Sashe 104
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ka kyauta gamunan zuwa, suna yanke wayar neman wayar sumayya yayi ya kirata sumayya dake zauce akan kantan customer care tana aiki taji wayanta na ringing d'agawa tayi tasa a kunne ganin sunan maikiran nata, "Hello Rabin Raina" Hello sweetheart kin koma gidane? "No Rabin Rai yanzun nake kokarin fita, musa driver na haraban bank yana jirana" Ok kice masa ya wuce dasu salim, ke ki jirani ina zuwa? "Lafiya dai naga kace mini yau sai 6 zaka dawo kana da aiki"? Lafiya yanzun Ammar yake sanar dani sun shigo lagos suna Airport. Ok saika zo tace tana yanke wayar, number musa driver ta kira ta shaida masa ya wuce kawai gida, sannan yacewa bahbah(tsohowar mai Aikinsu)ta kara wasu abubuwan cin zasuyi baki. Ba'a jima ba da wucewar musa saiga muhammad jakanta kawai ta d'auka ta shiga motarsa suka wuce Airport, suna isa Jakanta sumayya ta bude ta zaro Abayan ta sakawa tayi daman akwai have sunnah a jikinta dukansu suka sauka a motar waya Al'ameen ya d'aga ya kira Ammar. Tsaye suke suna duduba masu fitowa, daga nesa sumayya ta hango Khadija da katon cikinta a gaba tayi kyau kamar ba khadin goggo ba hutu dajin dadi sun ratsa ta, sai Ammar dake rike da hannun yaran su biyu mace da namiji,macen baka kamar babanta sabanin na mijin dayake fari, da sauri sumayya ta dagawa Khadija hannu da sauri suka karaso garesu da gudu, yaran suka rungumi muhammad suna masa oyoyo uncle da murna suka tattaru sai gida. Suna isa gida suka samu yaransu a tsakar gida, bahbah ta musu wanka, suna zazzaune a gaban malamin su dake can gefen flowern tsakar gidan, ai lokacin da suka gu momynsu ta sauko a mota da Ummi(khadija)gasu Amira(Aisha) da mukaddas yasasu rugawa da gudu suka nufesu da gudu, duk irin kwala musu kira da ustax keyi, ina sunyi gunsu da gudu da sauri suka rungume yaran suna murna. Koran su sumayya tayi hardasu Ameer suka wuce wajen karatu, tace sai ustax ya tadasu sai su shigo duka. Suna shiga cikin part daban sumayya ta sauke su khadija da mijinta, ta basu waje su kimtsa itama d'aki ta shiga ita da muhammad. Bayan mangariba zaune suke akan daining dukansu suna cin Abinci, Ga yaransu a zazzaune Suma ana ci dasu, hira ake na yaushe gamo, kallon sumayya khadija tayi. Aunty Gaskiya shagunan ki sun habbaka last months munje jalingo, nida maimuna mukaje shagon gaskiya nasha mamaki ganin harda saloon ga gyaran jiki duka? "Wallahi kuwa khadija kinsan yanzun shago hudu nake running Na make-up saloon gyaran jiki, lalle kuma gaskiya Alhamdulilh matar shagari na iyya kokarinta yarinyar ta burgeni akwai Amana" Gaskiya ne Aunty nima na yaba da nutsuwar Rufaida. "Ai shiyasa na bar mata kula da shagunan a hannunta sannan ita ke iban ma'aikata da masu training". Toh Allah ya kara budi. "Ameen khadija waini ina labarin kamila ne"? wallahi aunty tadaiji sauki yanzun ba kadangarun sai daifa Abin ya taba kwakwalwanta. "Toh Allah ya sauwaka,Yajikan momy(safina)da rahama" Ameen suka amsa dukan su,bayan sun gama cin abinci Yaran suka wuce ciki yayinda su sumayya ke hira falo, sallan isha'i sukayi sukaci gaba da zaman falo ana hira. Da gudu Na'ifa take saukowa daga upstair hannunta d'auke da system in sumayya tana kwala mata kira ga sauran yaran na binsu baya. Da mamaki sumayya ta kalleta ganin vedio call suke da mutanen nijar, karban system in tayi ta aje musu akan center table dake falon, duk suna zazzauna akan kujeran da take gaisawa suke da su nabila indo Aunty zainab da nana(Aisha takwaran mamansu muhammad)sai muwaddat dake rike da sabuwar jaririya a hannunta, gaggaisawa suke tare da mata barkar haihuwa akan basu samu zuwa ba cikin khadija wata 8 amma insha Allah zasu zo auren muhibbat. Bawa su muhammad da Ammar system in sukayi suma suka gaisa da yusuf dake cikin iyalansa cikin farin ciki don yara biyu zainab ta haifa masa Aisha da muhin, sosai akayita hira harda mahmah data kara tsufa sosai ga lawiza duka don yau akayi sunan muwaddat duk suna hade. Sai kusan 9 sukayi sallama khadija da mijinta sukayi part da suke sauka in sunzo, dayake yaransu dasu Na'ima zasu kwana, had'a kansu sumayya tayi har bedroom na maza wanka ta musu dukansu tasa musu kayan bacci ta kwantar dasu, tufa masu Addu'a tayi taja musu kofa, d'akinsu na'ima ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu Amira dayake duk zasu iyya ma kansu, Addu'a tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta. D'akin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani d'an iskan kayan bacci riga da wando jikinta sai kamshi yake ta wuce d'akin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga. Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa. Da sauri sumayya ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje d'aya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Rabin Raina menene sirrin ne kullum dad'a kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki. Murmushi sumayya tayi sai kuma ta tuno wani abu cikin dariya tace,kai menene haka? Dariya ya sake tuna masa da ranan su na farko, shima Amsa ya bata, yi hakuri gado nake nema zan kwanta ne? Itama ta sake basa Amsa, wallahi bazan kwanta dakai gado d'aya ba gadai kujera acan jeka kwanta. Gabaki d'ayansu dariya suka sake a tare cike da farin ciki suke romancing na juna, hannu muhammad yasa ya kamo blanket in ya lulubesu. *Alhamdulil!!!!!Alhamdulilah!!!!!!!! Alhamdulilh!!!!! nagode Allah daya nuna mini wannan rana cikin koshin lafiya, harna kawo karshen labarin matar makaho, duk wanda nama ba daidai ba ina neman afuwarsa* *MATAR MAKAHO FAN'S INA MATUKAR ALFAHARI DAKU, DON DA KARFAFAWARKU NA TAKA WANNAN STEPS DANAKE KAI AYAU, WA'INDA NAGA COMMENTS NAKU DA WA'INDA BANGANI BA WA'INDA NAMA REPLY DA WA'INDA BANMA WA BA, ALLAH YABAR KAUNA INA GODIYA* *SANNAN INA MAI MUKU ALBISHIR HADE DA SANAR DAKU SABON LABARI NA DAKE TAFE MAI SUNA* *ALKAWARIN MASOYA* *WANDA NAKE DA TABBACI HADE DA YAKININ ZAI MATUKAR KAYATAR DAKU INSHA ALLAH* Ruqeenjalal ke muku sallama Documented by H.M.G Times New Roman Times New Roman Symbol Symbol Arial Arial Calibri Calibri SimSun Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO KB7 TECNO LD7 WPS Office 605746a389fd4b90bcebfcf18fc92f13