini" Sumayya har yamma?ya tambaye ta "Eh man saina Gama aikina,Koh so kake na tafi da safene,jibine fa sunan" Toh shikenan Allah ya kaimu yace Yana mikewa ,ruwa ya ibo a boket ya shiga bandaki Muna idar da sallan mangariba Koh abinci bamu ciba Yan make-up na dinner suka zo su biyar ne dukansu harda Amarya heavy make-up suke so,Dole tasa na hakura dacin nawa zuba Masa nayi na d'auko Masa ruwa a freezer na jira Masa,a d'aki na fitoh waje,don ni bana saka baki a dakina Sam kowa ya zauna a waje kawai Sai da yaye isha'i kafun ya shigo gidan, gaisawa sukaye da customers nawa,don na fahimci yanzun mutane na ganin kirmansa tunda kofarsa suka shigo "Abincin ka na d'aki yayan Khadija"nace Masa ganin ya nufi d'akin kar yaje ya zubar da abincin tunda a kasa na jira. Toh yace Mata Yana shiga d'akin Make-up na Amarya na fara, Gamawa ta biyani akazo aka d'auketa saura hudun ma duk na Gama musu kafun 9:00,kudin da suka bani 25k Inna hada Dana d'azun kusan dubu saba'in na samu kenan Alhamdulillah yau kawai na tashi da kudi dubu sittin da biyar in aka cire 10k Dana bawa khadija Wani tunanine ya fado mini akan kudin, murmushi kawai nayi na nufi d'akin Ina bude labulin idona ya sauka Akan plate inda nasama yayan Khadija abinci nakai dubana garesa da mamaki ganinsa a.............. *My Real and special Fan'S* *Princess* *Maryam najibu* *Mummy* *Shamsiyya Gombe* *Ummu na'eem* *Faeexetion* *Zainab* *Bebi* *Maman khairat* *Oum Abdullahi* *UMSAD INCENSE* *Ummul husnah* *Duk Naga comments naku Allah ya bar kauna Nima Ina yinku* *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO*
Chapter 29 · 0% Book details